← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 211

Sashe 182

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Kwalla Sani ya fara kamar ba namiji ba, take ya Deen ya zaro idanu yana duban sa yace" haba Sani...ba fa yau ne akayi mutuwar ba common share hawayen ka addu'ah kawai zamu yi mata ba kuka ba..."
Shima 'din 'karfin halin maganar yake domin har yanzun bai gama samun sau'ki ba...kuma baya jin zai iya cire Baby a ransa kwanan kusa, ko yanzun ma kafin shigowar Sani pics din Baby yake dubawa yana tuno duk moments din da suka yi tare.
Shine kawai ya matsa akan gida zai dawo shi yasa aka sallame shi baya ga har yanzun kirjin sa bai bar yi masa ciwo ba.

Girgiza kai Sani yake yi a hankali cikin kuka yake fa'din" Yalla6ai wallahi na rasa ta ina zan fara neman afuwar ku, dan Allah ku yafe min..ku yafe min abubuwan da suka faru, ban ta6a dana sanin abinda nake aikatawa ba sai yanzun...ha'ki'ka na ci amanar ku na yaudari zuciyar ku na zalunci yarinyar da bata ji ba bata gani ba..ban san da wane idanu zan dube ku ba, kunya nake ji sosai, gani nake kamar Allah bazai ta6a yafe min ba...amma nasan idan kun yafe min wata'kila in samu sassauci...ka ro'ka min Hajiya ta yafe min dan Allah nasan tafi kowa shiga tashin hankali.."
Cike da karfin hali Deen yace
" Kar ka damu Sani, 'kaddara ce ai kuma dama azane yake, hakan ya zama ne tamkar Iznah agare mu gaba 'daya, ba mamaki ya kasance silan shiryuwan wasu daga cikin mu...ban ri'ke ka cikin zuciya ba saboda nasan baka da laifi Allah ne ya tsara saboda wasu dalilai da shi ka'dai ya sansu..fata na kawai ya kasance kayi nadama ne ta gaskiya kuma kayi min al'kawarin daga Jasmine bazaka sake 6ata 'yar wani ba...".
" Insha Allahu ranka shi da'de..wallahi zan yi fatan mutuwa ta 'dauke ni fiye da sake ganin faruwar irin hakan a rayuwa ta, tsakani na da Allah nayi nadama.."
" Very gud...zan so hakan ya kasance ko ba komai zaka taimaki ahalin ka ne, ba mamaki kana da 'kanne ko yayye mata, sannan dole wataran zakayi aure indai har ana raye, kuma zaka haihu...ka tsarkake tuban ka ta yanda zaka iya fansar ahalin ga fa'dawa cikin irin wannan halin".
" Nagode sosai Allah ya 'kara girma Insha Allahu zan kiyaye..nagode daka yi saurin fahimta ta..Allah ya 'kara 'daukaka yalla6ai Allah ya baku madadin JASMINE, Allah ya yiwa rayuwa albarka ya ji'kan mahaifa...nagode sosai.."
" Kar ka damu Sani..sai dai wani hanzari...inaso wannan abin da ya farun ya kasance sirri tsakanin mu, yanda ya faru anan bana so maganar taje ko'ina..Sani kayi min lakawarin bazaka fa'diwa kowa ba...."
Ba haka yaso ba amma he had no choice than ya amsawa Yah Deen ko dan halaccin da yai masa ma..." Insha Allahu zan kiyaye yalla6ai kar kaji komai".
Kai yah Deen ya jinjina cike da gamsuwa.

Sani kam ba haka ya so ba, da niyyar sa idan yaje zai fadawa mahaifiyar sa komai ne amma tunda haka ya za6a shikenan..." zaka iya tafiya".
Abinda ya tsinkayi muryar Deen ya fa'da kenan.
Sai yace
" To yalla6ai godiya nake...amma dama ina so ne yau in wuce gida saboda babu amfanin sake zamana anan..".
" Saboda me yasa kuma zaka tafi?".
" Hakan dai naga yafi min shiyasa na yanke shawara...".
Tun kan ya rufe baki Yah Deen yace da shi" Aikin naka kuma fa...".
" Yalla6ai bar batun aikin nan, da me zan yi aikin ni da ke da hannu guda, ko dama ace hannun nawa na nan yalla6ai ba zan iya aikin ba yanzu..gara kawai in koma gida...zai fi".

Tausayin sa sosai Yah Deen yaji shi aganin sa ai shine yayi masa silar da har aka yanke mai hannun sa, duk da Sani yayi masa ba daidai ba amma sosai yake tausaya masa cikin zuciyar sa.

A hankali ya sau'ke idanun sa kan Sani sannan yace" Ka bari amma ba yau ba ko zuwa gobe ka wuce, yanzun rana tayi idan ka 'dan huta kaga sai ka yi tafiyar bazan hana ka ba ".

Sani ba haka yaso ba amma baya son yin doguwar musu da Ogan nasa, domin ya fahimci dauriyar maganar kawai yake yi ba jin da'din ta yake yi ba.

Tashi yayi ya fita yana zuba godiya, domin da kansa yasan Deen yayi masa halacci, halaccin da bakowa ne zai iya ba, yasan komai da akayi masa a hospital Deen ne ya 'dau nawi, sannan kuma duk da yasan abinda ya faru amma ya 6oye bai ha'da shi da hukuma ba dan a hukunta shi sai ma ya bishi da nasiha, fatan Alkhairi kawai yake yi masa cikin zuciyar sa...yayin da Yah Deen ya lumshe idanun sa yana tunanin irin sallamar da ya kamata yayi da Sani.

Safwan da yazo duba shi adaren yake gaya mai yanda suka yi da Sani..cike da jimami Safwan ya furta Allah sarki...rayuwa kenan, naje ai Dr.Felix ke gaya min ai already anyi discarging nashi ashe nan ya dawo".

Sai da Sani ya kwana biyu kafin Yah Deen ya sallame shi da 50k yace yaje yayi jari da shi.
Da farko Sani 'kin kar6a yayi amma Yah Deen ya tsare shi dole ya ansa yana godiya ya fita bayan yayi masa sallama ya tafi.

Tun jiya abakin mai gadi yake jin labarin ai Hajiyar gidan sun tafi da su Ammi tun bayan rasuwar Jas, sosai ya tausaya mata wanda ya ku'durta cikin ransa cewar komai da'dewa sai ya dawo ya nemi yafiyar ta itama.

Bai ko 'kara awa guda cikin gidan ba ya shirya ya tafi bayan yayi sallama da kowa haka suka rabu da Bala mai gadi kowa na jin babu da'di, rayuwa kenan ta ha'da ta kuma raba aduk lokacin da ta ga dama.

*****
     Tunda Yah Deen ya dawo gida yake damun Safwan da batun tafiya Shuwarin amma yana kakkaucewa domin shi yafi son sai ya 'kara warwewa while shi kam yana ganin kamar 6ata masa lokaci yake yi.

Batun aikin sa kam ba'a magana..Safwan ne ya tura report can Abujan ta email bisa ga abinda yake faruwa da neman iznin hutu mai 'dan tsayi an kuwa amince masa..dan haka basu takura shi ba.

Ransa ne ya fara 6aci da yanda Safwa ke jan ransa dan haka yace masa Zuwa tursday shi kam ya shirya tafiya kuma bazai fasa ba.

Jin hakan yasa Safwan amincewa cuz yaga ya damu sosai, a lissafin sa kenan nan da kwana biyu zasu yi tafiyar.

Adaren ranar ya kasa ha'kuri, sosai yaji zuciyar sa na son jin muryar ta, tun tafiyar ta basu sake ganawa ba..babu ma wanda ya 'kira shi hatta Anty Zainab tayi fushi da shi.

Banda 'yan biyun Ammi babu wanda ya damu da shi yanzu.
Relaxing yayi yana kan dialling numbern ta, cikin sa'a kuwa ya shiga, lokacin kwance take tana game in Candy Crush 'kiran ya shigo mata bazata kawai ta ja recieve wanda shigowan 'kiran kenan sai ya zama kamar jira take yi tayi recieve.

Sai ma da ta 'dauka sannan ta fahimci abinda ta aikata ganin sunan shi rubuce kan fuskar wayar tata ga kuma sekanni da ke faman irguwa.

Cike da haushi ta runtse idanun ta lokacin da ta tsinkayi muryar sa yana fa'din sunan ta.

Taso tayi hangin call in amma bata so ya san cewa da gangan tayi dan haka sai ta ajiye wayar ta juyar da kanta 'daya gefen tayi shiru.

Hawaye ne suka fara taruwa mata jin yanda yake maganar ko daga muryar sa zaka fahimci halin da yake ciki.

"...mutuwa na kusan yi da kika tafi kika barni Nuree yaushe zaki dawo min?...baki ko yi tunanin halin da zan shiga ba kika tsallake kika bar ni bacin kinsan kece rayuwa ta?...".
Cikin zuciyar tace" 'karya kake yi ni ba rayuwar ka ba ce Yah Deen..".
Ta 'karasa fa'da hawayen ta na 'kara kwaranyowa.
Wayar ba'a speaker take ba amma tana iya jiyo abinda yake fa'da.
"...ni dai ki yafe min, ki dawo mu yi rayuwar mu dan Allah, Nayi miki al'kawarin canzawa, wannan karon dagaske nake yi bazan sake kwatanta ha'da wata macen da ke ba, ban ta6a tsammanin soyayyar da nake yi miki ta kai hakan ba sai da na wayi gari naga bakya gida na..please Nuree talk to me ko pim kice da ni insan cewa u ar with me...".
Da sauri ta rarumi wayar ta kashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya.

Kuka sosai take yi harda sheshsheka, taimako 'daya Allah yayi mata Ammi bata kusa da tasan dole ne sai ta tuhume ta.

Da kanta ta lallashi kanta tayi shiru, har yau har gobe tana son mijin ta sosai amma bata jin zata iya sake rayuwar aure da shi, burin ta kawai ya bata sakin ta ta samu damar da zata yi rayuwar ta ba 'kar'kashin inuwar auren sa ba...abu 'daya da ke damun ta kuma yake sata tausayin sa shine fushin da iyayen sa ke yi da shi, duk bata jin dadin hakan kwata-kwata, zaton ta ma ko zai biyo bayan su da wuri bayan tahowar sun, bawai dan dan ita ba tunanin zai biyo bayan iyayen sa ne amma ga mamakin ta sai taga shiru.

Koka'dan batajin tana son zuwan nasa dan jin da'din kanta face dan burin ta na ganin daidaito tsakanin sa da su Alhaji Baba.
Domin ita nata ta riga ta gama lissafi bama ta damuwa da kanta ji take koda bai rubuta mata saki ba a hakan zata cigaba da rayuwar ta amma bazata ta6a komawa gidan sa ba.
Indai igiyar auren ne zata iya tsare su batare da ta keta iyaka ba.

Sai da ta idar da sallahr Isha'i sannan ta sake 'dauko wayar ta ta kunna, tasan in ba wani dalili ba abu ne mai wahala ya sake 'kiran ta cuz tasan halin sa sarai...dan haka ranta sake ta kunna wayar, wurin text ta shiga ta rubuta masa message ta tura masa sannan ta sake ajiye wayar ta.
Chapter 182 · 0% Book details