Sashe 181
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya riga ya gama komai da Sani zai bu'kata ya ajiye me kula da shi, da wanda zai na jigilar abincin sa da duk abinda zai bu'kata har zuwa ranar da za'a sallame shi wanda ba kowa ne ya 'dau nawin hakan ba face Mu'een.
Da dukiyar sa ya 'dau nawin komai game da Sani, wanda Safwan ya jagoranci abin ta hanyar nemo wa'danda zasu yi musu aikin.
****
Wasa-wasa sai da Yah Deen ya 'dauki sati guda a asbiti kafin ya 'dan fara warware wa...
Comment
Vote
Share
*Salmerh* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *82*
Rama sosai yayi kamar ba shi ba duk idanuwan sa sun firfito, wanda cikin lokacin kuwa duk Safwan ne ke kansa, shi ke kula da komai na shi, har Alhaji Baba Safwan ya 'kira ya fa'diwa batun rashin lafiyar tasa ganin kamar abin na neman yayi tsanani ga mamakin sa kuwa sai ji yayi Alhaji Baba yace" To ni mai zan masa Safwan...Allah ya bashi lafiya".
Daga haka ya hanging call 'din ya jefa wayar sa cikin aljihu, Safwan sosai yayi mamakin sa anan kuwa ya 'kara tabbatar da irin fushin da iyayen sa suka yi da shi, bai bari Yah Deen ya san hakan ba soboda gudun sake 'daga mai hankali kawai ya bari cikin ransa.
'Bangaren Sani ma _Alhamdulillahi_ jiki yayi sau'ki babu abinda ke damun sa yanzu illah gurbin ciwon hannun sa inda aka cire.
Shima 'din baya damun sa sosai, yana iya yiwa kansa wasu abubuwan yanzu saboda baya jin wani ciwo, jira kawai yake a sallame shi yasan inda dare yai masa.
Yah Deen duk da yana cikin wani hali amma a kullum damuwar sa iyayen sa ne da kuma matar sa, burin sa bai wuce yaje inda suke ba, da yaga ya 'dan fara samun sau'ki sai ya fara batun tafiyar amma Safwan ya ce da shi ba yanzu ba tukunna sai ya warware gaba 'daya.
*****
'Bangaren Noor kuwa tunda ta koma gida sai tunani suka yi mata yawa, domin babu inda take zuwa daga aikin gida shikenan sai zama dole badan tana so ba tunanin suka cika mata kwanya.
A kullum bata iya bacci da wuri saboda tunanin rayuwar ta, idan ta tuna Baby kuwa sai dai kawai tayi ta hawaye, tana jin babu da'di a zuciyar ta, dagaske ne ashe Allah dama yake bawa bayin sa, idan ka'ki yin amfani da damar ka ta wuce ka shikenan, kamar ita... Allah ya bata amanar Baby matsayin 'ya dan ta kula da ita amma tayi watsi da amanar Allah, ta 'ki bawa Baby kulawan da ta dace gashi ya kar6e abinsa batare da ya sake bata wata damar ba...kuka take yi sosai tana ro'kon Allah akan ya yafe mata, kar yaga laifin ta akan hakan, tace Allah kasan halin da nake ciki, damuwa ce nima tai min yawa Yah Allah kar ka tuhume ni akan hakan Yah Allah ka sani ina damuwa ne akan abinda bani da damar canza shi shiyasa hankali na ya kasa natsuwa.
A kullum bata da aiki sai kuka amma bata ta6a bari Ammi ta fahimta ba, maganar kirki yanzu bata yi tafi so ta yi zamanta ita ka'dai yafi mata komai.
Sai da ta kusan kwana biyar da dawowa kafin ta sake kunna wayar ta, wanda shine ya 'dan fara 'debe mata kewa, ta kan yi game ta kuma chat da wasu friend nata na makaranta.
Idan sun tambaye ta batun makaranta kiwa takan ce da su ta bari ne kawai tana so zata canza wata.
Su kan yi mamaki sosai wasu har na mata nasiha akan cewa ai dan 'yar ta ta rasa ranta ba ya nufin komai nata na rayuwa ya tsaya ne...da yake suna da labarin rasuwar Baby har ma sun zo mata ta'aziya a lokacin...sai suke ganin kamar dan hakan ne.
Amsa take bayar wa da fa'din" Nasani, kawai na bar makarantar ne dan munbar garin Bauchi mun koma gida so nafi so in nutsar da hankali na wuri guda..amma ba wai dan Jasmine ta rasu bane.".
Ita kam cikin zuciyar ta take jin komai ma dake cikin garin Bauchi ya fice mata aka, bata 'kaunar abinda zai sake sata shiga garin balle har zama ya kamata talk more of attending lectures.
Duk take jin ta yafe...tunda har ta iya ha'kura da Yah Deen a rayuwar ta menene ma ba zata iya ha'kura da shi ba?.
Alhaji Baba ne ma yayi mata batun makarantar inda ya tambaye ta ko zata koma cikin school ta cigaba da makaranatar, take ta nuna masa a a bata so inda rabon ta wataran zata yi..
Da yake yasan dalilin ta sai ya jinjina kansa da burin canza mata wata, ko BUK ma tunda Saif ma acan yake duk dama shekarar 'karshe yake amma zata fi jin da'din zama a can.
*****
Satin Mu'een biyu a asbiti sannan aka yi discharging na sa washegari kuma aka sallami Sani dan shima ya warware sosai...shi kam sai share hawaye kawai yake yi yana tunanin ta inda zai fara.
Da 'kafar sa yake ta takawa domin bai yadda ya 'dauki komai da yake nasa bane a asbitin duk yace mai kula da shi 'din ya tattare ya bar masa, duk irin kayayyakin da Safwan ke sayo masa duk ya bar wa wanda yayi ta kula da shi in.
Ko sisi babu ajikin sa shiyasa yake takawa abin sa da 'kafa, Safwan yasan da batun Sallamar amma yayi zaton sai zuwa yamma za'a sallame shi irin na Mu'een sai kuma akayi rashin sa'a suka yi sa6ani.
Da 'kafar sa yake takawa a hankali har ya iso gidan Ogan sa Deen.
Wanda tunda ya dumfari gate in gidan zuciyar sa ke luguden bugu yana jin babu da'di amma bashi da wata mafita da ta wuce hakan burin sa bai wuce yayi arba da mahaifan Baby ya nemi gafarar su ba.
Daga hakan kuwa Insha Allah garin zai bari gaba 'daya ya koma mahaifar sa tunda fitan nasa bai masa amfani ba.
Hatta Bala mai gadi ma kunyar hada ido yake yi da shi domin shine ya san komai cikin halayyar sa...ai kuwa yana zuwa ya tura gate in yasa 'kafar sa ya shigo cak ya tsaya yana duban mai gadi dake zaune gefen gate in wanda shima turo 'kofan da akayin ya sanya shi 'dagowa.
Tsaye ya mi'ke da mamaki yake duban Sani ganin hannun sa 'daya, tausayin sa ne ya kama shi sosai cuz yana da labarin komai amma sam yau in ganin da yaiwa Sani sai yasa zuciyar sa karyewa.
Gaban shi ya fara takowa Sani sai ya kauda kansa gefe yana share hawaye.
Bala maigadi na zuwa sai ya rungume shi shima in kukan yake yi.
Dauriya Sani yayi yana murmushi yace" Sannu Bala, ya aikin?
Bala bai tanka ba illa sake kallon fuskar sa da yake yi.
Murmushi Sani yayi fuskar sa da hawaye yace" Kaga abinda Allah ya maida ni ko Bala?"
"..Na gani sani, ba komi bane kar ka damu wannan 'kaddarar Ubangijin mu ce.."
" Hakane..ya ha'kurin mu kuma..Jasmine Allah yayi mata rasuwa?".
Girgiza kai Bala mai gadi yayi yana jin mutuwar Baby har ransa...a fili furta" Ai yarinyar nan ta tafi da zu'katan mutane da dama, wallahi har yau ban daina alhinin rashin ta ba, mahaifin ta kansa ya kasa cire ta aransa, inajin kusan satin sa biyu kwance a asbiti sai jiya ya dawo..."
" Allah sarki...Allah ya ji'kan Jasmine".
Cewar Sani da fuskar ke cike da nadama marar misaltuwa, shi ka'dai yasan yanda yake jin abin a zuciyar sa.
Sai da ya ja numfashi sannan yana duban gefe yace" Ina so mu gana da yalla6ai domin yau nake so in wuce Plateau.."
" Ai kuwa yana ciki ka shiga ka same shi".
Bala ya bashi amsa yana mai matsawa daga gaban sa.
A hankali Sani ya fara takawa kansa 'kasa yake tunanin ko kashe ni zasuyi ma ya zame min dole in nemi gafarar ku Oga Deeni babu yanda zanyi saboda ni na jawa kaina da wannan tunanin ya nufi cikin gida.
Sallama yayi a parlour yana jin zuciyar sa kamar zata faso waje...Yah Deen kansa da yaji muryar Sani sai da Zuciyar sa ta tsinke, sosai aka hane shi da yawan firgici amma babu yanda zai yi ya zame masa dole ne.
Ciki-ciki ya bu'di baki ya amsa sallamar tasa, wanda ya matu'kar bawa Sani mamaki domin a yanda yaga Oga Deen yai masa ranar bai zaci zai samu amsar sallamar sa daga gare su ba,..." To ko dai bai gane Murya ta bane?"
Sani ya tambayi kansa while yana nan tsaye sam ya kasa 'daga 'kafafun sa balle ya shiga.
" Sani shigo ma na".
shine abinda kunnuwan sa suka jiyo masa daga ciki wanda ya sashi 'karya ta tunanin sa na cewa bai gane shi ba.
A hankali ya shigo yana yin 'kasa da idanun sa saboda kunya...gaban sa ya 'karaso nesa ka'dan da shi ya dur'kusa sau 'daya tak ya kalle shi daga haka yayi kasa da idanun sa duk da hakan sai da ya fahimci muguwar ramar da yayi.
Gaishe shi yayi ha'di da tambayar sa jikin sa..Yah Deen yana murmushi yace" Jiki Alhamdulillah ai sai dai in tambaye ka...yaushe aka sallame ka?"
Sani yace" Yanzun nan bai da'de ba.."
" Toh masha Allah, Ubangiji Allah ya 'kara sau'ki".
" Ameen Yah Allah".
Cewar Sani wanda daga hakan kuma sai ya rasa mai zai 'kara fa'di.
Yah Deen tashi yayi ya zauna da kyau shima 'din bai sake fa'din komai ba.
Bakin Sani har na rawa ya furta" Yalla6ai... ya ha...'kuri kuma..?"
Inda Yah Deen ya amsa da fa'din" Ha'kuri Alhamdulillah...Jasmine kam an tafi..sai fatan Allah ya ji'kanta yai mata Rahama...".