← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 211

Sashe 154

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka yayi mata yana yi kuma yana yi mata fa'dan" Baby na Mummyn ki bata jin da'di kuma kina da mun ta da rigima ko? Baki ga har kuka take yi ba ne?..ko so kike Daddy yayi miki bulala?"

Da sauri ta girgiza kanta alamar" a a".
Sai yace" To kar ki sake kinji Mama na, ki daina yiwa Mummy rigima in ba haka ba zan zane ki kuma mummy ma zata daina goya ki kinji?".

Da sauri ta sake 'dage kanta sama jin zancen bulala, babu wanda ya ta6a zane ta amma tsoro gare ta sosai.

Sai gani nayi sun sake fitowa, abinki da uwa da gudu kuma ta iso gaba na tana dariya take gaya min da gwarancin maganar ta wai Daddy yayi mata wanka.

Dole na nayi murmushi ina shafa kanta...har cikin jini na nake jin 'ya ta.

Zama yayi kan kujera mai  facing da mu yana kallon mu...kamar ba ya so kuma yace" Me ke damun ki?"

Sai nace masa" Headache".
A ta'kaice dan masifar da yamin yasa ni jin haushin sa.

Kamar yasan me ke cikin raina sai be ko sake tanka ni ba kawai yace" Baby mu tafi ko?"

Da gudu ta tafi inda yake ya 'daga ta sama yana fa'din" Yauwa Mama na".
Bai ko sake kallon inda nake ba yayi waje abin sa.

Asbiti suka koma yaje ya kawo min magani, da yake yasan da batun muran da nake yi shiyasa bai sha wahala wajen gano abinda ya haddasa min ciwon kan ba.

Ranar kam da kaina na bashi ha'kuri da dare ganin har a lokacin kama min kai yake yi..cikin natsuwa yace min" Ai ke ke tilastani yin wasu abubuwan Nuree ko da ban yi ba, please ki ringa bin Baby a hankali kinsan ita yarinya ce abinda ubanta ya jure ita bazata iya ba...wataran da kanta ma idan akace tayi irin hakan bazata yi ba so ki na ha'kuri da yarintar ta kema kinji?"

Da kaina na amsa shi alamar naji.

Ai kuwa ranar ya samu daman rabar jiki na cikin kwanciyar hankali da yake nasan nayi masa laifi shiyasa ban yi masa gardama ba.

*****
         Abu ko wani iri ne idan Baby ta nuna ra'ayin ta akai ko da kuwa iyaka abinda yake da shi kenan zaki ga ya cire ya siya mata.

Ciwo idan Baby nayi to shikenan shima walwalar sa ta 'kare kenan har sai yaga ta samu lafiya, balle lokacin da ta fara zazza6in ha'kori wallahi Yah Deen hutu ya 'dauka musamman a wurin aikin sa dan ya kula da ita ban sani ba ko raina nawa kulan yayi oho masa, domin azahiri ya nuna ni 'din bazan iya kula masa da ita kamar shi ba, Yah Deen sosai yake raina 'ko'kari na akan Jasmine.

Shiyasa nima yanzu na rage damun kaina, abu in dai naga ya fini za'kewa akai game da Baby to bar masa nake yi na hutawa raina.

Bai kasance ma'abocin kula da lamuran yara ba amma akan Jasmine sai da ya koyi duk wani abu da ya shafi 6angaren yara.

       Su Saif ma musamman suka zo shi da Zaidu wai ganin Baby Jas, suna ma fa shirye-shiryen tafiya makaranta ne amma wai su sai sun zo sun ganta kafin su tafi.

Tun zuwan mu Bauchi wannan shine karo na farko da suka ziyar ce mu, wannan 'din ma nasan saboda Baby ne.

In kinga kayan wasa da suka kawo mata abin ba'a cewa komai, haka ma sutura da Ammi da kanta ta sissiya mata ta bayar akawo mata ni kuma abaya ta siya min kala uku da takalmi.

Ni duk sai ma rasa wani irin so suke wa yarinyar nan, dan ko Alhaji Baba ba'a bar shi abaya ba, haka yake biye shirmen ta a waya har video call suna yi da ita, sai kiga tana ta shashshafa kan watar tana dariya tana fa'din _Baba_ ....da irin maganar ta.

Lokacin da ta isa yaye na yaye ta, sai ya kasance boobs 'dina na damu na sosai da zogi, har zazza6i yasa min dan nayi amfani da ha'din 'danyar shinkafan nan da ake yi.

Ni da kaina nasan Yah Deen na 'ko'kari wajen 'daga min 'kafa a duk lokacin da na'ki amince masa wurin kusantata, amma a cikin kwanakin sai na rasa me ya shiga kansa da yasa ya kasa ha'kura duk da yake cewa bana jin da'di.

A zahiri nasan yana matu'kar tausaya min amma da yazo min da bu'katar sa a lokacin da nake 'dan fama da zogin boobs 'din sai na'ki amincewa, nima 'din nasan ban kyauta ba saboda harga Allah a ranar bana jin zugin sosai, amma duk da haka sai na sanya masa kuka ina fa'din" sam baya tausayi na ai yana ganin halin da nake ciki amma zai 6ullo min da wani abu".
Na fa'di hakan ne kawai badan komai ba sai dan bana jin zan iya da shi alokacin dan nasan halin sa ba shi da sau'ki in dai ya samu kaina ba 'karamin caku'da min boobs yake ba...da jin na fara yi masa kuwa sai ya 'kyale ni da kansa ya lalla6ani gami da ban ha'kuri har nayi bacci na a jikin sa batare da na damu da halin da yake ciki ba.

Ni kaina yanzu bansan me yasa wasu lokutan nake 'kin amince masa ba, koma ba yau 'din ba lokuta da dama ma haoan nake yi masa, Yah Deen ya kasance 'daya daga cikin irin mazan nan da suka iya bi da mace wajen kwanciya ni da kaina nasani dan sosai salon sa ke tsaye min a zuci bazan yi 'karya ba, baya ga haka ma sosai nasan yanayin sa ta fannin bu'kata amma na banzatar cikin raina..a fili nake nuna bandamu da lamarin sa ba har hakan ya zauna min a zuciya.

Ada nakan 'ki amince masa ne da yake akwai haushin sa araina na bibiyan mata da yake yi, amma yanzu Alhamdulillah na fara mantawa da komai, kuma ina da tabbacin baya tare da ko wace mace a yanzu, amma duk da haka sai na rasa dalilin da yasa nake gudun sa, har sai nazo kuma na fara dangana hakan da 6atan rai da yake yi akan Baby sai inga hakan matsayin hukunci musamman da nasan shike fara lalu6a ta kowani lokaci..idan ya biye ni sai muyi 2weeeks ko ma fi batare da na amince masa ba.
Ban sani ba ko sabawa da nayi da 'kin amince masan ne yasa har yanzu ban daina yi masa gardamar ba.

Ranar lafiya lau muka kwana bai sake kula ni ba, a lokacin kwana biyar kenan da yayen Baby dan ita kam ma ta 6angaren ta babu wata matsala, ko irin kukan yayen nan bata yi sosai ba.

Washegari kawai naga ya hau shiri bai tanka ni ba har kayan Baby ya shirya da kansa batare da ya nemi taimako na ba, ina zaune parlour sai ganin sa nayi da jaka Jas kuma a hannun sa, waro idanu nayi kafin nayi magana yace min" Zamu tafi gida..Baby say Bye to ur mum".
Ai kuwa ta 'dago hannu tana min bye-bye.

Hanyar fita yayi yana fa'din" Ayi mana addu'ah".
batare da ya min ko.kallon arzi'ki ba.

Kaina sosai ya sara min, saboda tsananin tashin hankali, a fili na fahimci fushin da Yah Deen ke yi da ni, yau kam.nasan na 'kure shi, domin ada ko ba komai idan zasu tafi mukan yi sallama mai kyau har sumbata ta yana yi kafin ya wuce amma na yau 'din yasha banbam.

Inaji ina gani suka yi tafiyar su ban iya na ko yi musu addau'ar da ya bu'kata ba.

Da rana sai ga Hibbah tazo duba ni, wai inji shi ne ta ringa zuwa tana duba lafiya ta kafin ya dawo.

ni kuwa cike da haushi nace ni lafiya ta 'kalau ba abinda ke damuna, duk yadda taso ta nuna min cewa Dr.Mu'een ne ya turo ta amma na'ki sauraran ta, haka ta tattara tarkacen ta tayi gaba.

Ina jin ita ta sanar da shi cewa na'ki amincewa da yamma sai ga 'kiran sa kamar bazan 'dauka ba sai na 'dauka, take kuma sai naji kuka ya kubce min, shiru yayi yana sauraran kukan nawa daga inda yake harda lumshe idanu, yana jina har na 'dan tsagaita sannan naji muryar sa na fa'din" Jikin naki ne?"
Nace" a a".
" To menene kuma na kuka bayan naturo Hibbah ta duba ki kika 'ki amincewa?"

Shiru nayi ban ce dashi komai ba, shine ya cigaba da fa'din" Ki daina nuna kowa cewa ke mai taurin kai ce..kinga Hibbah daban ni daban amma sai da kika sa ta gane taurin kanki".
Da shagwa6a nace dashi
" Ai na warke ne shiyasa".
Ajiyan zuciya ya sau'ke tare da fa'din
" Haka ake so ai"
Sannan ya sake fa'din" mun iso lafiya su Ammi ma na gaida ki".
Da jin sunan Ammi sai wani kukan ya taso min.
Kashe wayar nayi na kifa kaina na cigaba da kuka na, shi kuwa 6angaren sa murmushin mugunta ya saki harda cije gefen baki.

Ashe ko da suka je ma Ammi sai da tayi masa fa'dan wai me yasa bamu taho gaba 'dayan mu ba, miye amfanin tahowar su su biyu su barni acan 'din.

Yah Deen ko tsoron Allah babu yace da ita wai ai nice na'ki binsu, wai banda lafiya yanzu sai dai wani lokaci, yace in ya bar Baby kuma damu na zata yi tayi shiyasa ya taho da ita"
Ya fa'di hakan ne da tabbacin 'karyar sa ta shiga domin yasan ni bazan ta6a musawa ba koda Ammi ta tuhume ni akai.

Wasa-wasa sai da suka shafe kwanaki takwas acan, duk zaman gidan ya ishe ni, ya kan 'kira na kullum sau uku mu gaisa yaji lafiya ta shikenan,  wani lokaci sai ya ha'da ni da Baby tayi ta min shirme.

Har gajiya nake yi da nata surutun sosai nake so ya bani ishshshen lokacin sa amma sam ya 'ki kamar yasan me ke cikin raina.
Chapter 154 · 0% Book details