Sashe 143
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da ya sanya 'karamar riga ne naga inda na yakushe shi ashe wurin har ciwo yayi kau da kaina nayi sai kuma naji ba da'di har cikin raina.
'Kilan hakan ne yasa idan zai fita sai ya canza riga zuwa mai dogon mai hannu dan ya rufe wurin.
Yah Deen kam da ya fahimci.bana sakewa da shi sai ya ke barin idan nake dan kar ya takura ni, suna dai yana gida ne amma ba inda nake ba, ya kan shigo dai akai kai duba ni dan ko abincin ma da kansa ya zo ya 'diba min duk da ina cikin ciwo amma bai hana ni mamakin sa ba, ni dai sai naga bai canza min daga Yah Deen dana sani tun farko ba, fuskar sa dai wasai ba yabo ba fallasa amma bazaki ta6a iya fassara yanayin sa ba, tunani na kuma bai bani cewar a yau 'din ina matu'kar bu'katan kulawar sa ba, dan ni ko shigowa da yake yi ma takurani yake yi, saboda har a lokacin tsananin kunyar sa da haushin sa ne suka yi min ca.
Hankali na ya 'kara tashi ne da lokacin bacci na yayi, fargaba yabi ya cika min zuciya, duk yanda naso in kawar da tunanin abinda ya faru tsakani na da shi jiya kasawa nayi saboda yanda tsoro ya mamaye ni.
Haka na kwanta luf amma motsin kirki idan naji sai zuciya ta ta harba take sai in shiga firgici.
Lokacin da naji ya janyo jikin sa kuwa kusan sumewa nayi jiki na ya fara kakkarwa sosai..yi nayi tamkar ina bacci da tunanin 'kila hakan zai sa ya 'kyale ni duk dama nasan jiya ina cikin baccin amma ya tada ni bai kuma sassauta min ba.
Cikin sa'a ma sai bai yi min komai ba ashe shi da kansa ya fahimci halin da nake ciki na tsorata da nayi da shi, da kansa ma kuma bai yi niyyan yi min komai ba, ina rungume cikin jikin sa naji yana sau'ke numfashi da alamu bacci ne yayi gaba da shi.
A fili na sau'ke ajiyan zuciya sannan na bu'de idanu na, hannun san da ya rungumo ni da shi nabi da kallo a hankali na 'daga nawa hannun na 'dora kan nasa kamar ance dani inyi hakan.
Ban san lokacin da bacci ya tafi da ni ba, yayin da nayi bacci na cikin kwanciyar hankali.
Kwanan mu biyu da shi amma bai sake yi min komai ba, haka kuma har a lokacin shike siyo mana abinci rana da da na dare, haka kuma ako da wani lokaci ya kan tabbatar da cewa nayi amfani da ruwan 'dumi, nima kuma da yake na fahimci idan nayi amfani da shi 'din ina jin da'di shikenan da kaina ma ko bai tuna min ba na kanyi anfani na da shi.
Sosai na fara sakan jiki na ganin irin waccan abin bai sake faruwa ba, gashi ba laifi yanzu na 'dan samu samu lafiya da yake da kansa ya duba ni, bana so amma bazan iya yi masa gardama ba dole inaji ina gani ya gane min jiki na da sunan wai duba lafiya ta...ranar haka na yini ina tura baki na, ga shi kunya sosai ya kama ni fiye da na ranan can...ko lokacin da ya gama duba nin ma kifa kaina na yi na kasa 'dagowa in kalle shi..ga haushi ga kunya haka suka taru suka hanani sakat...shi kam sai naga ko ajikin sa bai damu ba...cikin zuciya ta na raya ai dama Yah Deen ba shi da kunya sam.
Ranar kwana na uku da jinyan nawa ne na sake raina kaina, domin Yah Deen mantar da zuciyar sa yayi wace ni, ya manta da batun tsorona ya kuma kawar da kai ga 'kan'kantar shekaru na, tun kafin yayi nisa na raina kaina, domin ji nayi ko na farkon ma ba komai bane akan yau, azabar na danaci ranar sam bazan iya misaltawa ba.
Nayi kuka kamar raina zai fita ko tausayi na bai ji ba yau kam bai min sassauci ko na 'kwayar zarra ba, ba 'karamar wuya nasha a hannun sa ba.
Tun daga ranar ya maida ni abincin ruhin sa, duk lokacin da yaga dama baya ko bi takan hawaye na...watarana da abin ya isheni ne ina kuka nake ce da shi ya 'kyale ni ya tafi wurin 'yam matan sa, ni banaso yaje inda ya saba wurin Husnah ya 'kyale ni.
Da jin na ambaci sunan Husnah sai ya bige min baki na take kuwa nayi shiru ina hawaye cike da takaici.
Sam ni banason abin nan da yake yimin, sa'a ta ma 'daya yanzu yakan fita asbiti bakin aikin sa baya yini a gida, hakan yasa nake 'dan samun sararin da zan zauna ni ka'dai, a haukana gani nake zama tare da shi 'din takura ne babba.
Abu 'daya da yake tilastawa kansa shine lalla6a ni a duk lokacin da yaso ra6a ta, amma idan zaki gan mu da shi haka bazaki ta6a zaton muna zaman kirki a gidan ba, saboda babu wata sha'kuwa ta zahiri a tsakanin mu rayuwar sa yake yi nima nake yin tawa, musamman ma da ya fahimci ba nason zama da shi shikenan ya sawa zuciyar sa gudun takurani, tunda ya fahimci bana samun walwala a inda yake sai yake taka tsantsan da duk abinda zai takurani balle ya shiga rayuwa ta, lokacin baccin ne kawai rayuwar mu take zama wuri guda wanda hakan ma dan yasan ba zai iya bane.
He was da so kind to me that koka'dan ban ta6a zata ba, ban ta6a tunanin zai saki ransa mu zauna har haka da shi ba hantara ba, cuz a zato na zan fuskanci abu fiye da hakan a zama tare da shi.
Ni sam hakan sai ta6a damu na ba dan banga aibun sa ba ballantana in hango illar sa, abu 'daya da na sani shine kawai Yah Deen mijina ne na aure wanda idan nayi masa biyayya wata'kil Allah ya ha'da ni da rahamar sa, ko shawarwarin da akayi ta 'dura min cikin kaina har yanzu suna nan a brain 'dina ban manta ba, sai dai har yanzu ban ta6a tunanin akwai ranar da zan iya amfani da wasun su ba, saboda a gani na a gun Yah Deen ba aiki zasu yi ba da ma ace wani daban ne, ban kuma ta6a yin tunanin zamantakewar mu da sha'kuwar mu zai iya saurin dai-daita ba idan nayi amfani da damar da nake da shi musamman da nasan cewa yakan sau'kar min da kansa aduk lokacin da yake son ra6ata ba.
Na bar hakan ne matsayin dole akai na ne kawai matsayi na na matar sa shiyasa a kullum yanayin zama na da shi bai ta6a damuna ba.
Da kaina na fahimci 6oyayyen halin sa na sanyin hali, kyautatawa da kuma sanin hakkin wanda ke tare da shi, sai dai idan baki zauna da shi sosai ba bazaki ta6a gane hakan ba, 6angare na kuwa duk da na fahimci duk wannan amma sam nakasa yin wani yun'kuri dan yin amfani da damammakin da na samu.
Ko dogon hira ban ta6a zama nayi da shi ba, gani nake kamar komai da Addah ta ta koyar dani idan nace zan yi a wannan gidan tamkar wahal da raina ne kawai, shiyasa na share na watsar da komai hakan ma da muke rayuwa ni anawa ganin ya ishe mu.
Na kan yi waya da duk makusanta na, Ammi na, Ummah ta, Anty Zainab, Addah na Maryam Saif da sauran su, Yah Usman ma sau 'daya na ta6a 'kiran sa muka gaisa ya tambaye ni akwai matsala ne nace da shi bakomai yace to shikenan idan da wani abin in sanar da shi nace to, tun ranar ban sake 'kiran sa ba haka kuma shima bai 'kira ni ba, Addah Saudah kam ba waya a hannun ta shiyasa ban ta6a samun daman magana da ita ba tunda na zo garin Bauchi.
Addah Maryam ma kan yawaita tambaya ta yanayin zaman mu sai ince da ita ai bakomai yanzu lafiya lau muke zaune, a kullum ta kanyi 'ko'karin ganin ta 'dora ni a kan hanya amma ni kam a wautata sai dai inji ta inyi murmushi kawai a 6oye..ko da wasa ban ajiye akwai ranar faruwan irin zaman da Addah Maryam take tunanin muna yi ba.
Anty Zainab ma yanzu bana gaya mata komai dake tsakani na da shi, kullum idan ta tambaye ni sai ince da ita ai ya canza yanzu ba kamar da ba...duk da haka Anty idan tayi waya da shi akullum sai ta yi masa fa'dan cewa dan Allah kar ya yawan yi min masifar sannan sai yayi dariya yace" Itace ta ta gaya miki ina mata masifa ko Anty?"
" a a haba dai, ai nasan halin kane Mu'een shiyasa".
Yace
" To ki kwantar da hankalin ki Anty, ni da ma ba zama nake yi agidan sosai ba yaushe zan ganta ma har nayi mata masifa.."
" Bangane baka zama ba, ba ka ganin ta? Kamar yaya? wai kana nufin a haka kuke zaman auren Mu'een?"
" Kai Anty ba yanda kika 'dauka nake nufi ba".
Tace
" To yaya ne?"
Yana sosa kansa ya bata amsa da fa'din
" Ina ganin ta mana Anty, amma ai kinsan abubuwa sun min yawa yanzu sai ahankali bana samun zama ne sosai".
Anty kawai sai tace
" Hmm.. Allah dai ya shirya min kai".
" Ameen Anty na".
Ya 'karasa maganar da 'yar dariya
Duk da hakan a kullum Anty bata gajiya da tunasar da shi yaji tsoron Allah ya gujewa sharrin duniya, ta kan kuma ce da shi dan Allah ya ringa sassauta min da yake tasan ni da masifar tsoron sa.
Ko Ammi ma ta kan yawaita tambaya ta abinda ke damu na acewar ta wai sanyi na yayi yawa, sai dai inyi murmushi ince da ita bakomai, dan ni yanzu nawin Ammi nake ji sosai...yanzu nasan asalin matsayin ta waje na.