Sashe 95
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ita ta kammala 'daurayar ba har sai kusan 10:23...sannan ta koma ta na hutawa, bata jima da zama dan hutun ba sai kuma tayi wani tunani dan haka sai ta tashi da niyyar zuwa kitchen ta 'dan dafa musu ko indomie ma, harta shiga kitchen 'din amma sai ta fasa ganin dacewar yin wanka kafin shiga kitchen 'din cuz sam bata jin da'din jikin ta a haka, wannan dalilin ne ya sanya ta fita daga kitchen 'din ta wuce 'dakin ta dan ta watso ruwa sannan ta dawo kitchen 'din.
Kafin ta kammala komai har 11:38 tayi hakan yasa a 'kagauce ta shirya ta fita bata ko kwashe kayan ta dake shanye gaban gidan ba ta bari akan sai ta dawo kawai...gidan ta kulle da yake tasan yana da nashi keys 'din a hannun sa shiyasa bata damu ba.
Tana fita sai ta tari adai-daita ya wuce da ita makarantar.
Su Mu'een kuwa 12 cif suka fito daga lectures, shi da Ishaq da Imam suke tare harma Ishaq nayi masa 'korafin wai yau 'din sun ganshi wani iri ya babu sakin fuska kamar kwanakin da suka gaba ta..lokacin kafin su gama dai-daita wa da Husnah ne kowa mugun hali ya ringayi musu...bayan hakan kuma sai ya 'dan dawo dai-dai, and still gashi yau ma halin ya dawo.
Tsaki kawai ya saki ciki-ciki jin Ishaq zai fara takura masa da tambaya, shi ka'dai ya san damuwar da yake ciki shi kam, cuz tun jiya da Uncle J ya sanar da shi ya taso hankalin sa ya kasa kwanciya sam, tsoron abinda zai biyo bayan tattaunawar Alhaji da Uncle J yake yi...ko 'dazu da sassafe ya 'kirashi sunyi waya sai dai yace da shi yana Gombe amma suna shirin tasowa da yake acan ya kwana saboda doguwar tafiya ce.
Yanda yake jin ransa cikin 'kunci ne ya sanya bai 'kara ko da mintina goma tare da su Ishaq ba kawai yayi musu sallama ya wuce gida abinsa...da tunanin ko zai 'dan samu nutsuwa, sai yanzu yaga wautar sa, da tunda Husnah ta tabbatar masa da cewa babu komai ta 6angaren ta sai ya saki ransa da tunanin ba itan bace Alhaji ke hari, shab ya manta da cewar Alhajin jiran zuwan Uncle J yake yi suyi magana, ya manta ashe isowar Uncle Ja'afar da abinda zasu tattuna shine babbar damuwar sa, duk dama dai yana tunanin Uncle J zai goyi bayan sa ne amma idan Alhaji ya sanar da shi komai fa...shikenan kashin sa ya bushe kenan...da wa'dan nan tunanin ya isa gidan nasa ya bu'de ya shiga bayan ya sallami 'dan sahun da ya sau'ke shi.
Akwai research 'din ma da yake son yi ga kuma damuwar da ta dame shi shiyasa yafi bu'katar ke6ancewa shi ka'dai batare da an takura shi ba...addu'ar sa kawai shine Allah yasa tattaunawar ta su ta kasance masa alkhairi...amma sam baya wani son aure yanzu inda ace ra'ayin sa za'a bi...dama lokacin da Nanne ke raye ne zazzafar soyayyar da yake yi mata ya sashi tunanin auren ta a lokacin batare da ya ko dubi 'karancin shekarun sa ba, yanzu kuwa da babu wata cikin ransa sai yake jin yama tsani zancen auren, in kuwa ya zama dole sai an masa ne ma to Allah ya sa ba da Husnah Alhaji zai ha'da shi ba..sam ba zai iya kallan ta matsayin matar sa a cikin gidan sa ba shi kam.
Da shigar sa gidan ya maida 'kofa ya rufe harda datsewa da sakata kamar su Ishaq 'din sunce da shi zasu biyo bayan sa..a palour ya yada zango bai ko nemi abinci ba, batare da 6ata lokaci ba kawai ya fara abinda ya kawo sa.
Ya 'dauki a 'kalla kusan awa guda da 'yan mintina zaune a wurin yana aikin research cikin laptop 'din sa, bazata kawai sai yaji 'karar wayar sa tana rurin neman agaji.
Sai da ya 'dan saki tsaki kafin ya mi'ka hannu ya lalu6o wayar kamar baya son 'dagawa, ganin sunan da ke yawo kan fuskar wayar ne ya sashi saurin dai-dai ta zaman sa sannan yaja recieve.
"...Yaro na gani a Dutse...kana cikin school ne ko kuma kana gida?"
Muryar Uncle Ja'afar ne ya fa'di hakan wanda daka ji yanayin yanda yayi maganar ma zaka san cewa cikin tsananin farin ciki yake.
'Bangaren Yah Deen kuwa da jin abinda Uncle 'din yace sai da kansa ya sara masa wani gif..yaji tamkar sau'kar duwatsu a tsakar kansa...cikin ransa ya saki salati..sannan a fili yace" Uncle dagaske?"
Idan kaji yanda yayi maganar cike da mamaki zakayi zaton ko tsabar farin cikin da yake cikine ya sanya shi furta hakan, amma ina ba haka bane, tsanar ru'dani ne kawai yasa shi shiga wannan yanayin cuz bai yi zaton zuwan Uncle J har garin da yake ba sam bai yi wannan tunanin ba ma koda wasa.
Maganar Uncle J da yaji yana fa'din" Da gaske mana ko in koma ne?"
Shine yayi saurin dawo dashi hayyacin sa...cikin rawar murya yace" a a na isa ince ka koma ne Uncle... ina gida yanzu haka".
Sai da ya fa'di hakan kafin ya tuna babban kuskuren da ya tafka, sai dai yana shirin sake yin magana yaji Uncle J ya yanke 'kiran...bai ko tambayi address 'din gidan ba da yake tun zuwan Yah Deen na farko da shi akayi komai.
Tuni ya jima a tsaye hakan yasa ya dafe kansa da hannun sa 'daya thinking of yanda zai yi ya 6oye zaman sa da Husnah a gidan, yasan idan Uncle J yasan wannan labari cin 'kaniyar sa zai yi bada wasa ba kuwa.
Wayar tasa ya jefa kan kujera sannan ya fara waige-waige cikin palourn yana duba ko akwai wani abu da ya shafi Husnah da zai yi saurin bayyana zaman sa da ita amma luckily babu komai da ya dangance ta illah earings 'din ta dake kan center table ajiye.
Da sauri ya 'dauka yaje 'dakin ta ya wulla shi...zuciyar sa cike da tunanin me yasa Uncle J zai yi masa haka? Me yasa tun jiya da yau da sukayi bai sanar da shi zai zo ba har sai da ya iso tukunna...ai da ya san cewa Jigawa zai fara zuwa da tuni ya sallami Husnah da komatsan ta kaf ta bar masa gidan sa tuntuni.
Kitchen ya shiga nan ma ya fara dube-dube sai dai bai ga komai da zai iya tona asirin sa ba, kitchen 'din tsaf-tsaf babu alamun 'kazanta acikin sa tamkar wanda ba'a amfani da shi, duk kuwa da yana da tabbacin aranar ma bata fita ba sai da ta yi girki, shi kansa yana yabawa da tsabtan Husnah cuz ya san A ce ita 6angaren tsaftar jiki da na muhalli gaba 'daya.
Daga kitchen sai ya nufi 'dakin sa nan ma bai ga komai da ya danganci mace ba, cuz daga sun tashi a bacci take tattare komai ta gyara tsab...har bayin sa ya le'ka amma duk bai ga komai ba...duk da haka sai da ya tsaya ya 'kara kimtsa 'dakin yanda Uncle J ba zai zargi komai tare da shi ba...gadon shi tsaf a gyare ga shi ko'ina na 'kyalli tamkar ba mutane ke rayuwa cikin gidan ba...
Duk abin nan da ya ke yi kuwa cikin hanzari da rikicewa yake yin komai dan yasan Uncle Ja'afar na iya isowa a kowani lokaci..ya tadda shi.
Sai yanzu ma yake jin haushin kansa da ya riga ya furta cewa yana gida, da yace masa yana school kawai in yaso sai yayi gaggawan komawa cikin makarantar su ha'du acan amma ina...ya kwafsawa kansa.
Kafin ya baro 'dakin nasa sai yaji daga can waje ana buga 'kofar shiga gidan.
A 'dan dake ya fito kasancewar mutun 'daya yake tsammani a lokacin, abinka da marar gaskiya yana tafiya amma idanun sa tsuru tsuru yana sake bin ko'ina da kallo...fargaba yake yi kar asirin sa ya tonu, in har Uncle Ja'afar ya san cewa da mace yake zama agidan ai yasan kashin sa ya bushe, aure kuwa bai isa yace baya so ba koda mata hu'du aka ce za'ayi masa saboda hukuncin abinda ya aikata...bai isa ya ja da Alhaji Baba ba ko giyar wake yake sha duk bayan mintina.
Sai dai yana fita harabar gidan wani tashin hankalin ya ziyarce shi, dalilin cin karo da yayi da kayan Husnah shanye a igiya a gaban gidan...."Subhanallahi"
Ya furta afili sannan da gudu-gudu sauri-sauri ya isa ya fara tattare su yayin da ake cigaba da bugun 'kofar daga waje alamun an 'kosa da bugawa.
Da hanzari ya kai kayan 'dakin ta ko shiga bai yi ba ma watsa su kawai yayi sannan ya jawo 'kofar ya datse da key ya cire key 'din ya kai drawer 'dakin sa ya 6oye...sannan ya sake fita karo na biyu yana gyara zaman rigar da ke jikin sa..at same time yana baza idanuwan sa cikin gidan gudun kar yabar wani abin.
Yana cire sakatan 'kofar Uncle J yace" Sai yanzu ka ga damar bu'dewa ko..miye ma na kulle gidan bayan na riga na sanar da kai ina hanya soon?"
" Sorry Uncle...bayi na ke ne shiyasa".
Yayi maganar yana kar6an jakar dake tare da shi.
Murmushi Uncle J yayi sannan ya sa 'kafa ya shigo gidan, Yah Deen nayi mai barka da isowa.
A palour suka yada zango Yah Deen yaje ya kawo masa ruwa ya ajiye gaban sa, sai dai bai ma shaba kawai yayi murmushi yace da shi..." Mai ya kaini zuwa wurin 'dan makaranta da ishi, nasha ruwa na tun kafin na iso ni kam".
Shima Yah Deen 'din murmushi yayi kawai yayi yana sosa kansa, jin sa yake tamkar akan 'kaya yake tsaye, bai san mai yasa Uncle J yi masa irin wannan zuwan ba sam...shi da yace zai taho kan maganar Alhaji Baba kuma ya akayi ya 'karaso nan.
'Ko'karin zama gefen sa yake sai yace da shi" Ka shammace ni gaskiya Uncle..ban ta6a zaton zaka iso Jigawa ba fa..da na shirya maka better ai..."
Ya 'kara she maganar da sigar zolaya.