← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 211

Sashe 194

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa lokacin kuwa ji yake tamkar ya nutse cikin 'kasa saboda tsananin kunyar da ta kama shi...gefe guda ga 'kiran da Jiddah ke mai daya sake takura shi..karo na 'karshe da ta 'kira sai ya ciro wayar a 'dan hassale yace da ita" Jiddah plz zan 'kira ki an jima".
Wannan maganar da yayi matan ne ya sanya 'kiran da take yi masan ya kasance na 'karshe cuz ta fahimci yana bu'katan natsuwa ne.
Wanda shima Abban Jiddah da gama fa'din hakan sai ya maida wayar cikin aljihu yana sake jin babu da'di..wannan wace iriyar 'kaddarace haka? ace duk yanda yake ji da kansa ya tara dukiya masu 'dumbin yawan nan, yana rayuwar sa yadda ya ga dama lokaci guda 'kaddara ta 'dauko shi da 'kafafun sa ya tako ya zo ga tashin hankalin sa...kuma ma wai shi ke tafe da batun aure, shi mahaifin 'ya mace wanda shi yakamata azo gareshi neman aure sai gashi abin ya juye masa, gashi ma a yanda yasan Taheer yasan waye shi yana da ya'kinin ko da ace Jiddah ce mace ka'dai da ta rage a duniya yasan Taheer ba ze ta6a yadda ya ha'da jini da shi ba...in dai har ya gano waye shi cuz yasan abu me mai wahala ya manta wancan lamarin.

Cikin zuciyar sa ya fara tunanin mafita, a ganin sa gara kawai ya tashi ya tafi tun kafin asirin sa ya 'karasa tonuwa in yaso sai yaje yasan me ze ce da Jiddah...
Tunanin sa ya yanke ne lokacin da ya tuno irin tashin hankalin da Jiddah ta shiga kafin tahowar sa, me kuma ze iya faruwa idan ya koma mata da batun da ba shi take tsammani ba....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...hakan ya furta a fili batare da ya farga ba...goshin sa ya dafe da yake jin kamar kansa na juyawa.

Amsa kuwwa sunan Taheer yake masa cikin 'kwa'kwalwa, yasan Taheer ya kuma san irin kafiyar sa, yasan taurin rai da yake da shi, ya kuma san muddin Taheer ya gama fahimtar waye shi ba zai bar shi ya tafi haka nan ba..me ya kamata inyi?
ya tambayi kansa.
Duk yadda yake ji da kansa da dukiyar sa yau gashi gaban Taheer komai ya kunce masa, ji yake kamar ba shi ne wannan me fa'da ajin ba.
Sosai kwarjinin Taheer ya cika masa idanu, tsoro da fargaba duk sun mamaye shi...sai dai duk wannan ba damuwa bane kamar idan yayi kuskuren da Taheer ya 'dago waye shi dole yasan abinyi kafin faruwar hakan,

Cikin zuciyar sa ya gama yanke shawarar da yake ganin itace mafita agare shi.

Duk wannan abin da ke faruwa Alhaji Baba bai ce da shi 'kala ba, tsawon lokaci yana zaune yana jira ne yaji abinda ke tafe dashi amma hakan ya kasa faruwa, fuskar Alhaji wasai banda bayyananniyar murmushi dake kwance a fuskar bakaka fahimci komai daga 6angaren sa ba....

Duban.sa yake yana 'karawa cike da mamakin sa, yanda yaga ya rikice in sosai yake bashi mamaki, har zuwa lokacin da yaga ya 'dan sawa zuciyar sa natsuwa..duban Alhaji Baba yayi cikin dakiya da nuna alamun kuskure yace" Alhaji afuwa dan Allah..wallahi ina jin kuskuren fahimta muka yi muka zo gare ka....sai yanzun na fahimci ba kai in nake nema ba...".
Yana gama fa'din hakan ya mi'ke tsaye gami da bawa Alhaji Baba hannu.

Mi'ka masa nasa hannun yayi yana murmushi me 'kayatar wa suka yi musabahar bankwana.

Abban Jiddah be jira komai ba kawai ya sa kai yayi gaba abinsa cikin sauri da fatan Allah yasa kar Taheer ya gane sa...shaf ya manta da cewar tun farkon ganin Alhaji Baba da yayi ya ambaci sunan sa, zaton sa ko duk cikin zuciyar sa ne yayi hakan.

Tsaye Alhaji Baba ya mi'ke yana duban bayan sa da mamakin sa, maganar sa 'karshe 'din sam bata gamshi Alhaji ba, sam sai yaji bai yadda da shi ba, 'kila wani shirin zai koma yi akansa tun da har ya gano inda yake rayuwa, mamakin sa Alhaji Baba ke yi domin ya fahimci Barrister tamkar mara hankali ya 'dauke shi, me yasa yake tunanin shi ba zai gane sa ba, in har shi da yayi abin ma bai manta kammanin sa ba me yasa kuma shi zai iya mantawa da nashi kamannin.

Taku biyar yayi ana shidan Alhaji Baba dake kallon bayan sa bai bari ya 'karasa ba ya furta" _Barrister Kido_ ...!"
Yana murmushi ya fa'di hakan da muryar da ya tabbatar zai ji sa.

Cak Abban Jiddah ya tsaya dai-dai da harbawan da zuciyar sa tayi, salati ya maimaita atake kusan sau uku da be masan yayi su ba.

Takowa Alhaji Baba yayi ya dawo gaban sa hannuwan sa duk na cikin babbar rigar jikin sa yayin da Abban Jiddah ya sake rikicewa jikin sa na rawa ya kauda idanun sa gefe abinka da marar gaskiya.
Alhaji Baba kam be damu ba bayan kallon 'yan da'ki'ku da yayi masa sai yace da shi yace da shi" Barrister kenan...bayan tsawon lokaci da rabuwar mu sai gashi kallon farko da kayi min ka fahimci waye ni me yasa kake zaton ni bazan iya gane kamannin ka ba..? U thought haka kawai zan iya mantawa da kai ne bayan duk abubuwan da suka faru abaya?"

Shiru Abban Jiddah yayi ya kasa furta komai, 'kafafun sa yake jin tamkar baza su iya 'daukan sa ba.
Alhaji Baba ne ya cigaba da fa'din" Ai in har zaka iya fahimtar ko ni waye tsawon wannan shekarun nima kasan bazan gaza fahimtar waye kai ba...amma yanzu duk ba wannan ba i know wani abin muhimmi ne ya kawo ka gare ni kuma bamu kai ga tattaunawa ba ka tashi...dan Allah ka manta da baya mu koma mu 'karashe maganar da ta kawo ka".
Zai yi magana Alhaji Baba yayi saurin dakatar da shi da fa'din" Please Barrister...".
Inda yayi maganar tare da nuna mai hanya fuskar sa ba yabo ba fallasa bazaka ta6a tunanin ganin Barrister ya ka'da shi ba.

Haka badan yaso ba Abban Jiddah ya juya suka koma suka sake zama, shiru ya 'dan biyo baya kowa tunanin da yake sa'kawa daban ne, sai da Alhaji Baba ya sake ce mai ina jin ka kafin ya bu'di baki, madadin ya fa'di abinda ke tafe da shi a a sai ya fara ro'kon Alhaji Baba gafara kamar zai yi kuka...sosai nadamar bazata ta kama shi, yanzu ne ya fahimci cin amana bata da rana sam.

Gashi tun ba'a je ko'ina ba Allah ya kama shi da dasawa 'yar sa 'kaunar yaron da yaci amanar mahaifan sa da da'dewa...bai 6oye komai ba duk ya sanar da Alhaji Baba hadda batun da ya kawo shi, nan ma ya 'karashe da ha'dawa da neman afuwar su.

Duk abubuwan da ya fa'di 'din babu ba'ko wurin Alhaji Baba, amma batun Jiddah sosai ya ka'da shi.

Cikin.zuciyar sa ya furta ' _karshen zamani_ sosai yayi mamakin wannan lamari, yasan a haife Barrister ya girme masa dan ko lokacin da ya sanshi ma ya san yafi shekaru talatin a lokacin kawai haihuwa ce Allah bai bashi da wuri ba amma sam bai ji da'din jin wannan labarin ba.

Zurfafa tunani yayi a lokacin, a zahiri shiru Abban Jiddah yaga yayi har sai ya fara tabbatar da tunanin sa na cewa Taheer ba zai amince da wannan batun ba.

Alhaji Baba kam can cikin rayuwar Deen ya tafi da tunanin sa, idan bai manta ba akwai sunan Jiddah cikin labarin sa da ya basu, kenan itama tana 'daya ne daga cikin irin 'yan matan da yayi abaya.

Murmushin gefen baki Alhaji yayi, sai kuma yaji tausayin iyayen nata ya kama shi, abin takaici ne ace ga abinda 'dan ka ko 'yar ka suke aikatawa musamman abu dangin Zina sa6on mahalicci shi ya san ciwon hakan ya kuma yasan Abban Jiddah ba zai so jin wannan batun ba, baya ga haka ma a idanun sa zaka fahimci zallar 'kaunar da yake yiwa 'yar sa, babu mamaki itace mafi soyuwa a zuciyar sa cikin 'ya'yan sa shiyasa ma har ya iya amince mata kan wannan batun da yazo masa da shi wanda ya tabbatar ba kowa ne zai iya irin hakan ba.

Muhammad 'dansa ne na cikin sa amma zai iya rantsuwa akan bai bar Jiddah haka nan ba, matu'kar ya ta6a neman ta to kuwa babu mamaki itama tabi sahun su Husnah ne...kuma abu ne me wahala ya amince da auren ta....

Bai kai ga 'karasa tunanin ba ya jiyo muryar Barrister na sake ro'kon sa, wannan karon kam mamakin sa 'karuwa yayi akan na baya musamman saboda ganin gwiwoyin Barrister da yayi zube a 'kasa, fuskar da muryar da muryar sa duk sunyi rauni da alamun ro'ko yake fa'din" Taheer dan Allah kar ka tuna abinda na aikata muku abaya..kaji 'kaina ka amince da wannan ha'din, wallahi Jiddah ba hali ne da ita ba halin mahaifiyar ta tayi..kuma basu san komai game da hakan ba a yanzu idan ka 'ki amincewa bansan yadda zanyi da ita ba, tsoro nake ji kar na rasa ta Taheer ita ka'dai Allah ya bani bani da kowa sai ita..idan dukiyar ku ne i promise u zan dawo maka da ita gaba 'daya ni dai ka amince kawai shine damuwa ta...".

Alhaji Baba bai yi mamakin jin hakan daga bakin Barrister ba, domin da kanshi ma ya zargi hakan bayaga haka me ze sashi biyewa batun yara har ya iya yada girman sa haka nan.

Ro'kon sa yayi akan ya tashi ya koma ya zauna amma Barrister ya'ki cuz shi a ganin sa ai bashi da sauran girma kuma tunda har ya kasance maciyin amana, ko da kwanciya ne zai iya yi a wannan lokacin matu'kar zasu yafe masa su kar6i batun Jiddah.

Da 'kyar Alhaji yasa shi ya koma ya zauna sannan ya tabbatar masa da cewa shi bashi da matsala ta 6angaren shi kar ya damu in har Muhammad ya amince bakomai.

comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *88*
Chapter 194 · 0% Book details