Sashe 134
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga su ban kuma 'kiran kowa ba kawai na saka wayar tawa acaji...ban kuma bi ta kanta ba na tafi sha'ani na har bayan kusan 2hrs kafin nazo na cire ta a charge nan naci karo da missedcall 'din Baban mu guda 'daya wanda aka 'kira 57 mins back...ina shirin sake 'kiran sa sai naji Ammi na zuba salati daga parlour a 'dimauce nan hankali na ya kasu gida biyu.
Da sauri na mi'ke na nufi parlourn na sami Ammi tsaye da hannu dafe da 'kirji tana fa'din" Alhaji yaushe hakan ya faru?"
Daga wannan maganar na fahimci da Alhaji Baba take wayar.
Tunawa nayi da lokacin da ya bar gidan nan bai wani jima ba..." to me kuma ya faru?"
Na tambayi zuciya ta.
Ban ji amsan da aka bata daga 'dayan 6angaren ba sai gani nayi kawai ta koma ta zauna bisa kujera tana girgiza kanta tare da fa'din _Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un_ 'karasawa nayi gaban ta da sauri na tambaye ta" Ammi me ya faru?" " Bakomai" Shine amsar da ta bani sai kuma naga hawaye na gangaro mata sirara, haka da na gani sai ya sake 'dage hankali na sosai take nima na saki kuka ni kam har da sheshsheka dan ganin Ammi na da kanta tana kuka...ina yi ina sake tambayar ta abinda ya faru.
" Haba Ammi da kanki...?"
Naji muryar sa kamar daga sama yana fa'din haka daga bakin parlour.
Ammi bata kula shi ba haka nima a hankali ya 'karaso ya zauna gefen Ammi sai kuma ya dafe kansa..." Ni da nake kuka ina tambayar Ammin ni dakawa tsawar inyiwa mutane shiru sannan yace in tashi maza inje in shirya in fito zamu wani wuri".
Haka yace dani yana kallo na.
Duk da nayi mamakin maganar tasa amma sam koka'dan banga fuskar da zan tambayi inda za'a je ba.
A hankali na tashi ban bar kukan ba haka kuma ban fasa mamakin shirin da yace inje inyi ba.
Sharp-sharp na shirya na fito haka ma Ammi, tare muka fito dashi babu mai cewa 'kala cikin mu duka, Yah Deen ne da kansa ya sau'ke mu a 'kofar gidan Ummah ta nan na tarar da wajen gidan duk mutane, take zuciya ta ta tsinke haka kawai naji tsoro ya shige ni sosai.
Ammi na kalla na je fa mata tambayar abinda ke faruwa anan 'din cikin ki'dima sai tace min bakomai.
Banji amsar Ammi ya gamsar da ni ba dan haka sai na bu'de motar cikin sauri nayi gaba inda na tunkari mashigar gidan mu.
Abinda kunnuwa na suka fara cin karo da shi shine sautin koke-koke.
Da mamaki na 'karasa cikin gidan nan tarar da Addah ta kamar ranta zai fita saboda yanda ta fita hayyacin ta tana kuka..kukan nima na fara a ki'dime na isa gare ta na zube kan gwiwoyi na" Addah.."
Nace cikin kuka..Abinda ta fara furtawa shine" Baban mu...Baban mu Hudah, Allah ya kar6i ran Baban mu da safiyar yau 'din nan".
Cak kuka na ya tsaya na bu'de baki ina kallon ta da mamaki har da 'kan'kance idanu na...lokaci guda sai kuma na jijjiga kaina nace" Kai Addah ba shi ba dai, sai dai wani, 'dazun nan fa naga 'kiran sa cikin waya ta ina ma shirin 'kiran sa ne sai wani abin ya 'dauki hankali na ta ya kuma za'a ce Allah ya kar6i ransa".
" Shine mana Hudah a asbiti fa suka kwana...."
Ta sake bani amsa da alamun tabbatarwa.
" Nayi waya da Ummah amma bata sanar da ni ba kuma..."
Ban 'karasa maganar ba nayi shiru sakamakon tuno yanayin yanda naji muryar Ummah da safennan da na 'kira ta.
" Ke nan dagaske Baban mu ne ya rasu?"
Na sake tambayar zuciya ta.
Wani kukan ne ya 'kwace min mai tsuma zuciya...
Allah sarki rayuwa, ashe duniyar bakomai bace ga 'dan Adam...Allah ya ji'kan Ban mu da Rahama Allah yasa aljannar Firdaus ta kasance makomar sa ta har abada.
Ha'ki'ka munyi rashi babba..
A can Jos akayi jana'izar sa aka kaishi gidan sa na gaskiya da kyakkyawar shaida a bayan sa.
Su Alhaji Baba da su Yah Deen da sauran 'yan uwa duk can Jos 'din suka je sannan washegari suka dawo.
Su Zaidu ma sun zo gaisuwa inda suka shigo hatmr cikin gida suka gaida Ummah ta da sauran 'yan uwa.
Ammi kuwa dama kullum muna tare, ta kan zo da safe da yamma ta koma gida sai wata goben kuma.
Kwana na biyu a gidan mu da wata safiya da Ammi zata zo sai ta taho min da waya ta.
Ina kar6a sai naji hawaye na gangaro min a hankali musamman da na tuna 'kiran da na gani na mahaifi na na 'karshe.
Shiga nayi cikin wayar na sake dubawa wani hawayen na sake zubo min ina tuna mahaifi na da karamcin sa...Ammi ko da taga haka sai ta ce da ni da wayar zata koma ai in dai haka zan riga yi...".
Kife wayar nayi kan 'kirji na na juya mata baya na cigaba da share hawaye na.
11 da 'yan mintina na safiya lokacin ina can cikin 'dakin Ummahn mu ina kwance ina tunani, gefe na wasu ne daga cikin dangin mu yawancin su matasan 'yan mata ne kamar ni suna 'yar hira...Vibration naji waya ta nayi na neman agaji lokaci guda sai naji zuciya ta ta tsinke sanadiyan tuno Baban mu da nayi saboda da jin dirin wayar shi ya fara zuwa raina amma koda na duba sai naga ba'kuwar number ce ba ta shi ba.
Ban 'daga ba har ta tsinke ina kallon ta zuciya na dokawa, take wani 'kiran ya sake shigowa wannan ma ban 'daga sai da ya kusan yankewa kafin na 'daga.
Shiru nayi bayan na sada wayar da kunne na.
" Ya dai"
Da naji an fa'di daga 'dayan 6angaren ne ya sanyani saurin fahimtar wanda ke 'kiran nawa.
" Bakomai" nima na bashi amsa a ta'kaice ina murza idanu.
" Kina lafiya ko?"
" Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi.
" Ya ha'kuri kuma?"
" Alhamdulillahi".
" Har yanzu kina kuka ko?"
" A a"
" ance min kuka kike yi kullum"..
Shiru nayi ina sake jin idanu na na tsatstsafo da hawaye..taya bazan yi kukan rashin Mahaifi na ba...na ayyana cikin zuciya ta.
" Kina yi masa addu'a kuwa".
Naji ya sake tambaya ta.
Da" Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi.
Sai yace " Yauwa abinda zaki na yi masa kenan yanzu ba yawan kuka ba kinji?"
" Uhum"
" Allah ya ji'kan sa da Rahama"
" Ameen"
Nace a hankali.
" Ina Ammi?"
Ya tambaye ni sai nace
" Tana waje..bari in kai mata"
Saurin dakatar da ni yayi da fa'din
" a a barta anjima zan 'kira ki kinji".
" Uhum"
Daga haka ya yanke wayar...ni kam ri'ke ta nayi a hannu na ina binta da idanu na" _Yah Deen_ ".
Na furta cikin zuciya ta,
ji nake tamkar wani ne daban ba shi ba.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *65*
Mamakin sa be 'kara kamani ba sai ranar da aka cika 7days da rasuwar Baban mu ranar kamar daga sama naji ana fa'din wai ga Deeni mijin Hudah sun shigo cikin gida gaisuwa.
Ina 'dakin Baban mu ni da wasu 'yan uwan mu da basu wuce sa'anni na ba, su biyun su ma suke hirar su ban fiya saka baki cikin maganar su ba, da jin abinda aka fa'din kuwa haka kawai sai naji na mi'ke tsaye ta kafan labile na le'ka nan na hango su dur'kushe suna gaisuwa shi da abokan sa guda uku, ni kam ma ban tsaya na lurako da su waye yake taren ba akan sa ka'dai na tsaida idanu na.
Tun ranar da ya 'kira ni a waya bai sake 'kira na ba, na kan yawaita tsammanin ganin 'kiran sa ya shigo cikin wayata amma shiru kwana hudu kenan rabo na da ko jin muryar sa, ban ta6a tsammanin cewa nayi kewar sa ba sai yanzun.
Kaina na jingine daga jikin bangon gefen 'kofan na bar kallon su, ko 'yan matan da nake tare su da a 'dakin ma babu wacce ta bi ta kaina da yake dama ba wani hira sosai ke shiga tsakanin mu ba, hakan yasa suka cigaba da hirar su batare da sun kula da yanayin da nake ciki ba... ban san cewa na shiga dogon tunani tsaye a wurin ba har sai da naji ana 'ko'karin shigowa ciki daga waje sannan na dawo hayyaci na...Addah ta Maryam ce ta shigo" Yauwa ashe kina nan ma...".
Ta fa'di tana 'kare min kallo" Me ya sameki kuma Hudah?"
Ta 'kara tambaya ta da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta.
'Kasa nayi da idanu na sannan na bata amsa da fa'din" Bakomai Addah".
Bata ce dani 'kala ba sai kawai ta bi ta 'kare min kallo sama zuwa 'kasa sannan ta saki ajiyan numfashi mai sanyi" Mijin ki yazo zasu shigo, abokan sa ne inajin suke son gaida ki".
Bata tsaya ta saurari jin amsa ta ba kawai ta juya ga sauran dake 'dakin tace" Biba ku kintsa ba'ki zasu shigo yanzu".
" Toh". Suka bata amsa da shi cikin ha'din baki daga haka naga ta juya da niyyan barin 'dakin, yayin da naji 'kirji na ya ri'ke ni haka kawai ban san dalili ba, tsintan kaina nayi da tambayar" Wai da gaske ne zasu shigo 'din?"
Fat fat fat naji zuciya ta ta harbawa lokaci guda, ban iya nace da Addah ta komai ba har ta 'karasa barin 'dakin, a hankali na lumshe idanu na sannan na bi 'dakin da kallo a tsanake.
Ba laifi 'dakin nasan koma waye za'a iya kar6ar sa a ciki batare da damuwar komai ba, balle Yah Deen da abokan sa ka'dai.