← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 211

Sashe 173

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa tayi gaban inda aka kwantar da gawan ta sa hannu ta bu'de...take sai tayi saurin rintse idanu..." _Na shiga uku na ..Ammi Jasmine ce, wallahi Ammi yarinya ta ce dagaske, waiyo Allah ne, Ammi itama ta tafi ta barni? Dan Allah kice min ba gaskiya bane Ammi, Alhaji kace min zolaya ta take takeyi, dan Allah kuce mata ta dawo wallahi nayi rantsuwa zan kula da ita, bazan sake bari a cutar da ita ba.."_
Kan fuskar Jasmine ta dawo da kallon ta, fuskar ta ta tallafa tana kuka hawayen ta na 'diga kan jikin Babyn tace" Baby na..dan Allah ki tashi kinji, kin manta nayi miki al'kawarin zamu bar rayuwar su, kin manta nace miki zamu bar inda suke bari na har abada, amana ce ke awaje na Baby amma ban ri'ke amanar da Allah ya bani da kyau ba, dan Allah Maman Daddy ki tashi, ki tashi ki bani wata damar da zan wanke dukkan kuskure na, me zan gayawa mahallici na Baby idan kika tafi batare da na sau'ke hakkin ki dake kaina ba....Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un...Ya Allah ka farkar da ni daga wannan baccin...."
Tayi maganar tana dafe goshin ta da hannun ta 'daya...at same time tana kuka gwanin ban tausayi.

...Wata ma'kwabciyar su da ta shigo tun 'dazun itama kuka take yi sosai na tausayin Noor haka Hafsat ma, Ammi kanta bata iya ri'ke kukan ta ba.

Cikin su babu wanda ya iya zuwa kusa da ita balle ya bata ha'kurin kukan da take yi.

Dai-dai shigowan wata Hajiya dake bayan gidan su fuksar ta cike da Alhini amma ahakan bai hana ta ja ta tsaya ba ganin.kukan da Nnor ke yi, a hankali tabi sauran dake 'dakin da idanu taga duk suma yanayin da suke ciki babu alamun zasu iya iya lallashin wani.
A hankali ta 'karaso kusa da Noor ta kama ta ...tana fa'din"Haba- Haba Maman Baby, sai kace kin manta matsayin musulma kike, ba kuka ya kamata kiyi mata ba..Addu'ah zakiyi mata kinji.."
Jikin matar ta fa'da tana fa'din
" Innalillahi Wa inna ilaihi raji'un..."
Sai da maimaita ya kai sau biyar sannan ta fara fa'din" Ammi na! Ammi na..Ammi na.."
Da sauri ta bar jikin hajiyan ta nufi inda Ammi take taje ta fa'da jikin ta ta sake sakin wani kukan.

Ammi rungumar tayi da kyau tana 'ko'karin goge mata hawayen fuskar ta sam tarsa me ma ya kamata ta ce da ita...sosai Noor ke bata tausayi fiye da tunanin mai karatu.

"... shikenan Ammi yanzu bani da kowa?"
Hajiyan nan ce tayi saurin amsa ta da fa'din" Kina da Allah Maman Baby".
" Wallahi ina son 'ya ta kice da ita ta dawo min, zan kula da rayuwar ta kamar 'kwai Ammi, har makaranta ta ma zan bari saboda ita, wallahi ina son 'yata, Baby dan Allah kar ki tafi ki barni, ban ri'ke amanar ki da Allah ya bani ba, waiyo rayuwa ta...".
Kuka take yi sosai tana maganganu.
Yayin da Hajiyan nan ke 'ko'karin tausan ta da maganganu masu sanyi, a hankali.take nuna mata cewar" Ai duk soyayyar da take yi mata bai kai wanda Allah ke mata ba, shi ya bata Baby kuma shine ya kar6i abin sa dan haka tayi ha'kuri tayi Addu'ah, tace duk mu ma mutuwar muke jira a kullum Maman Baby, bamu san yanzu ne, anjima ko kuma gobe ba...ki daina tuhumar Allah akan abinda ya riga ya aiwatar...".
Duk maganganun da Hajiyan ke yi be hana Noor kuka ba, yayin da sauran ke faman tsiyayar da hawaye kawai Hafsat rungume da Afrah duk ta ji'ka su da ruwan hawaye.

Alhaji Baba dake harabar gidan shine yayi saurin shigowa jin kukan Noor da ya kasa 'karewa, shi kansa jikin sa yayi sanyi sosai, domin Jasmine akwai shiga rai yarinyar bata da hayaniya, sosai mutuwar ta shige shi shi kansa....Cikin natsuwa ya fara fa'din" Haba Hudallah... ke da nake yabon ki kuma, kukan amfanin me zai yi? kar ki manata fa idan an tafi ba'a dawowa, kukan ba zai dawo miki da ita ba...
Kiyi mata addu'ah kawai kiyi fatan Allah yayi mata  Rahama, Allah yasa mai ceto ce kinji...nasiha ya ringa mata mai ratsa jiki har ta yi shiru ta daina ihun sai dai hawaye....
Sai da yaga ta nutsu kafin ya juya ya fita yana tuno lokacin da yarinyar ta rasu a hannun sa.
Mintina goma kafin ranta ya bar jikin ta tana kallon idanun sa a lokacin bakin ta ya bu'du..yanda take 'kaerwa idanun sa kallo ne ya sa shi tambayar ta" Lafiya kuwa Aishatu kike kallo na haka?"
'Dan bakin ta ta tura sannan tace" Ai kaine ka mari Daddy na..."
Murmushi ya 'ka'kalo sannan yace mata " Daddyn ki baya ji Aishatu..shiyasa na dokesa".
" Ai shi babba ne kuma ba'a dukan Babba...".
Yace" To kiyi ha'kuri bazan sake ba...".
Tun kafin ya rufe baki tace" Baba Alhaji..."
Ta 'kira sunan sa tana lulllumshe idanu.
Sai yace" Na'am Uwata ya akayi?"
Idanun ta rufe tace " Mummy na...!..ai Daddy na yace da Mummy da Uncle Saif zamu tafi Madina da Makkah..."
Sai tayi murmushi, daga hakan bata sake wata magana ba tayi shiru, ba'a da'de ba sai yaga jikin ta ya hau kakkarwar sanyi, har alokacin kuwa fuksar ta da murmushin zasu je Makkah..sha'kuwa ta fara tana jan jiki, sai yayi saurin 'kiran Safwan a waya da ya tafi duba Sani bayan an fito dashi daga thearter room.
Sha'kuwan ta cigaba da yi wanda kafin Safwan ya iso ma har ranta ya bar jikin ta.
Shi kansa tsayawa yayi yana kallon ta a lokacin, jiyake kamar wasa, amma da yake shi babba ne kuma yasan mutuwa ya kuma san tana kan kowa hakan yasa shi shafa fuksar ka da fatan Ubangiji Allah yayi mata Rahama....kwana idan ya 'kare babu wanda ya isa ya hana mutum tafiya ko da kuwa babu ciwo dole ne atafi, a zahiri ciwon baby ba mai tsanani bane wanda har zaka kawo mata mutuwa kusa, domin Sani ya fi ta jikkata amma shi yanan nan lafiya kamasa aikin sa aka fito shi, ga kuma Deen da kenan shikam ma bai san inda kansa yake ba amma yana raye yayin da Baby take nan har hira tana yi amma dayake Allah ya riga ya rubuta iya rayuwar ta na duniya kenan haka anaji ana gani ta tafi...Allah kayi mana 'karshe kyakkyawa".

*****
        Noor tana nan har aka gama yiwa Baby suttura tana aikin kuka.

Addu'ah aka bu'kaci tayi mata amma bata iya tayin ba, bakin ta kaf kaf yake yi tana yi kamar zata rungume ta, idan dai kana wurin ko baka yi niyyan yin kuka ba ganin Noor ahakan ma sai ya saka kuka saboda tsananin tausayin ta..dan mata da dama cikin parlourn sai da suka zubda 'kwalla.

Ammi ce tayi 'karfin halin cewa..." Ki daure ko cikin zuciyar ki kiyi mata addu'ar kinji.."
Tace" To Ammi zanyi".
Sai ga wani sabon hawaye.
Wata mata tace" Kiyi ha'kuri dan Allah ki rage kukan maman Baby..".
Tace" Zan bari...zan bari Insha Allahu.."
Da rawar murya take basu amsoshin maganar su tamkar zautacciya.

Lokacin da akazo fita da Baby kuwa kamar zata shi'de saboda kuka a hankali cikin shashshe'ka take fa'din...shikenan yarinya ta, shikenan Baby na...Allah ya ji'kan ki mama na, Ubangiji Allah ya miki Rahama, Allah yasa haske ne ke jiran ki cikin qabarin ki...".

Duk kowa da ke wurin da Ameen ya amsa addu'ar tata, tausayin ta sosai ya kama su, saboda suna da labarin cewa mijin ta ma na can kwance a asbiti bai ma san da batun rasuwar ba...dole abin ya zame mata ba da'di ga rashin 'ya ga kuma jinyar miji...duk rashin tausayin ka sai ka tausayawa Noor idan ka ganta a wannan lokacin.
Jikin Ammi ta fa'da ta cigaba da rero kuka.

Kamar wasa wai Baby Jas ta tafi, tafiya kuma ta har abada, shikenan bazata sake ganin ta ba kenan..kamar yanda ta rasa Nannen su, ta rasa Mahaifinta...Allahu Akbar...Allah ka ji'kan mu ka bamu ikon bauta maka muna masu tsorin ka, kasa mana imani da yadda da 'kaddarar ka kowacce iri ce..."

Idanun ta sun kasa tsaida hawayen da suke yi  saboda tausayin kanta da take yi, gani take kamar Allah ma bazai yafe mata sakaci da tayi da rayuwar Baby ba gashi ya kar6e abin sa batare da ta cije gurbin kuskuren ta ba...tana makale jikin Ammi...bata ko iya amsar gaisuwa sai dai su Ammi.

Ba laifi kuwa dan duk da yake mahaifin ta baya nan amma sosai Jasmine tayi mutane an taru sosai wurin jana'izar Baby haka aka kaita makwancin ta na gaskiya...zuciyoyin mutane cike da alhini.

Mummyn Safwan da Mimah ma tuni sun zo gidan rasuwar
Kowa yaji sai jikin sa yayi sanyi, jiya-jiya yarinya na nan amma da yake ba a gayawa Allah yanda zaiyi sai gashi yau an yini babu ita...rayuwa kenan...Allah ka bamu ikon gyara kurakurakanmu kafin cikar wa'adin mu...Ameen"

Su Saif ma Alhaji bai sanar da su ba da yake sun riga sun sanar da shi cewa gobe zasu iso, yaso ya hanasu ma tun safen da suka yi waya amma sam sun kafe sai sun zo sunga jikin princess 'din su..Allah sarki basu sani ba ashe Baby kam ta amsa 'kiran Ubangijin ta.

Uncle Ja'afar ka'dai Alhaji Baba ya fa'dawa wanda shima sosai jikin sa yayi sanyi, lokacin da ya sanar da Anty Zainab kuwa har sai da yayi da na sanin sanar da ita cuz sosai ta tashi hankalin ta ta 'kara tashin nasa ma, kukan da tayi tunda yake da ita bai ta6a ganin tayi irin sa ba, tausayin su Deen takeyi sosai, domin tasan yanda ya 'kwallafa Jasmine a ransa...tun ranar ta gama shirin ta tace gobe zata taho Bauchi.

Uncle Ja'afar bai hanata ba cuz shi da kansa ma badan aikin Bank yake ba da tare zasu taho, amma dole ne sai ya nemi izini tukunna.

Hakan yasa da kansa ya shirya mata komai na tafiya zuciyar sa cike da tunani, shikan sa yana tausayin 'dan nasa, tunowa da irin yawan Pic 'din sa da na Jasmine dake wayar sa wanda kusan kullum sai yayi musu pic masu kayu ya tura musu wai su ga jikar su.
Chapter 173 · 0% Book details