← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 211

Sashe 115

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai samu damar zuwa ganin Husnah ba har sai washegari...kuma Alhamdulillah 95% ya samu ha'din kanta kan auren dan bata nuna masa tsana ko nuna bata 'kaunar zaman aure da shi ba.
Batun tarewar ta kuma yace shi da kansa zai shirya komai kafin ya koma.

Wurin mahaifiyar sa yaje  suka sake magana akai inda ya nuna mata cewar ba abin damuwa bane tunda ma tana makaranta, so zata cigaba da karatun ta a Jigawa har sai ta kammala kafin.

Ai kuwa muhalli kawai aka canza mata daga campus zuwa wani madaidaicin gida zubin zamani, wanda Hisham ya cire ma'ku'dan ku'dade aka biya haya da shi.

Gidan ta aka tsara mata tamkar acan zata 'kare rayuwar ta dan sosai gidan yaci ku'di abin ba'a cewa komai, yayin da shi Hisham 'din zai cigaba da zaman sa a Abuja bakin aikin sa, sai dai ziyara kawai zai ringa kawo mata aduk lokacin da ya samu dama.

~Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya mai 'dorewa.~

*****
          Cikin shirin makaranta ta na fito da yake nayi latti so sai nake ta hanzari inga na fita dan kar in makara sosai, Ammi da Anty Zee na zaune a parlour na fito ina sanya Hijab akaina ko duban su da kyau ma banyi ba na nufi 'kofa ina fa'din" Ammi na tafi yau na makara sosai".
" Adawo lafiya".
Ammi tace da ni gami da mi'kewa tayi ciki kamar dama jiran fitowa ta take yi...ko juyawa banyi ba na cigaba da tafiya ta ina gyara zaman jakata da tunanin saurin da zanyi kafin in isa, daf da zan bar parlourn naji muryar Anty Zainab na fa'din" Hudah baki ko gaida Yayan ki ba zaki tafi?"
Saurin waigowa nayi jin ta ambaci Yaya na..nan naci karo da Yah Deen zaune daga gefen ta ya wani kishingi'da yana danna wayar sa.

Sam ban lura da shi ba lokacin da na fito sai yanzun na ganshi.

'Dauke idanu na nayi daga kallon sa na mayar kan Anty sai naga ta min murmushi tana min nuni da in gaida shi...cikin sanyin murya na furta" Ina kwana Yaya"...kamar ba zai amsa ba can 'kasa-'kasa cike da izza ya amsa da" Lafiya" ata'kaice.

Sai da na juya na kalli Anty Zainab dan ganin yanayin ta da son tabbatar mata da cewa na gaida shin sannan na
juya na sa kai nayi gaba da tunanin halin sa cikin raina.

" Wai me yasa kake haka ne Mu'een...?" Anty ta tambaye shi tana kallon fuskar sa bayan fitata.

" Me nayi Anty?"
Shima ya mayar mata da tambaya madadin amsar maganar ta yana mai 'daga idanu ya kalle ta.
" Aww kana nufin kai baka san me ka aikata yanzun ba? Yadda kake wa yarinyar nan ai kai da kanka kasan bai dace ba...kai baka tunanin gaba ko Mu'een?...kar fa...".

Bata 'karasa fa'dar abinda tayi niyya ba ya tare ta da fa'din"...Insha Allahu babu abinda zai faru Anty...dan nasan abinda zaki fa'di bai wuci wanda kika saba fa'da ba".

" Hmm..amma dai ya kamata ka daina haka nan tunda babu wanda ya san me gaba zata haifar..'kila sai ka gama mata fi'ili yanzu wataran kuma mugan ka kana ro'konta.. kasan ita rayuwa babu abinda bata tafiya da shi..."

Gira ya ha'de tare da gyara zaman sa da kyau yana duban Anty yace" A wani dalili zan yi hakan kenan Anty?"

" Dalilin aure mana".
Ta bashi amsa tana murmushi...take ya sake ha'de ransa tare da kauda kai gefe yana fa'din" Allah ya sawwa'ka wallahi..wannan 6eran kike fatan aure tsakanina da ita Anty ni me zan yi da ita?"
" Ko ma menene dai kai kasani..ko da ita kiyashi ce kuwa idan Allah ya tsara kaine mijin ta baka isa kayi jayayya ba..."

Da serious tune cike da 6acin rai yace
" Please Anty ki daina min wannan fatan dan Allah..ban so".

Bata 'kara cewa komai ba kuwa illah bayyananniyar murmushi dake haskawa saman fuskar ta...tana tunanin ranar da Mu'een zai ji da kunnen sa cewa Hudah matar sa ce ta sunnah da aka 'daura musu aure batare da sanin sa ba... ayanda ta sanshi take kuma ganin take-taken sa tasan ranar kuka ne kawai ba zai yi ba saboda ba'kin ciki...ni kuwa nace ( ~time ll tell~ ).

Tunda suka yi wannan maganar bai sake doguwar hira da Antyn ba, bai ma jima a gidan ba ba ya tashi yayi musu sallama ya koma gidan can sa ransa a matu'kar 6ace.

Daga ranar kuwa naga ya sake canza min, ni ban san abinda ya faru ba sai gani nayi idan mun ha'du ko kallon arzi'ki bai min, duk da ma ko da can baya ma haka ne amma dai ba kamar yanzu ba, ada, haka ma gaisuwa ta sai ya ga dama yake amsawa, ni kam ban wani damu da hakan ba da yake nasan wannan ka'danne daga cikin halin sa da ni na sanshi da shi.

Sati guda bayan bikin Yah Deen sai ya tattara ya koma Jigawa ranar wata Sunday...Anty ma washegarin tafiyar sa ta koma Azare wurin dangin ta...gida ya dawo shiru babu kowa sai mu ka'dai.

Duk wani abu da ya faru a bikin bai sa na kawo faruwar wani lamari cikin zuciya ta ba, da yake ma har a lokacin ban gama mallakar hankali na ba shiyasa sam ban ta6a wani dogon tunani kan maganganu ko abubuwan da naga suke faruwa a gidan ba.

Sai daga baya ne ma bayan kowa ya watse nake tambayar Ammi ashe wai an fasa auren Yah Deen 'din.

Ammi sai tace da ni a ina naji..ban 6oye mata ba nace Ma'u ce ta gaya min nima.

Ammi sai tace 'karya ne ba'a fasa ba, an 'daura auren tun a ranar babu wani fasawa da akayi.
A 'kagauce na sake tambayar ta ta da fa'din
" Ammi to ya banga amaryar ba har yanzu?"
Sai tace" Tana gidan su tukunna ba yanzu za'a kawo ta ba".

Jin haka yasa na yadda cewa amaryar Yah Deen 'din tana gidan su har kuwa na fa'dawa Ma'u yanda muka yi da Ammin kaf da muka ha'du da ita...jim naga tayi bata ce dani komai ba, ashe abin ya dame ta sosai sai dai ta ri'ke cikin ranta kawai...tunani take yi akan 'karyar da suka shirga mata shi da abokin sa Imrana akan wai ya fasa auren kuma  gun mahaifinta zasu zo neman auren ta ashe 'karya ce ba'a fasa auren nasa ba...shiyasa ma ya yi tafiyar sa bai ko sake bi ta kanta ba ashe..bayan uwr azabar da ya bata suka kuma hanata sanar da kowa.

Bayan wasu kwanaki...
Yanda abin yake cinta arai har yasa ta fara 'dan ramewa sai dai babu wanda yasan takamamman me ke damun ta, ko makaranta ma yanzu ba zuwa take yi sosai ba sai lokaci zuwa lokaci.

Yah Deen ya riga Husnah komawa makaranta so hankalin sa kwance ya cigaba da karatun sa.

Ya kusan yin a'kallah kwanaki tara da komawa amma bai ta6a ganin ko gilmawr Husnah ba..shi kam ma ko tunawa da ita bai yi ba, sai dai acikin 'yan kwanakin ranar wata laraba labari ya iso masa cewa anga Husnah cikin makaranta.

Basarwa yayi bai nuna wata alamar damuwa ba,  dan harga Allah shi yanzu ba ta gaban sa..sai da ma aka same shi da maganar ta kafin ya tuno da ita.

Sai dai me ?
komawar sa gida sai tunanin Husnah ya bi ya cika shi, a lokacin ya fara missing presence nata, 'kewar ta ya'ki barin sa ya sarara har ya kasa ribatar zuciyar sa shai'dan yayi galaba a kansa ya mantar da shi cewa tana da auren wani daban  akanta wanda bashi ba.

Kamar wasa ya 'daga wayar sa...batare da wani tunani ba kawai ya danna mata 'kira da wani layin sa da ya tabbatar bata shi.

Daf da 'kiran zai yanke sannan ta 'daga tare da fa'din " Hello".
Cikin sanyi..cuz duk yanzu Husnah tayi sanyi kamar ba ita ba.

Yah Deen kuwa shiru yayi bai ce komai ba illah murmushin mugunta da yake saki daga 'dayan 6angaren.." Hello"!!
Ta sake fa'di akaro na biyu tana yatsina fuska amma still shiru bai amsa ba.

'Dan 'karamin tsaki taja da niyyar yanke 'kiran dan ganin kamar ba'a da alamun furta komai  wanda jin zata yanke wayar yasa Yah Deen saurin ambatan sunan ta cikin muryar da ya san zai sanyatar mata da zuciya.

Ai kuwa cak ta fasa abinda tayi niyyar yi zuciyar ta take ya fara dokawa abinku da zafin 'kauna...sai dai bata iya ta ce da shi ko 'kala ba.

Cikin wata mayaudariyar muryar ya sake fa'din" Husnah ashe kin dawo shine kika 'ki neme ni ko?..Husnah har haka na zama a wurin ki ban sani ba?"

" Meyasa sai ka sani to?"
Tayi 'karfin halin furta hakan.
Sai yace" Haba Husna..."
Saurin tarar sa tayi da fa'din" Malam matsayin matar aure nake yanzu...."

" Na sani Husnah bacsai kin tuna min ba.."

" So ka fita hanya ta please ka daina damuna.."

" Husnah ni ne fa? ko kin manta badan wani 'dan dalili ba da nine mijin naki a yanzu.."

Cike da takaici ta cire wayar a kunnan ta tana jan tsaki.

Yah Deen kam da murmushi yabi wayar sa dake ri'ke a hannun sa jin yanda ta yanke masa 'kirara a zafafe...shi kansa yasan ya cancanci fiye da haka daga gareta saboda sam bai mata adalci ba a rayuwar ta.

Sam maganar auren dake kantan bai dame shi ba dan yasan shi ka'dai take so, shiyasa ma shai'dan ke 'kara ingiza shi akanta yana sake tunzura zuciyar sa akan sake mallakar jikinta cikin ko wani irin hali.

Text ya rubuta ya tura mata
_"..Ina fatan baki manta abinda yafaru a Azare ba.."_

Yayi zaman kusan mintina ashirin da uku yana jiran reply amma har a lokacin shiru baiga komai ba.

Yanzu kam yasan Husnah gagarumin fushi tayi da shi tunda har ta iya masa wannan wulan'kncin.

Cikin ransa ya ayyana zai share ta tukunna na kwana biyu yagani..sai dai me?
Kafin cikar mintina talatin sai ga text 'din Husnah ya ratso cikin wayar sa, wanda da ganin hakan ya saki murmushi a fili ya furta" ai nasan hali..yarinya indai zaki kulani ko yayane ai shikenan..".
Chapter 115 · 0% Book details