← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 211

Sashe 25

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai ga mamakin sa da sauri Deen ya zo ya wuce shi batare da ya bi ta kansa bama balle ya samu koda kallon arzi'ki ba daga gareshi.

Da idanu Dr. Felix ya bi bayan sa da sakakken baki, sai dai mamakin sa ninkuwa yayi akan nada lokacin da yayi arba da hannayen Dr. Mu'een jikin wuyan Sani yayi masa sha'ka na gaske domin kallo 'daya zaka masa ka tabbatar ba da wasa yayi hakan ba hatta jijiyoyin kansa sun fiffito hakama idanun sa.

Waro idanu Dr. Felix yayi tare da dawowa baya da gudu yana fa'din " haba Dr baka ganin halin da yake ciki ne?
Me yayi zafi haka please?"

Yana maganar ne at the same time yana 'ko'karin cire hannun Mu'een daga wuyan Sani amma sam ya kasa.

Sani kam gaba 'daya ya cire rai a sake rayuwa a doron duniya domin kuwa ba 'karamin sha'ka Deen yayi masa ba, gashi hannun sa 'daya ne mai lafiya ballantana ya yun'kurin 'kwatan kansa.
Hawaye kawai yake sau'kewa cike da azaba sai kakarin fizgo 'dan numfashin daya rage masa da 'kyar.

Dr. Felix daya kasa raba hannun Deen da jikin Sani sai yayi saurin ciro wayar sa daga aljihun sa ya danna 'kiran Safwan inda yana 'daga wa yace " Dr. Please we need you here, ka zo da sauri please Dr. mu'een zai yi kisa".

Safwan dake 'ko'karin yiwa matar sa Hafsat jagora zuwa ward 'din da Noor suke 'kiran Dr. Felix ya riske shi, ai da hanzari ya bar ta yace tayi tambaya za'a nuna mata" da 'dan gudu-gudu ya kama hanyar male ward 'din dan kai agaji.

Wanda sunan Mu'een da yaji cikin lamarin ne ya 'kara rikita shi gaba 'daya.

Dr. Felix kuwa cigaba yayi da 'ko'karin 'kwatan Sani hannun Deen da har yanzun bai bu'di baki ya furta komai ba, da 'kyar yayi nasaran 'kwatan sa amma Deen ya'ki sakin sa gaba 'daya, mari ya rin'ka sau'ke masa hagu da dama idan Dr. Felix yayi yun'kurin dakatar da shi sai yayi masa wani kallo mai rikitarwa tsoro sai yasa shi matsawa baya.

Sani ya kwashi mari a 'kalla fiye da biyar a hannun Deen wanda sai lokacin da yake marin sannan bakin sa ya bu'du fa'di yake " i ll kill u right away.....i'm going to kill u today....Sani u cheated me u ruined my daughters life....u fool me da kyakkyawar fuska kasa na yadda da kai Sani...... idan ban kashe ka ba yau Sani ni mutuwa zanyi.....gara ka mutu ko zanji sanyi a raina......"

Da 'karfi ya girgiza shi yana hawaye yace " Sani mai yasa kaci amana ta, me yasa zaka min haka?
Why only my daughter?
Me na tsare maka a rayuwa Sani laifin me nayi maka?

Mari ya sake sake masa ya kuma fa'din " ka bani amsa Sani, open ur eyes and tell me meyasa ka min haka Sani?"
Ashe baka da tausayi baka da imani da sanin ya kamata?

Jijjiga shi Deen yake da 'karfi yana surutai kamar wani mahaukaci.

Dr. Felix kam hanyar waje yayi dan dubo wanda zai taimaka masa kan wannan lamarin.

Sai dai bai kai ga fitan ba suka ci karo da Safwan a bakin 'kofan shigowa, wanda ganin sa da ya sakeyi a rikice yasa bai ko tsaya tambayar sa komai ba ya zarce ciki, shima Dr. Felix ya rufa masa baya.

Yana isowa dai-dai Deen ya 'daga hannu zai kai wani marin wa Sani cikin kuka amma kafin ya sau'ke nashi sai Safwan ya riga shi sau'ke nasa marin kan kuncin Deen.
Gami da fa'din " baka da hankali ne Mu'een, me kake shirin aikatawa ?"
Cikin tsawa yayi maganar da 6acin rai.

Take Deen ya sau'kar da hannun sa gami da sakin Sani da ya jima da sumewa a hannun sa ya tafi la'kwab ya kwanta.

Mi'kewa tsaye Deen yayi da jajayen idanun sa yake kallon Safwan kallo na 'kas'kanci.

'Kirjin sa ya nuna da hannun sa 'daya gami da fa'din " Did u just slapped me Safwan....did u?"

"yes i did...."
Fa'din Safwan cikin masifa, hannu ya 'daga ya nuna Deen 'din dashi tare da cigaba da fa'din "........and ina tabbatar maka more is coming idan har kace zaka 'kara yi mana irin wannan haukan anan.....meke damun ka ne Mu'een?
Kai baka ganin halin da yake ciki ne?
Da wanne kake so yaji?".

Cikin tsawa gami da watsa hannu Mu'een ma yace " i don't bloody care Safwan!
I don't.....i thought da bakin ka ka tabbatar min da abinda ya aikata wa rayuwar 'ya ta? How dare he?
bashi da sence ne ko kuma rainin hankali me ya sashi aikata min hakan?
Yadda sosai sosai nayi da yaron nan Safwan fiye da kowa cikin ma'aikatan gida na, amma ji abinda ya aikata min, dubi abinda ya saka min da shi, ko tsoron Allah be ji ba talkless of yaji kunyar abinda yake aikata wa ya farma that little soul, ka tambaye shi Safwan me ya samu me ya tsinta a jikin ta? ribar me ya ci?.......wallahi Safwan ganin mutuwar wannan yaron ya fiye min komai a yanzu, bana 'kaunar sake ganin sa a rayuwa ta....Safwan....me na zama, miye matsayina? Me nene amfani na matsayin uba ga Jasmine, Safwan ina raye amma wani 'dan iskan banza ya lalata min rayuwar yarinya ta, ina jin tamkar bazan iya yafewa kaina ba, duka laifina na ne, nine na yadda da shi na amince da shi na bashi yadda na kuma dam'ka masa ragamar jigilar 'yata a hannun sa...yanzu me zan cewa ubangiji na, wani irin ri'ko zance na yiwa Baby idan ubangiji ya tambaye ni game da rayuwar ta....... ".

Kuka ne yaci 'karfin sa sosai da yasa shi dakatawa da maganar.

Zama yayi kan wani kujera dake 'dakin ya dafe kansa da dukkan hannayen sa biyu ya cusa su cikin gashin kansa, cike da damuwa ya sunkuyar da kansa gami da jijjiga wa, gaba 'daya ya nemi nutsuwar sa ya rasa.

Sosai tausayin sa ya kama Safwan dan ya sani koma waye irin haka ya faru da shi dole hankalin sa zai tashi, musamman ma idan kayi duba da 'kan'kantar Jasmine 'din, amma ya za'ayi?
wannan ba komai bane face daya daga cikin 'kaddarorin dake tafe da rayuwar 'dan Adam, babu kuma wanda yafi 'karfin 'kaddara matu'kar yana raye a doron 'kasa.

A hankali ya tako ya 'karaso kusa da Deen 'din, kafa'dar sa ya dafa tsawon minti guda batare da ya furta komai ba.

Dr. Felix kansa jikinsa yayi sanyi amma a haka ya daure yayi kan Sani yana sake duba shi tare da bashi taimakon gaggawa.

Cikin 'karfin hali Safwan yace
" I'm so sorry Mu'een..... please kayi ha'kuri.....the deed is alredy done babu yanda zamuyi.....'kaddara ta riga fata, sannan kai kanka kasani 'kaddara dolen banu Adama ce dole ka kar6e ta ko kaso ko ka 'ki imma mai kyauce ko kuma akasin haka, ba zamu iya ta6a canza ta ba.....kar ka girgiza kafuwar imanin ka akan faruwar hakan Mu'een, ka daure nasan ba da'di...it really hurt but Allah ya sani yasan meke faruwa and insha Allahu komai zai dai-dai ta tunda Jasmine yarinya ce, still tana da wani chance 'din da zata yi regaining duk abinda ta rasa.....ka daina damun kanka akan Sani as u can see tun daga yanzu sakayyar Allah ta kama shi, can't u see shirin cire mai hannu ake yi ne? Wannan ka'dai ya ishe shi sanin cewa Allah bai barin hakkin wani......idan kuma kai ka 'dauki hukunci a hannunka ka kashe shi kasan hukuma bazata barka ba.....Allah ma kansa ba barinka zai yi ba duk kuwa girman laifin da ya aikata maka...to ribar me ka samu ......?"

" i don't care Safwan ....koma me zai faru I'm ready to face it......su hukuntani su sani rayuwa cikin u'kuba da tsananin bauta da wahala wallahi bazan ta6a damuwa ba matu'kar akan Jasmine ne....Safwan"

Kai Safwan ya girgiza ha'di fa'din " Calm down malam don't u dare say that again...idan ka juri wahalar duniya ka iya 'dauka to tsakanin ka da mahallicin ka fa?
Zaka iya da wannan
ne ?

Shiru Deen yayi ya zuba wa 'kasan farin tiles 'din dake ward 'din idanu shi kansa yasan gaskiya Safwan ke fa'di amma me yasa yake 'kara jin zafin abinda Sani ya aikata masa.

Safwan cigaba yayi da fa'din " ......kowa fa nada laifi Mu'een dama haka rayuwa a kullum take tafiya.....kar ka tsaya duba girman laifin wani sam duba naka kayi ma kanka hisabi and then cigaba da tafiya......Don't ever think i was supporting Sani......just want to wake u up daga dogon baccin da ka tafi..idan har kai zaka ji zafin abinda Sani ya aikata maka first then turn back kayi recalling kaf 'din rayuwar ka, ka duba da kyau kayi tunani akai.......".

Tsaye Deen ya mi'ke da sauri yana sake tattare goshi ransa a matu'kar 6ace yace " me kake nufi ne Safwan bangane ba...me kake shirin sanar dani?"

" What i mean is clearly opened Mu'een....kai dai kayi 'ko'karin godewa mahallici kawai domin ba 'karamin son ka yayi da rahamar sa ba....ina jin kamar gaskiyan Noor ne...bana haufi akan abinda ta fa'da, babu mamaki sakayya Allah ya so yi shiyasa ya sanya maka ninkin son Jasmine a zuciyar ka fiye da komai, ya kuma baka ita matsayin 'ya mace sannan ita ka'dai a gaban ka domin kawai sha'kuwar ku tayi tsanani ta yanda ko menene ya samu rayuwar ta zaka fi kowa jin zafin hakan.....ina maka kwa'dayin rahamar ubangiji Mu'een gami da fatan wannan abinda ya farun ya kasance babban darasi kuma iznah cikin rayuwar ka......."

Tarin da Mu'een ya fara ne ya dakatar da Dr. Safwan ga cigaba da maganar da yake yi, da sauri ya taho ya ri'ke shi.

Tari yake yi yana dafe 'kirji cikin tsananin azaba har yana 'ko'karin kaiwan 'kasa amma Safwan ya rirri'ke shi yana mai sannu Dr. Felix ma da wata likita da bta jima da shigowa ba dan suke kula da Sani tuni suka yo kansa domin taimaka masa.

Kan 'dayan gadon dake 'dakin Safwan yasa aka kwantar dashi amma Deen ya'ki kwanciya.
Chapter 25 · 0% Book details