← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 211

Sashe 136

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da hakan ma sosai naga ta nuna alamun mamaki 'karara kan fuskar ta, a fili ta furta dama ai irin wannan auren galibi haka yake kasancewa sai dai in mutun ya dage sannan yake samun kwanciyar hankali, amma kafin hakan sau an kai ruwa rana, tace shiyasa sam baku damu da junan ku ba, nan ta fara yi min fa'dan wai ai nima da laifi na, wannan ganganci ne ne na aikata, me yasa ni idan zaman ya 'daure minbaki bazan nemi shawarar kowa ba, tace mu miye amfanin mu matsayin mu na yayyanki ai dole ne muyi iya 'ko'karin.mu wajen ganin daidaituwar farin cikin gidan ki, amma kika 6oyewa kowa, nasan ko Ummah bata san komai ba game da zaman kun nan ba ko?"
Na girgiza kaina tace" Ammi fa?"
Sai nayi shiru..masifa ta hau ni da shi me yasa tunda ya tafi ni ban 'kira sa ko a waya ba? haka kika ga ake yi ne?"

Shiru na sake yi mata cuz ni kaina ban san dalilin ba.
Sai da ta daka min tsawa kafin na 6ata rai nace" Addah shima fa bai 'kira ni ko sau 'daya ba tunda ya tafi".
" 'Kaniyar ki....wallahi Hudah tun wuri ki dawo hankalin ki ki san me kike yi..tun ranar da aka 'daura miki aure fa ya kamata ace kin bar wannan shirmen a baya".
Tace dani cike da 6acin rai tana nuna ni da yatsa.

Shagwa6e fuska nayi kamar zanyi kuka nace" Addah dan Allah ni toh me zan masa?"

Shiru tayi ta zuba min idanu tana kallo na, sau'kar da murya tayi sannan ta 'kara da fa'din" Ina fatan dai ke da kanki kin san halin mijin naki ba sai an fa'da miki ba?, me kike tunanin zai yi dake shi da yake hul'da da 'yan mata da suka take ki a komai? Wannan yarinyar Ma'u ka'dai ma in kina da tunani ta isheki babbar misali Hudah, ke kina tunanin a hakan da kike yi har miji zai iya dawo da hankalin sa gare ki?"

Idanu na hawaye kawai suka fara tuno asalin halayen Yah Deen da nayi cikin zuciya ta, ni ka'dai na san me nake ji a duk lokacin da na tuno irin abinda idanu na suka gane min yana aikatawa..a gani na Yah Deen ko me zan aikata a duniyan nan hankalin sa ba zai ta6a juyowa zuwa gare ni ba, saboda naga irin matan da yake mu'amala da su, ni da kaina nasan ko cikin mafarki ban isa in kamo 'kafan Husnah a komai ba, toh dan me yasa zan dami kaina bacin nasan abu ne mai wahalar gaske ganin faruwar hakan.

Cikin muryar kuka nace da ita" Addah toh ni nace ina son hankalin sa ya dawo gare ni ne....?"
Tun kan na rufe baki na ta tare ni da fa'din" Ki min shiru 'yar 'kauye kawai, wallahi ke dai wannan karatun naki sam ban san amfanin sa ba..jibe ki kamar zaki yi abin kirki idan angan ki nan kuwa ba haka ba, Hudah ke baki san cewa kin girma ba ko? sa'annin ki nawa aka yi musu auren suka je suka zauna lafiya a 'dakin mijin su ke kin tsaya wani banzan shirme dan kin samu da ma ko?"

" Nima ai ba fa'da muke yi ba Addah".
Na bata amsa ina share hawayen idanu na.
Idanu ta zaro sannan tace" Ikon Allah! anya Hudah kina da wayo kuwa? da alamu 'kauyen cin ki ba mai 'karewa bane har abada, tun wuri fa wallahi  ki natsu ki ja mijin ki a jiki tun kafin lokaci ya 'kure miki...yanzu ina wayar ki?"

" Tana nan".
Na bata amsa ina mai tura baki na jin tace da ni 'yar 'kauye.

Sani tayi na 'dauko wayar wanda bayan na kawo wayar ta kar6a ta ajiye gefen ta.

Maganganu tayi min cikin natsuwa inda ta ringa nuna min muhimmanci da darajar da miji ke da shi a gun matar sa...manufar aure da kuma asalin dalilin da yasa ake yin sa duk sai da ta sanar da ni cikin natsuwa.

Wasu maganganun nata ma ni kunya suka bani sosai amma ganin ita bata damu ba yasa kawai nayi 'kasa da kaina na cigaba da sauraran ta.

Ta 'dauki tsawon lokaci tana yi min bayani sannan daga 'karshe tace in kwantar da hankali na indai ina son in bita can Darazo to dole sai nayi abinda zata saniyi yanzu.
Tace ke kanki kin sani ko Ummah ma bazata ta6a barin ki ki tafi ba har sai ta tabbatar da yardar Deen kafin nan dan haka ki 'kira shi yanzu ki gaishe shi sannan ki ro'ke shi batun tafiyar.
     Tace duk da tasan 'kiran da zanyi masa a yanzun bazai 'dauke shi da muhimmanci ba saboda dan kaina nayi shi ba wai dan inji ya yake acan ba amma dai still yana da kyua in 'kira shin kuma zai iya jinsa daban ta 6angaren sa.

Duk wannan bayanan da tayin kaina 'kasa ban kalle ta ba har sai da ta kai aya kafin na 'dago kaina nace da ita" Addah ai ni bani da numbern sa a wayar?"
" Kamar ya kuma bki da numbern sa Hudah?..baku ta6a waya da shi bane dama?"
" Mun ta6a yi sau 'daya".
" To ki duba cikin wayar mana...." Tayi maganar tana mi'ka min wayar tawa.

Ansa nayi na shiga inda ya nasan zan samu numbern na tafi can 'kasa ina dubawa, ni da kaina nasan babu numbern da banyi saving ba sai ta shi ka'dai, hatta Zaidu nayi saving numbern shi duk wanda na ta6a yin waya da shi to bana ajiye wayar har sai nayi saving numbern, ta Yah Deen ce ka'dai ban bata wajen zama cikin waya ta ba.

Ban wani sha wahala wurin nemo numbern ba domin ita ka'dai ce babu suna, na riga na samu amma sai na kasa sanar da Addah Maryam cewa na samu, shiru nayi na zubawa wayar idanu kamar me neman wani abu ina tunanin ta yadda zan fara magana da shi idan na 'kira shi.

Bansan lokqcin da na cika iska cikin baki na na furzar ba tare da 'dan 'dage kaina sama ka'dan.

Ganin hakan yasa Addah Maryam jefa min tambayar" Wai har yanzu baki samu bane?"

Sai nace
" A a ban gani ba, ga dai wata number amma ban sani ba ko ta shin ce".
Nayi maganar ina mi'ka mata wayar tawa, bata kar6a ba sai tace da ni" Ni kuma me zan yi da ita kina mi'ko min, ki gwada 'kira mana kiji ko shi 'din ne".

Fa'dan hakan ke da wuya take sai naji zuciya ta ta fara harbawa da sauri-sauri...marairaicewa nayi nace" Addah ni inna 'kira toh me zance masa dan Allah...shi fa kullum masifa ce da shi?"
" Ikon Allah ke da a tunanin ki haka zaku cigaba da zama ne? Ke da mijin ki amma kike irin wannan maganar?"
Nace" Ni wallahi Addah tsoro nake ji".
Sai kiyi ai, idan kin gama tsoron sai ki 'kirasa ina nan ina jiran ki..."
Mita ta cigaba da yi ina da take fa'din" Ashe dama ma kinsan numbern ta shi shine dan kin raina min wayo kike wani ce min baki sani ba ko?"

Yi nayi.tamkar zanyi kuka ina 'kif-'kif da idanu ina kallon ta.

Cike da masifa tace" Sai fa kin 'kira, ke bari kiji ko ma ba dan batun tafiyar ba a yau 'din nan in kinga baki 'kira yaron nan ba to 'kaddara numfashi na ne ya tsaya cak wallahi, shashancin banza kawai, idan haka ake yi ai bazaki ga kowa na zaune lafiya a gidan sa ba, maza kira shi yanzu ki gaida shi ki tambaye shi ya karatu sannan kice dashi kina so za ki bi Addar ki Darazo muji me ze ce".

" Toh Addah in ya'ki amincewa zaki ro'ka min shi?"
" Allah ya kiyaye ai in ke baki da wayon ki tambayi mijin ki abu da kanki sai dai kawai kawai ki ha'kura zuwa wani lokacin idan wayo ya ratsaki".
Ta fa'di haka ne a fili amma cikin zuciyar ta cewa tayi wannan 'dan rainin hankalin yaron ina zanje ina wani kwantar masa da murya a banza salon.ya ha'da ni da ke in duk ya raina mu".
Ta 'karashe da ta6e bakin ta.

Hannu na har rawa yake yi lokacin da nake 'ko'karin yin dialling numbern shi,  sai na tsaya kallon wayar kamar wawuya.

Yanda nake jin wayar ke 'kara nuna alamun 'kiran ya shiga haka nima nake jin zuciya ta na harbawa...daf da zai yanke sannan ya 'daga amma sai naji yayi shiru...nima kuma sai.na rasa me zan ce da shi dan haka shirun nima nayi.

Satan kallon Addah Maryam nayi sam ban san me zance da shi ba a dai-dai wannan lokacin da ni da kaina fama nake da zuciya ta.

Da idanu Addah Maryam tayi min alamun inyi magana mana sai nace"  Hel...lo" Da rawar murya har nawi naji baki na yayi min...sai Shima yace" Hi" a hankali tamkar dole aka sanya shi yin maganar.
" Ina yi...ni" na sake fa'di ina yin 'kasa da idanu na.
Bai amsa ba sai yace " Yau kin tuna dani kenan".
Ina kan tunanin yanda akayi ya gane ni na bashi amsa da fa'din" A a" Inda nayi maganar ina mai satan kallon Addah ta.

Daga inda yake sai yayi saurin gyara kwanciyar sa sannan cike da mamakin amsar da na bashi yace" Indai ba tunawa dani kika yi ba toh me yasa kika 'kira ni...tell me".

..." _ki 'kira shi ki gaida shi ki tamabaye shi ya karatu sannan...._ maganar Addah Maryam na tuna dan haka sai nayi saurin bashi amsa da fa'din" Yah Makaranta?"

Ajiyan zuciya naji ya sau'ke sannan yana shafo kansa daga 'daya 6angaren ya bani amsa da fa'din" Alhamdulillah...karatu ya 'kare ai saura ka'dan mu kammala insha Allahu..".

" Allah ya bada sa'a".
Na fa'di ina kamo wayar da duka hannuwa na biyu kamar wani kayan nauyi ne na ri'ke.
Chapter 136 · 0% Book details