Sashe 61
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Bangaren Alhaji kuwa ganin na tsaya shiru ne ya sanya shi tambaya ta da fa'din " uwa ta ya akayi ne?"
Sai da na goge hawaye na kafin na ce da shi " wani ne yazo"
Nayi maganar ina nuna hanyar da na shigo kamar wata sokuwa.
Alhaji sai yace " maza je ki ce masa ya shigo, kuma ki daina kukan nan babu abinda ya faru da shi kinji".
Da sauri na juya na ifmsar da sa'kon Alhaji amma ban iya na sake zama da su Zaid ba sai bin bayan likitan nayi, Allah ya taimake ni ma da ya shiga bai tura 'kofar ya rufe ba hakan sai ya bani daman shiga batare da sun lura da ni ba dan lokacin hankulan su yana wajen Yah Deen ne.
Direct wajen Ammi na wuce na jinginu da jikin ta na yi shiru, Ammi kam hankalin ta na ga 'ko'karin da likita ke yi ne na ganin farfa'dowar Mu'een amma duk da haka Ammi bata kasa bani kulawa ba, bata kalle ni ba kam amma da hannun ta 'daya tayi 'ko'karin tallafoni zuwa jikin ta.
Tsawon mintina uku likita na fama da shi kafin ya farfa'do da sakin ajiyar zuciya mai 'karfi.
Ammi da Alhaji Baba duk a fili suka saki hamdala Ammi har tana murmushi inda ta sake tallafa ta....wanzuwar likita awurin ne kawai ya hanata isa ta rungumi 'dan ta cikin jikin ta amma Allah ne ka'dai yasan yanda ta ji da'din farkowar tasa.
A hankali ya bu'de lumsassun idanun sa wanda suke saitin inda muke zaune ni da Ammi.
'Kara waro idanun nasa yayi akan mu saman la66a ya furta _" Amina...."_
Take Alhaji Baba da likitan duk suka juya suka kallo mu.
Ammi kam da bata ji maganar tasa ba ganin sun kallo mu ne sai ta tsorata da sauri ta mi'ke gami da kama hannu na muka isa gaban su tana tambayar su abinda ya faru cikin harshen turanci.
Ni kuwa ido na tsura masa ganin yana dafe 'kirjin sa kuma yana kallo na, a hankali sai na cire hannu na daga na Ammi na tsuguna agaban sa...idona cikin nasa cikin sanyin murya nace " Yah deen baka da lafiya ne?"
Bai amsa ni ba dan haka sai na cigaba da fa'din....kar ka yadda ka mutu irin na Nannen mu kaji...su Saif da Ammi suna sonka kuma idan ka mutu kuka zasuyi baza su 'kara ganin ka ba".
Maganar da nayi ne ya sanya shi rintse idanu da 'karfi sai a lokacin ya fahimci cewa ni 'din ba Aminan sa bace, ya san Aminan sa bata shirmen magana kamar ni.
Idanun sa a rintsen likita ya gwada B.P 'din sa sai yaga bai hau ba...yana cire abin sai ya fara yunkurin mi'kewa da sauri likitan ya tallafo shi har suka mi'ke tsaye.
" Ina zaka ne wai Muhammad?"
Alhaji Baba ya tambaya yana mi'kewan shima... a hankali da rawar murya yace " 'daki... na".
Shiru suka yi masa dukkan su, inda Alhaji Baba ya iso ya kama shi da kyau yayin da likita ya tsaya ya tattari tarkacen sa sannan ya bisu abaya nima ganin Ammi ta bisu sai na bita da sauri.
Shigar su parlourn ne ya sanya su Saif saurin mi'kewa duk jikin su sai ya 'kara yin sanyi da ganin yanayin da 'dan uwan su yake ciki, tamkar ba 'dazun yazo garin da 'kafafun sa ba.
Likita ne ya fara shiga sai ya ri'ke musu 'kofa suka shigo sannan Ammi ma ta shiga, ina 'ko'karin shiga sai Zaidu ya ri'ko hannu na a hankali yace " me zaki je yi ke kuma?"
Ban bashi amsa ba kawai na sanya kuka ina 'ko'karin 'kwatan hannu na ni dai burina ya barni in je..." let her go please Zaid".
Saif ya fa'di yana kallo na.
Take kuwa sai ya sake ni...na kuwa kama hanyar 'dakin na shiga.
Lokacin da na shiga Alhaji Baba na cire mai rigar Jumps da ke jikin sa sai ya rage masa sauran farar singlet ne da dogon wandon kayan....a hankali ya komar da shi ya kwantar Ammi ta dai-dai ta masa pillow akan sa.
Numfashi yake fitarwa da 'karfi wanda duk sanda zaiyi sai kaji ya fitar da sauti har 'kirjin sa na hawa da sau'ka sosai...in kin ganshi a lokacin gwanin tausayi Hafsat tamkar ba shine Mu'eenuddeen 'din Uncle Ja'afar ba".
Nuree ta fa'di tana kallon fuskar Hafsat da murmushi kan fuskar ta.
Hafsat ma murmushin tayi sannan tace " Sharrin zuciya ne ba laifin sa bane ai, kinsan so mugun cuta ce sam bata da da'di".
"Hmm"
Kawai Noor ta ce sannan ta cigaba da bata labarin.
" Allurar bacci kawai Alhaji ya bu'kaci ayi masa kafin gobe dan haka batare da 6ata lokaci ba likitan yayi masa nan take.
Har a lokacin kuma ina tsaye ina share hawaye na, har ga Allah tausayin shi nake ji sosai duk da bansan meke damun sa ba amma yanayin sa ba 'karamin karya min zuciya yayi ba, ga kuma tunanin Nannen mu da ya tsaya min cak a zuci banaso ace shima ya mutu irin na ta a daina ganin sa...har cikin raina nake jin banason hakan sam.
Likita na cire Allurar sai nayi saurin 'karasawa gaban gadon na dur'kushe gwiwa na daga 'kasa tare da kamo hannun sa 'daya na ri'ke da duka hannuwa na.... na cigaba da kuka na.
Idanun sa dake lumshe ya bu'de a hankali, yana kallon fuska ta sai yayi murmushi mai kyau mai sanyi mai kuma tsaywa a zuciyar wanda ya san muhimmancin ta.....dishi-dishin da yake gani a lokacin ne ya sanya shi kasa tantantace kamanni na...a hankali ya bu'di bakin sa ya ce da ni ".....Amina ai baki mutu ba ko?....ai dama nasan bazaki tafi ki barni ba..."
Yayi maganar yana kallon fuskata.
Ban damu ba duk da sunan Amina da naji ya 'kira ni da shi ban kuma san manufar hakan ba, ni dai fatana kar shima ya mutu irin na Nannen mu, bansan me yasa na damu da hakan ba tun a wancen lokacin...nafi son rayuwar sa fiye da rashin sa duk kuwa da cewa ba wani 'kwa'k'karan ala'ka ce tsakani na da shi ba.
Hannun sa naji kan fuska ta yana share min hawaye na batare da ya sake magana ba...su Ammi kam kallon mu suka tsaya yi da mamaki jin sunan da ya 'kira dashi, wanda sai a lokacin ma Ammi da ta 'kura min ido sannan ta fahimci kammanin dake tsakani na da Nanne, bata ta6a lura da hakan ba sai yanzu, sosai kuma muke kama da ita abinki da jini kinsan ko babu kamar ma dole sai an gani ta wani 6angaren, sai dai haske kawai da Nannen mu ta fini dashi da kuma karan hanci....
Yana gama share min hawayen ya sau'kar da hannun sa tare da sake lumshe idanun sa a hankali inba a kusa da shi kake bama baza ka ta6a jin abinda yace ba...ni dai dake tsugunne gaban sa naji yace "....do not ever leave me...plea...se?"
Daga haka bai sake magana ba.
Alhaji ne ya tambaye ni abinda yace dan yaga bakin sa yayi motsi, ba ma iya fa'da zanyi ba dan ban fahimce shi ba a lokacin da yake ban gama koyon turanci ba ni, Saif ne ma yake 'ko'karin koya min kuma ya kan min magana da shi wani sa'in shiyasa nake 'dan ji ka'dan-ka'dan....so naji abinda yace kuma zan iya fa'da a baki amma bansan nufin sa kan hakan ba.
Ina shirin maimaitawa Alhaji Baba abinda naji ya fa'da ne sai Ammi ta riga ni fa'da masa...ashe itama taji.
Kallon sa kawai Alhaji yayi sannan ya kalle ni, ni kuwa ban ma san yana yi ba.
Suna ganin ya samu baccin Alhaji Baba yayi godiya wa likitan anan yake sanar da shi cewa babu mamaki ma ya tashi da 'dan 'karfin jiki koma babu ciwon tunda da farin ciki yayi baccin cuz har a lokacin idan ka dubi fuskar sa zaka hango kwantaccen murmushi akai.
Godiya sosai Alhaji Baba ya sake yi masa sannan ya sallame shi, tare suka fita daga 'dakin ya raka shi, nima suna fita na mi'ke na fita ina goge fuskata.
Ammi ce dai bata fita ba sai da ta 'dan kintsa 'dakin tukunna, wanda ga rin hakan ne ta ci karo da jakar da ya saka kayan da siyawa Aminan sa.
Ammi zazzage su tayi da mamaki take 'dagawa take gani, sosai tausayin sa ya 'kara kamata dan a zahiri zaka fahimci zazzafan soyayyar da yake yiwa yarinyar.
Tun lokacin da na fito sai na isa gefen Saif na raku6u jikin sa nayi shiru...shima shirun yayi, Zaid kuwa da idanu kawai ya bini.
Cikin sanyin jiki Saif ya tambaye ni " wai meke faruwa ne?"
Sai na bashi amsa da fa'din " Nima fa bansani ba, amma naga yayan can ba lafiya kuce masa kar ya mutu ya barku irin na Nannen mu...Ammi ma tana son shi kuma?"
Zaid dake gefe ne azafafe ya bani amsa da fa'din " an gaya miki mutuwa zai yi ne...ke kin fiya shirme wallahi".
Shiru nayi ban kula shi ba haka ma Saif da ya rafka tagumi.
Wajen sai yayi tsit bamu sake magana ba.
'Bangaren Ammi kuwa maida kayan tayi cikin jakar sannan ta fito da shi ri'ke a hannun ta, kallo 'daya tayi mana sai ta 'dauke kanta kamar ance ta juyo kuma sai ta waigo take ta ha'de gira ganin yanayin zama na da Saif.....Da 'dan 'karfi ta ambaci sunana sai na waigo na kalle ta," ta so ki biyo ni"
Ta ce dani tare da juyawa ciki.
Sai da ta kai kayan ta 6oye su sannan ta dawo gare ni....ba ta son ya sake gani balle har ya tuna da cewa ya siya mata kaya amma kafin ya isa gare ta labarin mutuwar ta ya riske shi dan haka dole ta 6oye masa kayan daga idanun sa.