← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 211

Sashe 202

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anty Zainab rage sautin muryar ta tayi sosai ta sake matsowa kusa da ita tace" Hudah kin san mun 'dauki tsawon lokaci tare da ke ko haka ne ko ba haka ba?"
Da sanyin murya ta amsa ta da fa'din" Hakane Anty".
" A iya zaman mu dake na ta6a tilasta ki yin abinda ranki bai so ne?"
Nan ma kai ta girgiza mata.
" Na ta6a cusa miki ra'ayin son Mu'een ko kuma na ta6a nuna miki rashin jin da'di na game da 'kiyayyar da kike yi masa?"
" A a Anty baki ta6a ba".
" Kin san dalili?"
" a a".
" Toh saboda naga ra'ayin ki ne hakan shiyasa na biye ki, kuma na fuskan ci ciwon da kike ji a lokacin cikin zuciyar ki shiyasa ban ta6a takuraki akan sa ba, nasan duk wacce irin hakan ya same ta dole ne taji babu da'di amma Noor bazan 6oye miki ba, dai-dai da rana guda ban ta6a farin ciki da rabuwar ki da Mu'een ba, idan kuwa naga irin 'kiyayyar da kike yi masa har cikin zuciya ta nake jin babu da'di kinsan dalili?"

Kai ta girgizawa Antyn.
Yayin da ta cigaba da fa'din" Saboda 'kaunar da nake yi masa ne matsayin sa na 'dana, Mu'een tun yana da shekaru shida a duniya ri'kon sa ya dawo hannu na bai kuma bar gaba na har sai lokacin da ya shiga Jami'ah a lokacin kuwa kinsan ya riga ya mallaki dukkan hankalin sa ya san me ya kamata yayi da rayuwar sa, Noor ki kwatanta yanda ni nake ji matsayi na na uwar ri'kon sa da yanda Ammin sa zata ji ita datake matsayin mahaifiya agare shi wacce ta haifi abinta da kanta, kinsan dole nata fin nawa ne ko?...wallahi ko ala'kar dake tsakanin ki da Hakeem ban son ta, amma babu yanda zanyi, inaso inga auren ku ya gyaru da shi amma na rasa ta ina zan fara, ina ganin ki agaba na amma ban isa nayi yanda nake so ba saboda gudun kar inci amanar da Ammin ki ta bani, domin an kawo ki wuri na ne da niyyar shiga tsakanin ki da Mu'een..kinga babu yadda zanyi in nuna miki muhimmancin dayake da shi agare ki tunda ga dalilin zuwan ki waje na, shiyasa kika ga ban ta6a furta komai agare ki ba, amma wallahi nasan hatta Ammi kawai dauriya take yi tana biye miki ne saboda farin cikin ki, ko lokacin da kuka ha'da baki da ita kika canza layi ma ba 'karamin takaici naji ba haushi sosai hakan ya bani har ya sani furta wasu 'yan maganganu idan baki manta ba... amma ba wai nayi ne saboda wani abu ba kawai dai raina ne ya 6aci da ganin 'kyamar da kuke nunawa duk wani abinda ya shafe shi...dukkan ku ina son ku Noor ina kuma son farin cikin ku, yanzu da kike gaban iyayen ki kika bar hannu na a yanzu ne nake da damar da zan iya bayyana miki komai da ke raina...Ke da kanki kinsan Mu'een na 'kaunar ki kuma nasan kema kina son shi Noor me yasa zaki da'kile muku farin cikin ku ta hanyar shigowa da wani cikin rayuwar ku? me yasa bazaki koma 'dkin mijin ki na asali ba? kar kiyi zaton auren wani da zakiyi mafita ce agare ku domin shima baki da tabbacin nagartar halayyar sa, may be idan kika bincika ki samu nashi halin ninkin na Mu'een ne ta iya yiwuwa kuma ki kasa fahimta har sai bayan auren ku a lokacin ya zakiyi da shi to?..ko shikenan kin ringa yin aure kina fitowa kenan saboda mazajen nada wasu halayya?, na tabbata bazaki yadda da hakan ba, me ze hana ki daure ranki ki koma ga mijin ki tunda shi kin riga kin san halayyar sa kuma gashi nan da kanki kinsan yayi nadama sai ku rungumi rayuwar ku ku rufa asirin junan ku, dan Allah zakiyi badan komai ba nd na tabbata Ammin ki kanta zata fi farin ciki da hakan, kar kiga wai su suka raba auren ku da shi, ina da tabbacin har gobe suna son sake ganin ku tare kawai farin cikin ki suke son gani da kuma gudun danne miki hakki shiyasa suka basar...yanzu ki zauna kiyi tunani da kanki ki ga me yafi dacewa da ke, koma bazaki tausaya wa halin da yake ciki ba dan Allah ki zauna kiyi nazari ki bi dacewa ba wai dan nayi miki maganar ba a a, kiyi abinki saboda Allah, ni ban miki magana dan ki takura kanki ko kuma dan in tilasta ki koma masa ba face dan ki fahimci gaskiyar da ta kasa bayyana miki.
Horo ko wani irin horo kun hora min yaro Hudah sauran kuma sai dai in bayan sa kuke son gani...".
Ta 'karasa tana murmushi sannan ta 'dora da fa'din" Kinga ko Uncle J ma jiya muka gama magana da shi kuma ban sanar da kowa ba wannan tsakanin ni dake ne, yace Alhaji Baba na shirin bada auren ki ne ga wani abokin Mu'een amma ya dakatar da shi saboda yafi so ki koma ga mijin ki ya ma ce idan ya samu amincewar ki zuwa nextweek yake so amaida auren kun kafin tafiyar ki in yaso sai ki 'karasa karatun da auren ki..ke ya kk gani jira kawai yake yaji daga gare ki yanzu dan ke ke da linzamin komai".

Kuka sosai Noor ta sanya ta kife kanta tsawon lokaci babu wanda ya sake furta komai tsakanin su Anty ma shiru tayi tana jimamin wannan lamari, tasan duk laifin sa ne koma menene da ace bai aikata abinda ya aikata ba da duk hakan bazai faru ba, da yanzu suna can zaune a gidan su cikin farin ciki da iyalan sa.

Ganin kamar kukan Noor 'din bashi da alamun tsagaitawa ne ya sanya Anty Zainab fara rarrashin ta tana neman afuwan magangun da tayi tace idan na 6ata miki raine kiyi ha'kuri Noor ko ka'dan ban fa'di abu guda da niyyan 6ata miki ko cin zarafin ki ba, abinda ke raina kawai na gaya miki saboda ganin kamar na isa in fa'da 'din ne, nasan dole zakiji babu da'di amma please kiyi ha'kuri on behalf of dukkan iyalan Taheer Manga nake baki ha'kuri, Noor kar kiga laifin mu kuma kar kiga kamar son zuciya muka nuna, dukkan wanda irin hakan ya faru da 'dansa dole ne yayi wani yun'kuri dole zai aikata abinda yaga yafi dacewa ne shiyasa kika ga mun dawo miki da maganar baya kuma ba wai dan kema bamu son ki bane a a kawai dai dacewa muka duba sai dai nasan a yanzu bazaki ta6a fahimtar hakan ba, inaso kiyi mana afuwa dan Allah idan kinji 'kudurin mu ya 6ata zuciyar ki..ni zan tafi amma ina so ki zauna ki nutsu kiyi nazari kafin wani lokaci ina so in san abinda kika yanke.."
Anty ta shi tayi tai mata sallama ta fita nan taje ta samu Ummah ma suka yi magana..a nan ta sake fahimtar Ummah ma ba da'din hakan take ji ba, tunda taji cewa akan ta lafiya tayi masa 'karanci duk sai take tausayin sa, Ummah tace su fita harkar ta kawai duk abinda suke ganin ya dace suje suyi.

Anty Zainab ne tace a a kam ba za'a yi haka ba, Umman Saudah ai hakkin ta ne yanzu dole sai an nemi amincewar ta kafin a zartar da wani hukunci".
" Hakane kam..to Allah ya za6ar mana mafi Alkhairi".
" Ameen Ameen" Anty Zainab ta amsa ta da shi sannan ta yiwa Ummah sallama ta fita daga gidan gaba 'daya.

Nasiha Ummah tayi wa sosai akan hakan ta kuma bata wasu addu'o'i tace ta ringa yi ta kuma ro'ki Allah akan yayi mata za6i mafi alkhairi...kar ta wani ru'dar da kanta domin dukkan mafita yana wurin Ubangiji ne..".

Anty Zainab da 'kafan ta ta koma gida kuma tun a hanya ta 'kira Uncle Ja'afar tayi masa bayanin abinda ke faruwa bai damu ba sai yace a barta ta samu lokaci tukunna.

Anty bata ko tattauna batun da Ammi ba dan tasan hanawa zatayi zata ga kamar za'a takurawa Hudah ne hakan yasa Anty Zainab taja bakin ta tayi shiru sai dai a kullum bata fasa Addu'a akan Allah ya daidaita lamarin ba.
Chapter 202 · 0% Book details