← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 211

Sashe 52

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya ka'dan suka sakeyi tare wancan 'din ya shige gida sai ya rage saura shi ka'dai...yana tafiya yana tunani....." Nannen Malam Mamman da abokinsa Ashiru ya fa'da da kuma yanzu da aka ce masa " nan gidan Malam Mamman ne, kenan nan ne gidan mahaifinta.

Cikin ransa yake ta tunani har ya isa gida....baiji 'kwarin gwiwar da zuciyar sa ke bashi ta ragu ba saboda sam bai hango wani 'kalubale game da hakan ba.

Ya riga ya tsara musu a rayuwa cikin da'da'dan mafarkan sa, tun farko Engineering yake da burin karanta amma ha'duwar su Nannen mu yasa shi canza ra'ayi zuwa zama cikakken likita ta yanda zai rin'ka bawa matar sa kulawar da ta dace.....batun yara ma sam bai sasu a lissafin sa ba shi dai Burin sa ya samu Nanne.

         Shi kansa wani lokacin sai yaga kamar kawai yaudaran zuciyar sa yakeyi da cewa wai yana sonta amma  tsoron ranar da Uncle Ja'afar zai fahimci hakan yakeyi dan yaga-yaga zai masa cuz karatu mai zurfi yake so yayi in yasan da batun tun yanzu ya kamu da soyayya kuwa ai ya shiga uku, Uncle Ja'afar ba 'karamib raina shekarun Mu'een yake ba har a lokacin kallon yaro 'karami yake masa bansani ba ko dan shika'dai ne agaban sa oho.

Sannan sarai yasan halin Uncle Ja'afar bashi da sanyin hali kamar Alhaji Baba....shi kuwa baya jin zai iya cire ta a zuciyar sa cikin sau'ki balle ma irin yadda yake jin mugun kamun da soyayyar ta ta tayi masa...abin sai wanda ya san zafin so ne ka'dai zai iya fahimtar sa.

    Satin sa biyu a garin amma gaba 'daya ya mance da damuwar da yake ciki lokuta 'kalilan da suka gabata, damuwar da tayi sanadin zuwan sa garin gaba 'daya, shaf ya manta da Rahma da sha'kuwar su harma da rayuwar da suka yi tare da ita kaf ya manta da su duk a sanadin soyayyar 'yar uwata, abu 'daya ne kawai da ya kasa raba kansa dashi shine yawan jin feelings...wannan  abin kam har yanzu ya kasa raba kansa da shi sai ma 'kara yawaita da yake yi masa.

Ta 6angare na ma haka kullum ban fasa zuwa gidan ba, sai dai kwanaki 'kalilan ne muke ha'duwa dashi cuz mafi yawan ranaku na kan zo har nafi ma bangan shi ba, idan kuwa mun ha'dun gaisuwa ka'dai ne ke ha'da ni da shi.

Akwai watarana da na gaida shi ma ya amsa a yatsine ya ficewar sa lokacin tare nake da Saif muna zaune, yana wucewa sai na yamutsa fuskata nace da Saif" Allah Deenin kunnan ya fiya yanga da yawa".

Ido Saif ya zaro harda kama baki sannan yace dani " yaji ki dai ba ruwana ni...wa ma yagaya miki cewa sunan sa haka?"
"Alhaji Baba ne ya fa'da min"...
Na bashi amsa ina kallon cikin idanun sa.
Sai yace " to ba Deeni zaki ce ba, Yah Deen zaki ce in bahaka idan yaji kina ce mai Deeni duka zai miki ni kuwa ba ruwana".
Ban ce komai ba kawai na ta6e bakina na daga nan nayi shiru ban 'kara fa'din komai ba.

    Tun daga ranar Yah Deen ya kama baki na dan gudun kar ya dakeni kamar tanda Saif ya gayamin.
   Ban ta6a fa'da a idanun sa ba kam dayake ba zaman hira nakeyi da shi ba, amma a duk lokacin da wata hira ta 'dauko aka sako da sunan shi to bana ta6a canza nawa salon 'kiran sunan, ga dukkan alamu kuma ni ka'dai ke amfani da hakan, dan ban ta6a jin wani ya fa'da ba banda ni.

Shima 'din tun baya kulawa da lamarina abu na yau da kullun har ya saba da gani na cikin gidan su, bai san me nake zuwa yi ba haka kuma bai ta6a tambayar kowa ba, kuma har yanzun bai san dalilin dake kawoni cikin gidan su kullum da safiya ba.  

  Sau tari ya kanyi mamaki idan yaga yanda Alhaji da Ammi ke nan-nan dani, ban dama sha'kuwar da yaga nayi da 'kannan sa musamman Saif da jinin mu yafi ha'duwa dashi......
   Bai wani damu sosai da yasan dalilin sha'kuwar mu da ahalin nasa ba dan haka shima sai ya 'dauke ni a yanda ya ganni wanda wani lokacin ma ya kan bani fuska ne albarkacin yawan gani na da Nanne da yake yi.
....tsakanina dashi dai gaisuwa ce kurum daga haka kuma babu komai.

   〰〰〰
        'Bangaren Rahma kuwa.....tun lokacin da ta ga dangi na faman cika gida da 'da'ddaya, taga yanda Hayatu ya dulmiya tsundum cikin shirin biki shikenan ta saduda, yanzu kam ta yarda cewa auren ta da Al'amin babu fashi....tayi danasanin abinda ta aikata yafi sau 'dari uku, a kullun sai tayi danasanin biyewa Mu'een da tayi.
  Gashinan ya yi tafiyar sa ya bar ta ana shirin aurar da ita, babu wanda ya damu da 'karancin shekarun ta ga dukkan alamu ma kowa farin ciki yakeyi da hakan.

A cikin yanayin idan taje gun mahaifin ta kwantar da kai takeyi kullun ta sha kuka son ranta kafin ta fito, baya magana balle ya lallashe ta dan haka da kanta take bawa kanta ha'kuri ta fito.

Ranar wata Juma'ah ne aka 'daura auren ta da Amin bisa sadaki mai daraja.

   Ranar tasha kuka sosai kamar ranta zai fita....da yamma kafin a akaita Hayatu ya shigo 'dakin ta wanda ganin a yanayin da ya shigo 'din ya sanya jama'ar dake tare da ita sulale a hankali suka watse baki 'daya.
Hayat zama yayi a bakin gado a hankali, Rahma dake can kan stool 'din gaban mirror sai ta cigaba da rera kukan ta bata damu da wanzuwar  sa cikin 'dakin ba.
Duk da zuwa yanzun ta tsani Mu'een tsana mai girma amma har yanzu birbishin son shi bai bar 'kasan zuciyar ta ba, yanzu kuwa da take ganin cewa ta zama mallakin wani sai take jin kamar bazata juri rashin sa ba kwata-kwata, 'ka'k'karfar soyayyar ta shi ne ta dawo mata sabuwa dal.

A hankali Hayat ya 'kira sunan ta cikin natsuwa, bata amsa ba amma kuma ta rage sautin kukan nata haka kuma bata 'daga idanu ta kalle shi ba.
Bai damu ba shima kawai ya cigaba da maganar sa cikin natsuwa da sanyin murya yace
" Kiyi ha'kuri Rahma ki gafarce ni, banyi haka dan na 'kuntatawa rayuwar ki ba, nayi ne kawai dan in kare mutuncin ki da mu ma ahalin ki gaba 'daya, na san babu mamaki kina gani na matsayin mutun mai son kan sa ko kuma kice bandamu da za6in ranki ba.
Sai dai inaso kisan wani abu Rahma.... lokuta da dama mukan so wasu abubuwa ne mu kuma kafe akan su alhalin ba su kasance alkhairin rayuwar mu ba, sai kiga wanda muke guje masa 'din shine dai-dai garemu kuma za6in Allah masanin komai, amma wanda Allah yaso sau'ka'kawa lamurane ka'dai yake ganar dashi hakan da wuri ya kuma gane.
   Ki gode Allah kawai Rahma domin da wuri ya bayyana miki irin yaudararriyar soyayyar da Mu'een ke miki harma ya nufe ni da gani da idanu na matsayi na na yayan ki.
      Hukuncin da na yanke kuwa har yau ban ta6a regretting ba, face godewa Allah ma da nake sake yi a kowani lokaci da ya sanya akwai mai yi miki son gaskiya agefe wanda a koda yaushe yake shirye da kar6an ki matsayin matar aure, gudun kar ya zargi wani abu ne ya sanya na sanar dashi dalilin da yasa nake so ayi auren cikin 'kan'kanin lokaci duk da bani da tabbacin idan yaji zai amince amma bani da za6i face bayyana gaskiya ta...nasan idan yana matu'kar son ki ba zai 'ki yadda da auren ki ba tunda akwai masu 'dauko mace agidan karuwai ma kuma su tsarkake ta su aura su kuma rayu cikin farin ciki.

  Allah cikin ikon sa ma sai ya sanya Amin cikin masu kyakkyawan zuciya domin kuwa cikin farin ciki yayi na'am da ke inda ya bani goyon baya 'dari bisa 'dari.
Hakan da yayi ne ya tabbatar min da cewa zai ri'keki da Amana har 'karshen rayuwar ki........Rahma gashi yau burina ya cika na dam'ka amanar rayuwar ki 'dungurungum a hannun Amin, yanzu matsayin aljannar ki Amin yake, mijinki ne kiyi masa biyayya ki nemi aljannar ki, bana son fitina kuma, ke kanki kinsan Amin ni kaina ya girme ni balle ke dan haka ki bashi girman sa ki kuma nemi aljannar ki da 'karfin zuciya, bisa yardaewar ubangijin ki, karkiyi tunanin zaki yi masa wasu mugayen halaye da baki son shi, to duk abinda kikayi Rahma ki sani kece da asara dan kuwa ko Amin ya rabu dake da wuya ki 'kara samun makamancin sa, ina tabbatar miki da cewa har shi Mu'een 'din da kika yi domin sa ba auren ki zai yi ba alokacin dan matsayin bazarawa za'a kalle ki a lokacin...ki ma yi tunani Rahma, wanda bai aure ki lokacin da ya tabbatar da kuruciyar ki ba yaushe kike tunanin zai dawo ya aureki?......Ni 'dan uwanki ne, kuma inason ki Rahma ke kanki shaida ce akan hakan, ina kuma da burin ganin farin cikin ki a koda yaushe, banason rayuwar ki ta girgiza ne koda wasa shiyasa na aikata hakan wanda na tabbata koda da ran mahaifiyar mu bazata so ganin ki hakan ba hakama Daddy bazai so yaji ance ga mummunan abinda ya faru da rayuwar ki ba, idan kuwa yaji hakan kuma yana da cikakken lafiya na tabbata bazai bar Mueen haka nan ba, amma kinga yanda duk Allah ya gyara komai ba'a yi masa gyara dan haka sai dai muce ALHAMDULILLAH....dan girman Allah ba dan ni ba ki kula da rayuwar auren ki kiyiwa mijin ki biyayya ki daraja ahalin sa hakan shi ka'dai idan kika yi zai tabbatar min da cewa nima kina sona kuma kin bi magana ta Rahma, ina miki fatan 'daurewar farin ciki na har abada....Allah ya albarkaci rayuwar ki.."
Chapter 52 · 0% Book details