← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 211

Sashe 64

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba 'da ya zaman garin sai ya ishe shi, ji yayi daga yau 'di. nan baya jin zai sake iya kwana cikin garin nan kwata-kwata, gara ya tafi ya daina kallon duk abubuwan da ya ha'da ala'ka da Nanne, musamnan ma ni....wani sa'in ji yake tamkar baya 'kaunar ya sake ganina a rayuwar sa, duk lokacin da ya ganni ya ha'da ido dani...fa'duwar gaba ke ziyar tan sa domin kuwa Nanne sak yake gani tare da ni...har sai ji kamar wai itace...Aminan sa ce....shi yasa idan ya ganni ya ke 'kura min idanu har zai zuciyar sa ta garga'de shi da cewa ni 'din ba Nannen sa bace kafin yake kawar da idanun sa daga kaina....idan hakan ya faru kuwa sai yaji dama mutuwar ni ta 'dauka ta bar masa sahibar sa a raye....
" _Astaghfirullah_ " yake saurin furtawa idan yayi wannan tunanin...daga 'karshe sai ya 6ige da fa'din duk laifin Ammi ce ai...bansan me yasa ta 'dauko wannan me kama da magen ta kawo ta nan ba.
'Dan 'karamin tsaki ya ja a fili sannan cikin ransa ya furta " i hate seeing her wallahi" tare da tattare goshin sa wuri guda.

Daga haka ya nufi bakin gado ya zauna dafe da kansa yana me cigaba da tunani.

Baya so yawan gani na da yake yi ya ta6a 'karfin imanin sa, saboda yasan Allah ne ya halicci mutuwa so kuma shi ne ya kar6i ran Nanne me yasa zai ringa jayayya da yin sa.

Ammi ce a gaba dan haka ita tayi sallama, banji an amsa mata ba ni ma kuwa sai banyi ba kawai na biyo bayan ta cikin 'dakin muryar Ammi naji cike da damuwa tana fa'din " koda yaushe kana nan a haka Mu'een sai yaushe zaka gane cewa jayayya kake shirin yiwa Ubangiji towards his decision?.

'Dagowa yayi da rinannun idanun sa ya kalli Ammi gami da cire hannun sa da ya dafe kansa da shi.

Ammi da sauri ta 'karasa kusa da shi ta zauna, hannun sa na dama ta kama sannan ta cigaba da fadin " ka kwantar da hankalin ka please...ko ka manta cewa hukuncin Allah ne hakan? yarinyar nan Addu'ar ka kawai take bu'kata a yanzu, kayi mata sannan ka yiwa kanka ma, ka ro'ki Allah ya sanya hakan shine mafi alkhairi a gare ku da mu ma baki 'daya..."
     Bata gama rufe baki ba ya 'dago ya kalli fuskar ta, Ammi sai ta jinjina masa kai alamar tabbatarwa sannan ta 'kara da fa'din"....yes!..ko kasan manufar Ubangiji akan hakan ?"
Da kai ya bata amsa alamar " a'a"...Ammi tace " then you should keep praying Allah ll surely lead u, he ll be with u in every circumtances...ka daina 'daga hankalin ka...Allah da kansa yace yana tare da masu ha'kuri masu mi'ka masa lamuran su, be strong and take a stand kaji? i konw yaro na is a fighter, and please don't loose hope for any reason just take Sabr, Bi'iznillah u will soon meet ur type, the better khair for u, the person who is always there when u ar in needs, who sticks up for you even when no one should.."
Kanshi ta shafa a hankali yayin da shi kuma ya lumshe idanu yana jin sanyi na ratsa zuciyar sa, 'kaunar mahaifiyar sa na sake ratsa shi, cike da kulawa Ammi ta 'kira sunan sa, take sai ya bu'de idanu ya sau'ke su saman fuskar ta...a hankali Ammi ta cigaba da fa'din " Ka daina damun kanka dan Allah saboda mu kan mu hakan na affecting 'din mu, ka fuskanci rayuwar ka ka gina future din ka da kyau Allah zai dafa maka, idan kuwa kace a haka zaka cigaba da rayuwa kanka zaka cutar, before u know ka riga ka tarwatsa rayuwar ka gaba 'daya with that silly reason...sometimes Allah brings people in to our lives just for some purpose, and he also tooks them away when the purpose is done, may be we would never ever know the reason for sure...but Mu'een Allah knows everything, he knows the best and he sees everything....don't worry kaji Baba na...miye ma duniyan....rayuwar mun fa it's all a journey, mu 'din ma we ll leave oneday...may be today, tomorrow nextweek, month or year or years but we ll surely all leave to our own judgement...who ll leave first? me, you, Alhaji, your brothers or someone that u knew..u don't know whom will be...but we are all human and waiting for the death, just focus on that Mu'een and then increase your Du'ah, put your trust in Allah, ask him whatever you want, ask him to ease your troubled heart....Bi'iznillah u will not fail, he will surely lead you, and he will give u the strength and courage to steady your self..."
Jikin hannun ta ya kwantar da kansa a 'ko'karin sa na 6oye hawayen da suke shirin gangaro masa...sai da ya tabbatar ya maida su kafin ya 'dago kansa, cikin 'karfin hali da sanyin murya yace " Thank u so very much Ammi na, really proud of u, insha Allah daga yanzu na daina damuwa Ammi..and i ll not cry for Amina again insha Allah".

Murmushi Ammi tayi na jin da'di...tana murmushin ta kamo chicks 'din sa tamkar wani 'karamin yaro tace " May Allah bless u with the very best of his blessings...Allah ya haskaka rayuwar ka...".

Da " Ameen"
Ya amsa ta shima yana mai jin da'din Addu'ar ta har cikin jinin sa.
" Whenever something troubles you, you hurt or in pain just narrate....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un don't follow your hearts to break you down kaji.."

"Insha Allah Ammi na..."
Ya fa'di cike da girmamawa da kuma farin ciki....'dari bisa 'dari ya yadda da maganganun Ammi, sai dai sam baya tunanin akwai wani abin daban da zai iya cike masa babban ramin da soyayyar Nanne ya tona cikin zuciyar sa.
Ammi kam kawar da waccan batun tayi ganin yanda duk yayi laushi, jikin sa ta duba da kulawa tace " kar dai har kayi shirin bacci tun yanzun?"

Da rawar murya yace da ita " Ina so in samu bacci da wuri ne Ammi kaina ciwo yake yi min sosai kuma ko na sha maganin bai tafiya".
" Ai bazai tafi ba kam tunda ba ka cire damuwar da ke ranka ba dole headache ya kasance tare da kai...Allah ya sawwa'ka nd baccin ma will help..but before that ga abinci ka samu ka ta6a ko kadan ne".
Ammi ta 'karasa maganar tare da mi'ka min hannu alamar in bata.

Tausayin sa sosai ya kama ni duk da bansan ma'kasudin damuwar ta sa ba amma har ga Allah yanda ya koma 'din gaba 'daya sai naji tausayin sa, hakan ne ma ya sanya ni matsowa cikin sanyi da niyyar bawa Ammi abinda ke hannu na.

A hankali ya dago ya kalle ni sannan ya maida idanun sa kan abin hannu na, take ya kawar da kansa gefe sannan yace "..Banso Ammi i'm not hungry"

Ammi na murmushi tace " Da wuri haka Mu'een ai ka bari kaga ko menene kafin kace baka so 'din ko?"
Shi kam baya ya koma ya jinginar da bayan sa sannan yace " am ok Ammi banjin cin komai yanzu, kuma ma 'dazu na sha Zuma wurin Alhaji".
" K'aniyar ka...zuma na hana jin yunwa ne?"
Ammi tayi maganar gami da ware hannun ta saitin fuskar sa.
Ajiyan zuciya ya sauke mai sanyi sannan yace " Ni dai Ammi please... kinga kaina na damu na sosai".
" In tafi kenan in baka wuri ko?"
Ammi tayi maganar tana kallon sa da alamar zolaya.

Saurin gyara zaman sa yayi yana fa'din " Haba Ammi ba haka bane...ni dai kawai abincin ne banso".

Murmushi kawai Ammi tayi masa tare da mikewa tsaye...plate 'din abincin ta sake mi'ko min ni kuwa ina kar6a sai na juya na fita abina.
  Itan ma baya na ta biyo tana fa'din " Mu kwana lafiya...amma fa karka manta da shan maganin ka kafin ka kwanta".
Bai amsa maganar da tayi masa ba illah sunan ta daya 'kira "...Ammi"!
Yayi maganar tamkar dan dole aka sanya shi as if ba yanzu ya gama surutu ba.

Juyawa Ammi tayi ta kalle shi sai taga ma har ya mi'ke tsaye sai tayi shiru ta zuba masa idanu tana sauraran abinda zai ce da ita.

Sai da ya sosa kansa kafin yace...." gobe insha Allahu nake so in koma".

Zuba masa idanu Ammi tayi na y'an sakanni cike da mamaki tana karantar yanayin sa yayin da shi kuma ya lan'kwashe kansa gefe yayi kalar tausayi.

Da mamaki ta furta " Gobe kuma?saboda me zaka tafi?"
" Haka kawai ne Ammi...dama ba da'dewa zanyi ba kuma kinga...kinga"
Sai ya kasa k'arasa wa ya 'karashe maganar da in ina.

Ammi bata damu ba sai kawai tace
" Ka sanar da Alhaji ne?"
Tun ma kafin ta gama rufe bakin ta yace "..please Ammi inform him".

" Allah ya bamu Alkhairi"
Kawai Ammi ta fa'di a takaice gami da juyawa ta bar masa 'dakin.

Yah Deen na ganin  hakan sai ya koma ya zauna gami da sakin ajiyan zuciya...
Idanu ya lumshe ko bayan da ta bar 'dakin, tausayin kansa da na iyayen sa yake ji, har cikin zuciyar sa, har tsawon wani lokaci  zai 'dauka yana bautar dasu da zuciyar su saboda wata damuwa tashi ta daban, ba zai juri ganin kullum iyayen sa na nan nan dashi ba bisa ga damuwar da ya san basu suka 'dora masa ba, shiyasa ya sanyawa ransa 'karfin gwiwar cigaba da rayuwa kamar kowa, gara yaje inda yafi wayo cikin abokan sa 'kila zai fi saurin mantawa da matacciyar soyayyar sa, Addu'ah ce kam yayi al'kawari daga yanzu har ranar da shima zai koma ga mahallicin sa ba zai cire ta cikin Addu'ar sa ba.

Tun a daren Ammi ta sanar da Alhaji Baba batun tafiyar, bai damu ba cuz ko shima 'din yana ganin kamar hakan yafi masa dan baya jin da'din ganin sa cikin wannan yanayin.
Chapter 64 · 0% Book details