← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 211

Sashe 135

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na koma na zauna gefen su Biba tare da gyara zaman mayafin na...ba bu'katar sai na sanar da wa'danda muke tare a 'dakin domin nasan ta riga tayi musu bayanin komai dan haka ban kuma ce da su 'kala ba kawai nayi shiru.

'Dayar mai suna Fati itace ta ta jefa min tambayar" wai su mijin nawa ne zasu shigo?"

Da kai na bata amsa alamar" Erh "sai tace ita dama tana so ta ganshi dan bata ta6a ganin sa ba kuma taji ana fa'din wai 'dan gayu ne".
'Dan murmushi kawai nayi mata sai ta 'kara da fa'din" Dan Allah idan yazo ki nuna min shi kinji..juyawa tayi ga Biba tace kema Biba ba kina so ki gansa ba?"
Duka Biban ta kai mata tana fa'din" Allah ya shirye ki ke kam".
Zabura tayi gefe tace" ba wani ai gaskiya ne".
Duk yanda nake jin zuciya ta na harbawa amma hakan bai hana ni yin murmushi da jin irin maganganun nasu ba.
A fili cewa nayi da su
" Kar ku damu insha Allahu zaku ganshi". nace dasu ina mai yin 'kasa da kaina.

Kafin ta 'kara yin wata magana sai muka ji sallama daga bakin 'kofar shigowa 'dakin.

Imam ne kan gaba sai Ishaq sannan Yah Deen da wani a bayan sa da bansan sunan sa ba.

Jan Hijab 'dina na 'karayi ya rufe min rabin fuska ta yayin da su Biba suka gyara zaman su da kyau tamkar wasu manya...gaisuwa da ta'aziyar Baban mu su Ishaq suka yi min wanda cikin muryoyin nasu ko ka'dan banji tashin muryar sa ciki ba.

Duk yanda su Biba suka 'kagu da su ganshi amma kasa sakin jikin su suka yi balle su fahimci waye Mu'een 'din a cikin su, daga gaisuwar kawai naga sun mi'ke tsaye duk suka yi waje ya rage daga ni sai su Yah Deen.

Su Ishaq ke 'dan labarin sanin da suka yiwa Baban mu musamman lokacin da ya bada aure na ga Yah Deen wanda tun a lokacin kusan dukkan su suka yabawa karamci da dattakon sa,  ashe kwanaki 'kalilan suka rage masa...yanzu sai dai Fatan ubangiji Allah yayi masa Rahama yasa Aljannar firdausi ta kansace makoma agare sa...muma ya kyautata namu tafiyan...Ameen

  Daga 'karshe Ishaq ne ya 'dan 'kara yi min nasihar ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara inda ya nuna min cewa irin su Baban mu ba iyalan su ka'dai ne ke damuwa da rashin su ba..yace kusan duk wanda ke tare da shi dole yayi alhinin rashin sa, gata 'daya da yakamata mu yi masa a yanzu itace addu'ah ka'dai...da kansa yayi masa addu'ah muka shafa wanda daga haka duk suka mi'ke tsaye suka nufi hanyar fita.

Suna masu sake maimaita Allah ya ji'kan Baba da Rahama.

Kaina 'kasa nake amsawa da" Ameen Ameen" ina wasa da yatsun hannu na yayin da nake jin siraran hawaye na gangaro min saman kunci na a hankali.

Ban yi ta6a tunanin har haka Baban mu zai samu yabo daga abokan Yah Deen ba musamman akan auran mu, ji nayi duk jiki na yayi sanyi 'kalau, cikin raina na ayyana" in dai har haka ne kuwa da iznin Allah zan yi ha'kurin zama da shi cikin kowace irin hali, in dai har akan aure na da shi mahaifi na zai ri'ka samun kya'kkyawar Addu'ah to kuwa zan 'daura 'damarar zaman aure na, Yah Allah ka mantar da ni komai, Yah Allah ka sanya fahimta tsakani na da shi.

Ban yi tsammanin akwai wanda yayi saura cikin 'dakin ba da yake naji shiru, amma haka kawai sai naji ni a tsarge tamkar ana kallo na, a  hankali na 'dan 'dago kaina ka'dan nan naci karo da shi zaune shiru ya zuba min idanu.

'Kasa na sake yi da kaina batare da na furta komai ba illah tunanin abinda ya zaunar da shi a anan 'din da na fa'da, nan na tsinkayi muryar sa yana fa'din" Har yanzu kukan kike yi ko?"

Girgiza kaina nayi a hankali sannan na fara goge hawayen dake fuska ta da hannu na 'daya.
Tsaye ya mi'ke ya sanya hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jikin sa sannan ya kalle ni yace" Anjima zamu koma Jigawa da su Ishaq fatan ba wani abu ko?"

Da kai na bashi amsa alamun a a...sai yace" Toh Saif zai kawo miki sa'ko anjima ko zuwa gobe, in kuma akwai wata matsala ma ai ga  Ammi ko kuma ki 'ki 'kirani a waya kawai ki sanar da ni kinji".
Ya 'karashe maganar yana duban agogon dake 'daure a tsinysiyar hannun sa.
" Uhum"
Na bashi amsa da fa'din hakan batare da na kalle shi ba.
" Na tafi"
Ya sake fa'di yana me nufan bakin 'kofa cikin tafiyar sa mai birgewa....da farko rasa abinda zance da shi nayi dan haka nayi shiru ina bin bayan sa da idanu kawai...dai-dai ya isa bakin 'kofa zai fita sai na tsinci baki na da furta" Allah ya tsare".
Take kuma na sake yin 'kasa da kaina.

Cak ya tsaya sannan ya waigo ya dube ni, fuskar sa ba yabo ba fallasa ban kuma ji ya amsa addu'ar da nayi masan ba balle insan matsayin ta kawai sai naga ya sa kai ya fice daga 'dakin abin sa.

Zugum nayi kamar kurma idanun 'kyam wuri guda ina bin hanyar da yabi da kallo...ni kaina ban san me yasa nayi masa addu'ar ba, kamar yadda yanzun ma ban san me nake tunawa ba haka kuma na kasa fahimtar matsayin da zuciya ta take a yanzun da naji cewa zai tafi Jigawa ba.

*****
       Ko bayan tafiyar sa ban koma gidan Ammi ba, zama na a gidan mu nake jin ya fiye min kwanciyar hankali domin ina ganin Ummah ta da sauran 'yan uwa na sai nake jin bani da damuwar komai.

A hankali duk jama'ah na nesa da na kusa suka watse ya rage saura mu ka'dai, ko gaisuwan ma yanzu an rage zuwa sosai hatta Ammi ta kan 'dauki lokaci bata zo ba...haka ma 'kawata Binta ta kan yawaita zuwa tana tayani hira, wani lokaci har yini mukan yi tare yayin da wasu lokutan bara jimawa take komawa.

Sa'ar da naci ma 'daya ne domin duk cikin su babu wanda ya matsamin da batun cewa in koma gidan Ammi.

Baba Alhaji da kansa ya kan yawaita yin aike na ku'di ko wani abu yace akawo min bayan ko wanda Saif ya kawo min bayan tafiyar Yah Deen ma har yau ban ta6a ko sisi a ciki ba.

Waya kuwa bana 'kiran kowa daga Anty Zainab yayye na sai Ammi, ita ma idan na 'kira ta bata 'dauka sai dai ta yanke ta 'kirani daga baya...ko Yah Deen 'din ban ta6a 'kira ba ban ta6a ko tunanin 'kiran sa ba, hasalima ni ko saving number shi cikin wayar ban yi ba,  haka kuma shima banga ya sake 'kira na ko sau 'daya ba.

Har akayi 40 days 'din Baban mu aka gama ina gida..wanda tun kafin ranar su Saif suka koma school da yake hutu ya 'kare, ni kam ma ban san me yasa yanzu naji bana son zuwa makarantar ba sam naji ta fice min aka.

Ammi ce ma da kanta ta fara yi min maganar makarantar har ta tattaro min shirgin uniforms 'dina ta kawo min amma ko sau 'daya ban iya naje ba.

Lokacin da Addah Maryam zata koma ne nace zan bita Ummah ta ta hanani, nan na fara yi mata kuka sosai na 'daga hankali na kan batun tafiyar har Ammi sai da ta sani nan ta ro'ki Ummah ta da fa'din abar ni man naje tunda ba 'dadewa zanyi ba Ummah ta tace " a a ba inda zani tace hala kun manta ne cewar matar aure take yanzu ba kamar da ba".

Murmushi Ammi tayi domin sai yanzu ta fahimci Ummah da manufar hana ni tafiyan duk da bata fito fili ta bayyana ba amma hakan bai hana Ammi fahimtar ta ba.

  Cikin ranta ta bari akan cewar da ta koma gida zata 'kira Yah Deen ta gaya masa taji shi kuma me ze ce.

Hakan kuwa akayi, Ammi bata ta6a tunanin bama waya da shi ba, so a yanda tayi maganar sai ta nuna masa cewa idan munyi waya ko da na tambaye shi batun tafiya dan Allah kar ya 'ki amincewa, tanaso taje mahaifiyar ta kuma ta hana ta wai saboda tana da aure".

Yace" Gaskiya ne ai Ammi matan aure na yawo ne dama?"
" Ba yawo bane fa Mu'een sistern ta take so tabi...".
Tun kan ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din" Sistern ta har ina kenan?"
" Ban sani ba...kana min irin wannan tambayar nice fa na haife ka ba kai ka haife ni ba".
Ta yi masa maganar a 'dan masifance.
Kansa ya sosa sannan yace" Sorry Ammi amma ai naga anyi resuming school shine kuma zata wani wuri saboda me?"
" Ka tambaye ta mana zata gaya maka ai, shikenan saboda makaranta bazata yi ziyara ba?"
Sai yace
" To Ammi taje abinda ni ba ruwa na...Allah ya bada sa'a".
Daga haka ya yanke wayar yana mai jin haushi cikin ransa amma ya danne bai bayyana ba.

Bayan tafiyar Ammi da muka ke6e da Addah Maryam sai take shan cikina akan yanayin zama na da Yah Deen dan tunda take bata ta6a ganin ko waya ma muna yi ba, tace bata ga wani alamun kulawa tattare da 'dayan mu ba...tace da alamu ma har yanzu baki san me manufar auren da akayi miki ba".

Ni kam ban 6oye mata komai ba na sanar da ita yanayin zama na da shi, abu 'daya ne ban bayyana mata ba shine ganin sa da nayi da Husnah, haka kuma ban sanar da ita cewa dalilin kenan da yasa da na dawo gidan Ammi da zama ba...na riga na yiwa kaina al'kawarin bazan ta6a sanar da kowa wannan abin ba, duk da nasan bani da ranar mantawa da shi, a kullum idan har zan zurfafa tunani na to dole sai  wannan mummunan photon ya zo raina.
Chapter 135 · 0% Book details