← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 211

Sashe 67

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma yadda Yah Deen ya dage da kuma yadda Ammi ta goya masa baya yasa shi amincewa kawai ya 'kyale shi.

Hakan kuwa akayi da yake gidan babu kowa wa'dan da ke haya a gidan basu jima da tashi ba dan sun gina nasu, so bayan 'dan gyare-gyare da akayi wa gidan sai aka shishshirya komai...yayi sa'a ma ba'a jima da canza kayan gidan Alhaji baba ba so tsofin nan aka zo aka zuba su, Ammi ce ta aika aka gyara komai sai T.v data sa aka siya masa da curtain, gida yayi kyau tamkar na amarya...sai dai babu da'di saboda shiru babu ko neighbours illah kangon gidaje da'd'daya.

A hakan shi kam  ransa yafi jin da'di ya fi farin ciki.

Rayuwar Yah Deen kullum akarkace take shi, kusan ko wani lokaci yafi so yaji shi zaune shi ka'dai yayi tunanin da ransa ke so, shi ka'dai batare da an yanke mai ba, yayi rayuwar sa shi ka'dai, ba tare da yaji motsin kowa ba.

Mutane na gudun ka'daici amma shi hakan ne mura'din sa koda wani lokaci...a fa'dar sa wai damuwa ce kawai bai so...sannan wai mu mun cika hayaniya.(Ohh ni Salmerh...naga de banda abin Mu'een dama wake son damuwa a rayuwar nan kawai dai ha'kuri ake ana lalla6awa kawai).

Kuma fa 'karya ce kawai yake yi amma babu wata hayaniya da mukeyi gara ma idan musu ya ha'da mu da Zaidu mukan 'dan ta6a hayaniyar amma itan ma ba kullum ba, bayaga haka kuwa ba komai, sai ko idan muna kallon movie musamman American Movie mu kan 'dan yi hayaniya saboda kowa na za6an star 'din shi ne tun kafin film yayi nisa so aduk lokacin da star 'din wani cikin mu yayi abin da ba dai-dai ba mukan 'dan yi mai ihun mugunta sai kuma idan film yazo 'karshe duk wanda star ya fito daga 6angaren sa ya kanyi murna sosai...shine kawai hayaniyar da muke yi agidan, wannan kam nasan ko Ammi ma tana mana fa'dan ihun, to a daren ranar da ya zo mun kalli Fast 3 da Terminator 2....kuma munsha shagalin mu aranar shine fa ya fake da shi...har da 'kin zama a gida.(ALLAH YA RAKA TAKI GONA....inji Maman Muhammad fa amma).

      Washe garin tafiyar sa da muka zauna ni da Saif lokacin zai koya min karatu kuma sai ya kasance ranar a harabar gida muka zauna, tashin farko tunani na sai ya tafi can wurin sa ban san dalili ba amma har da ta6e baki na.
Ban iya nayi shiru ba kuma sai nace da Saif " Amma wannan Yah Deen 'din gaskiya yana da mugun hali".

Ido Saif ya zaro yana kallo na...sai na ha'de goshi na ganin yanda yake kallon nawa...A hankali yace
" Ni dai ba ruwa na idan yaji ki".
Saif ya fa'di yana mai bu'de text book 'din da ke hannun sa.
Cewa nayi
" A ina zai jini shida ya koma can jejin..."
Tun ma kan in rufe baki na Saif ya tare blni da fa'din" To wai ke ina ruwanki...haka ya ga dama, kuma ra'ayin sa ne ba tilasta shi akayi ba kuma ya koma 'din bashi kenan ba".
Baki na ta6e ina jin araina cewa da ni Aljana ce da sai na ringa bashi tsoro da dare tunda ya koma can shi ka'dai.
Daga haka muka ci gaba da karatun mu bamu sake bi ta kan zancen sa ba.

Yakan zo gidan kullum da safe da rana da kuma yamma, bamu fiye ha'duwa da shi da safe ba da yake sai bayan mun tafi makaranta yake zuwa yayi breakfast wurin Ammi, da rana ma sai kusan 'karfe uku yake zuwa a lokacin kuwa har mun tsufa a Islamiya ma, da yamma ka'dai ne muke haduwa da shi sai dai kuma ba kullum ne yake zuwa gidan da yamma ba sai ranar da yaga dama...saboda bai wani damu da cin abincin dare ba shi.

Sai ko a weekend mukan ha'du dan muna gida ko wani weekend da safe.

Ni kam haushi sosai yake bani yanzu, balle da naga ya 'karawa kansa mugun hali, ko kallan arzi'ki bai mana a gidan, idan kuwa mutun ya kuskure yayi mai wani abu ranar zai kwashi yatsun sa biyar a fuska.

Yah Deen sam baya shayin sau'kewa mutun mari akan kowani irin laifi ne, sa'ar da ni nayi kawai shine ban ta6a ha'duwa da marin sa ba tun zuwan sa, amma ranar da ya mari Saif a gaba na ji nayi tamkar in rama masa dan haushi.

Wai dan ya bashi wankin singletes da safunan sa kala kusan biyar, Saif kuma hannun sa na ciwo shine fa na kar6a yana zaune ina wankewa da ya fito zai tafi sai yaga ba Saif ke wankin ba batare da yayi magana ba kawai muka ganshi tsaye agaban mu..." Ban isa ni in saka abu kayi min ba ko ?"
Yace da Saif da damammiyar fuska.

Saif na shirin magana kawai sai ya 'dago hannu ya wanki fuskar Saif da mari....ba zata kawai naji 'karan mari, ina 'daga kaina sai naga Saif ya dafe kuncin sa da hannu...
" Dan ka raina ni Saifu in baka ka wanke min shine zaka bawa wannan yarinyar salon ta 6ata min kaya ko me?"

Ko da Saif ya bu'di baki zai mai bayani sai ya sake kai masa wani mari gami da fa'din " Shut up da Allah bana son maganar banza...kuma ka tabbatar ka wanke min kaya na da kyau...stupid kawai ".

Yana gama fa'din hakan yayi gaba abin sa cikin ta'kun sa na 'kasaitattu.

Yanda tsoron sa ya shige ni sai naji ko kallan banza ba zan iya yiwa bayan sa ba ballantana inyi magana, badan haka ba da sai na yi masa bayanin abinda ya sanya nake taya Saif wankin da har ya mare shi akan hakan.

Ha'kuri kawai kawai na dinga bawa Saif kamar zanyi kuka sai da naga ya fice daga gidan kafin a hankali nace " ai sai na gaya shi da Ammi....take Saif ya hana ni yace min a a kar in fa'dawa kowa.

Tun daga ranar nake jin haushin sa ga kuma tsoron sa da ya dasa min a zuci....ganin akan 'dan wannan abin shine Saif yasha mari har haka to ina ga kayi wani babban laifin ai sai ya tattaka ka abanza....wannan dalilin ne ma ya sa ko ya zo gidan ban fiya fito wa ba koda ina nan, zama na nake a 'daki har yazo ya tafi ban fitowa ko gaida shi dan gani nake kamar idan mun ha'du zan iya masa abinda zai mare ni batare da nasan na aikata laifi ba, tunda shi komai ma laifi ne a wurin sa...ga kuma wani uban 'daure fuska da ya koya ba zaka ta6a ganin fuskar sa asake ba sam sai dai ko in yana tare da su Ammi su 'din ma wataran ba fara'ar yake yi musu ba.

   Da yake kusan kullum muka ha'du da Ma'u sai ta tunadar dani cewa kar in manta idan ya dawo in sanar da ita...tun wancan tafiyar tasa take kan tunatar da ni, da yake yanzu mun saba sosai tunda nace da ita ai Ammi tace idan an 'kara fa'da min irin waccan maganar inzo in sanar da ita, Ma'u sosai ta kiyaye bakin ta bata ta6a 'kara gigin sanar da ni ba, dama itama ji tayi ana fadi, to ko mutanen ma sun tayin gulmar a tsakanin su sika yi shiru ganin babu hanyar ya'dawa, Ammi ba shiga cikin shirgin matan garib takeyi ba balle taji, sai dai bansan ko Ummah ta ba...'kilan taji amma dai bata ta6a ce da ni komai ba.

Rashin sake maimaita maganar da Ma'u batayi ba yasa nima na saki raina itama mukayi sabo da ita, daga 'kawata Bintu ban kula kowa sai Ma'u.

Ai kuwa kwana shida da dawowar sa muka ha'du da Ma'u, da ta tambaye ni kamar yadda ta saba bama ta6a ha'duwa bata kawo maganar sa ba...sai nace mata " ai ya dawo ma amma ya koma wancan gidan na hanyan makaranta..." na 'karashe da yi mata kwatancen gidan.

Tun daga lokacin Ma'u bata 'kara tambaya ta shi ba ban kuma san meke faruwa ta 6angaren ta ba.

Ni dai ban ta6a zuwa gidan ba dan ko ya 'kira su Zaidu bana binsu, sau tari kayan wankin sa yake ha'da su da shi idan sun wanke sun goge sai su 'kara kai masa can.

Har akaci sati biyu da dawowar sa.
   Akwai watarana da Zaidu ke 'dan jin zazza6i Saif ne shi ka'dai yayi wanki da gugan kayan Yah Deen 'din da ya bayar, dan mugunta kuma wai shi bai son asanya masa kayan a machine dole Saif yayi wankin da hannun sa ko shanya ban taya shi ba saboda tsoro.

Da zai kai masa kayan ne yace in raka shi na'ki, yayi-yayi dani na'ki amincewa, sai da Ammi tasa baki da fa'din " ki raka shi Hudah kinga ma yace yau bazai shigo ba wai atafi masa da Tea kuma ai kinga kayan sun yiwa Saif yawa ko...daure ki raka shi kinji uwata".

Kafa'da na no'ke nace da Ammi" Nifa Ammi tsoro nake ji kar ya mareni".
Na 'karashe maganar da shagwa6a ta.
Ammi sai tace
" Ai idan ya kuskura ya mareki rama miki zanyi kinji Hudah...yi ha'kuri ki raka shi ai ma ba zama zakuyi ba...yana ta6a ki let me know.. i ll deal with him insha Allahu".
Tayi maganar tana mi'ka min 'dan madaidaicin Teaflask da ke hannun ta.

Kar6a nayi ina share hawaye na nudi 'daki na 'dauko 'dan hijab 'dina fari na sanya har na 'kara fitowa hawaye na bai daina zuba ba.....ganin hakan ne ya sanya Ammi fa'din "...To Saif idan kunje sai ta jiraka a waje in ka mi'ka kayan sai kazo ka anshi flask 'din ma ka kai  tunda ita tsoron sa takeji...."
Ta 'karshe da gungunin " Ya maida kan sa dodon 'karfi da yaji kam ba dole yara suji tsoron sa ba".
Da " To". Saif ya amsa ta sannan muka wuce.

A hankali muke tafiyar cuz ni bana sauri yau 'din da yake raina ba son tafiyar yake ba.
Chapter 67 · 0% Book details