Sashe 122
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni kam kuka nake yi sosai har ban iya amsa addu'ar da yai 'din ba shi kansa Baban mu jikin sa sanyi yayi daga yanayin muryar sa zaka fahimci damuwar da yake ciki.
Ummah ta da kanta ta ringa lallashi na har nayi shiru bacci ya 'dauke ni ajikin ta...tausayi na take ji amma babu yadda zatayi, ita dai bata san me zata je da su Ammi ba...duk abin nan tarasa matsayin da ya kamata ta bashi..shin so ne ko kuwa...ta wani fannin akwai wani haske tattare da kasancewar mu tare da su amma wani 6angaren sai dai ace Alhamdulillah kawai...sau tari ta kan hango tsagwaron son kai cikin lamarin su amma sam hakan baya bayyana kansa a fili 'kauna ta zahiri kan lullu6e komai...dan duk abinda ke faruwa da tsigar zallar so suke bayyanuwa..ji take
da tana da iko da bazata ta6a yadda da batun zama na da Mu'een ba amma babu yadda zatayi ha'kurin nan dai sai addu'ah kuma....fatan ta Allah Ubangiji ya shirya shi yasa Hudah ta kasance Haske cikin rayuwar sa".
Ana gobe zan koma gidan Ammi aka kawo kayan lefen aure na akwati set biyu masu kyau da 'daukan hankali, ni kam ma ko kallo kayan ba su ishe ni ba inaji anata zuzuta kyan kayan da kuma yada habaicin wai _dama haka ake so kuma an samu_ inji mutane...Babu wanda ya tanka su haka kowa yazo zai gani ya fita da maganar kayan a bakin sa.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
💕💕 ~*This page is 4u Dear Zainab Kabir Ingawa...Alkhairin Allah ya kai mk duk inda kike...nagode sosai da 'kaunar ki gare ni.*~💕💕
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *59*
Addah ta Maryam ma tazo da wasu 'yan uwan mu a hakan ma abin yazo ne cikin lokaci 'kan'kani amma duk da haka ba laifi gidan mu ya tara jama'ah ka'dan.
Itama Addah Maryam tayi mamakin faruwar lamarin yanda yazo agaggauce, ta yi 'ko'karin ganin ta samu cikakken bayani daga bakin Ummahn mu amma hakan bai samu ba, sai da suka zauna da Addah Saudah shine tayi mata bayani gamsashshe a fahimtar ta, tace Baban mu ne ya matsa akan dole sai an kai ni 'dakin na saboda labari ya iske shi cewa Mijinnawa shine ke da alhakin cikin dake jikin Ma'u 'yar gidan malam Barau shiyasa Baban mu yace agaggauta kai masa matar sa a tunanin sa ko laifin nasu ne da tun farko ba su bashi matar sa ba suka bar ya a gida..inda ta 'kara da fa'din ni.nama yi mamaki wallahi ban zaci Baban mu zai kuma amincewa da zaman Hudah tare da yaron ba bayan jin abinda ya faru sai ga shi da kansa kuma yayi umarni da akaita gidan sa batare da ya koyi tunanin me hakan zai haifar ba".
Baki kawai Addah Maryam ta ta6e tare da kawar da kanta gefe bata iya ta furta komai ba, sai dai har cikin ranta bata ji da'din maganar ba sam...aganin ta ba haka ya dace ayi ba..kamata yayi a bar Hudahn agida tukunna inma ba zasu iya raba auren ba har sai an tabbatar da shiryuwar sa kafin abrta zama dashi baya ga haka taya za'ayi a 'dauki yarinya 'karama kamar ni abawa mutumin da bai san ciwon kansa ba Baban mu yana nufin bai damu da abinda ya farun bane ko me? ..taso su tattauna maganar da Ummahn mu amma bata samu fuska ba hakan yasa dole ta ha'kura tayi shiru da bakin ta.
Ana gobe za'a kaini gidan Yah Deen Saif yazo gidan mu shi ka'dai hr naso ma nayi msmskin ganinsa shi ka'dai 'din amma sanin ba'kin hali irin na Zaidu yasa mamaki na ya kau ...y Saif yasha Jumpa milk colour da hula kamar wani babba, fuskar sa fayau sai 'dan 'kasumba da ya fara tarawa, yayi kyau sosai abin sa...a 'dakin Baban mu aka masa masau'ki inda aka yi 'kirana bayan sun gama gaisuwa da Ummahn mu.
Jin cewa Saif necyazo ya sani tahowa cikin tsananin farin ciki, jiki na da doguwar rigar material sai 'dan 'karamin ba'kin mayafi da na yane kaina da shi...fuska ta da fara'a muka gaisa da shi na tambayi su Ammi da Zaidu..yace min lafiyan su qalau.
" Meya sameka kai in kuma?"
Na tambaye shi ina kallon fuskar sa.
Take ya amsa ni shima da tambayar" Me kika gani?"
Nace" Kamar baka da lafiya".
Yace" Ni lafiya ta qalau".
Ya 'karashe maganar yana suman shafo kansa.
Shiru nayi ban kuma fa'din komai ba cikin rains nake tunanin abinda zai iya sashi canzawa haka cikin sau'ki dan nasan Saif ba haka yake ba...tashin farko tunanin na kan Yah Deen ya sau'ka cuz a sani na shi ka'dai ne ke takurawa su Saif a gidan..baki na ta6e cikin raina nake fa'din" Har yanxu ba zai canza hali ba".
Lallen dake zane a hannu na naga yana kallo ban damu ba sai ma nayi murmushi da fara'a ta nace 'dazu da safe aka zana min yayi kyau ko?..har an min kitso ma 'kanana zafi ma kaina yake min har yanzu".
Ido ya tsura min yana kallon fuska ta kamar wanda ke son gano wani abin acikin idanu na....Nima 'din sai nayi shiru ban kuma cewa komai ba.
Cikin sanyi ya ambaci sunana sai na amsa nima a hankali jin yanda yanayin muryar sa ya koma.
Yace
" Hudah dagaske Yah Deen mijinki ne yanzu?"
" Nima haka naji an fa'da...amma bansan lokacin da akayi auren ba".
Na bashi.masa bayan yanayi na na canza izuwa na damuwa.
Idanu ya lumshe tare da yin 'kasa da kansa hannun sa cikin gashin kansa, kamar an tsikare shi kuma sai naga ya mi'ke tsaye hannun sa ri'ke da hular sa yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yake ce min" Zan tafi gida...dama nazo ne kawai in dan ganki inga matar Yaya na".
Yayi maganar yana me 'ka'kalo murmushi.
" To bazaka tsaya in kawo maka ko ruwa ba?"
Na fa'di ina mi'kewa tsaye da hanzari na.
'Daga idanu yayi ya kalle ni, sai da ya juya ya fara tafiya sannan ya furta..." Karki damu Matar Yayah.. am ok.."
Biyo shi nayi abaya ina 'kun'kunin sunan da yake 'kira na da shi, a fili kuwa cewa nayi" Sai nagaya ka da Ammi tunda ka'ki zama ka ci komai".
Murmushi yayi ta'kaitacce sannan ya waigo idanun sa yasa cikin nawa idanun yana murmushi yace" Idan naje gidan ki ai zan ci".
Dajin haka sai na fara buga 'kafafu na a 'kasa tare da tura baki.na gaba...zan yi magana yayi saurin tara na da fa'din" Common..me hakan kuma...ke fa yanzu kin girma...gobe-gobe za'a kaiki 'dakin mijin ki ko so kike ace yarinyar Ammi shagwa6a66iyace".
Daina abinda nake yi na cigaba da kallon sa..sai ya juyo da kyau ya fuskance ni gira ya 'dage sama sannan yace" Kinsan me nake so dake 'yar gidan Ammi?"
Kai na girgiza alamar a a sai yace" Ha'kuri zakiyi...ai nasan kinsan halin Yah Deen da kyau ko?"
Wannan karon kam shiru nayi ina mai cigaba da kallon sa.
" Kiyi ha'kuri ki zauna lafiya da mijin ki kinji?...kuma nayi al'kawari kullum zan rin'ka taya ki Addu'ar Allah ubangiji Kar ya bashi ikon cutar mana dake kuma ya daidaita miki hankalin sa...ko baki so?"
Ban bashi amsa ba still nayi shiru ina jin yanda cikin idanu na ke tsatstsafo da ruwa ...Saif sai yayi murmushi ka'dan sannan ya cigaba da fa'din" Kar kiyi min kuka ni...ai nasan kina so ko...to ubangiji Allah ya baki ha'kurin zama da shi...Allah ya baku zaman lafiya ya sanya muku albarka cikin auran ku..ki kwantar da hankalin ki insha Allahu bazaki yi danasanin auren Yayah ba".
Daga haka ya juya tare da sanya hular sa akansa ya fita batare da ya jira jin amsar da zan bashi ba...yana saka takalmin sa ya ke sake fa'din kice da Ummah na wuce kawai dan naga tana cikin hidima kar mu raba mata hankali".
Ganin dagaske tafiyar zaiyi ya sani saurin fa'din" Ka gaida min Ammi na" Abinda kawai na iya fa'di kenan ban kuma san dalili ba sai naji zuciya ta gaba 'daya ta karaya kafinvna ankara sai jin idanu na nayi suna tsiyayar da hawaye.
Saif bai sake yadda mun ha'da idanu ba yayi gaba abinsa, har ya 'karasa fita daga gidan kuwa ban kuma cewa komai ba illah bin bayan sa da na tsaya yi da kallo ina tsaye daga bakin 'kofa ina share hawaye na.
Saif yaro ne ba wani babba ba amma yana da nagartar da idan ka zauna da shi sai ya birke ka..wani lokaci har zaka iya mantawa da 'karancin shekarun sa, musamman ma idan magana ta fahimta ta ha'da ka da shi...ko cikin yaran Alhaji Baba Saif ne wanda yafi jin natsuwa da shi sosai...da suke je boarding school 'dinnan ma sai abin nasa ya 'karu, halin girma da mutuntaka duk suka shige shi ga su dama akwai jikin girma ba laifi.
Ni dai 'dan maganar nan da muka yi da shi sai naji wani iri tamkar wanda akace min daga yau 'din bazan sake ganin su ba...tun daga yanzu har na fara missing presence na su..hakan yasa na koma cikin 'dakin Baban mu na kwanta na dinga rizgar kuka na wanda babu mai lallashi na...da 'kyar na samu kukan ya tafi har bacci 6arawo ya sace ni.