← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 211

Sashe 91

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Husnah kam taji da'din hakan sosai har ma ya sanya ta manta duk damuwoyin da take ciki da al'kawarin da ta yiwa ranta....haka suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki kamar da can baya.

Lokacin da ta samu tsarki kuwa batare da 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dora daga inda suka yi madakata, balle dama gashi duk sunyi missing junan su...ai hikenan.

*****
'Bangaren Alhaji Baba kuwa tun washe garin tafiyar Yah Deen ya tura wani amintaccen yaron sa Yusha'u can cikin garin Azare da sunan mahaifin Husnah da yake shima yayi zaman garin so bai wani sha wahalar gano inda Alhajin ya turasa ba, inda yaje domin yai masa kyakkyawan binciken da ya dace game da ita.

Cikin kwanaki biyu kacal ya kammala ya dawo, akan 'dan wannan tafiyar Alhaji Baba sadaukarwar 100k yayi saboda tafiyar, hatta da hotel 'din da Yusha'u yayi masau'ki da sauran abubuwa duk cikin ku'din yayi su, hakan ma lokacin dawowar sa ya dawo da canjin kusan 30k amma Alhaji Baba ya bar masa saboda jin da'din labarin da ya zo masa da shi.

Dama can mahaifan Husnah mutanen kirki ne na gaske basu da abokin gaba balle 'yan tsama, sai dai mahassada.

Duk iya binciken Yusha'u bai ci karo da komai da ya danganci 6atanci ga iyayen Husnah ba, ita ka'dai suka haifa daga ita Allah bai sake basu wata haihuwar ba, sannan mahaifin Husnah ri'ka'k'ken 'dan kasuwa ne da ya shahara ta 6angagori da dama, ya tara dukiya fiye da zaton mai karatu, sai dai Allah bai bar shi ya rayu cikin iyalan sa ba da mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Husnah.

Yawan takurawar da wani wansa ke yi masa ne kan ya bashi kaza yau kaza gobe kaza yafi damun sa, ya gina masa gida mai girman gaske kwatankwacin wanda yake ciki da iyalen sa, ya kai sa Hajji har sau uku wanda shi kansa mamallakin dukiyar ma zuwan sa Hajjin sau biyu ne, matar sa kuma sau 'daya amma dan kawai ya faranta ma Yayan nasa rai ya sanya shi biya masa har sau uku, ya kuma biyawa uwargidan sa ma taje sau 'daya, ya 'dau nawin karatun 'dansa Hisham har Cyprus yaje ya kammala kuma cikin saa yanzu haka yana aiki a Abuja...amma duk wannan abin bai sa wan mahaifin Husnah Alhaji Mamman ya bar 'kanin sa ya sake da dukiyar sa ba.

Ya kan zo da bu'kata ta ku'di a duk lokacin da ya ga dama kuma ku'di masu nawin gaske, haka mahaifin Husnah zai bashi check idan bashi da cash a hannun sa, bai ta6a nuna masa 6acin ransa game da hakan ba.

Amma duk ranar da ya kuskure yace ya bashi lokaci idan ya tambayi ku'di to kuwa ranar mahaifin Husnah ya taro march har da August ma kuwa, domin masifa zai sashi a gaba yanayi kamar 'dan cikin sa da ya haifa, duk wasu alkhairan da yai ta masa abaya mantawa da su yake yi ya dinga ya6a masa maganganu son ransa kan cewa yana yi masa wula'kanci dan yaga Allah ya hore masa dukiya.

Sosai irin wannan abin ke 6ata wa mahaifin Husnah rai amma sai yake dannewa kawai yake dauriyar bashi duk yawan ku'din da ya bu'kata.

Mummyn Husnah bata ta6a saka musu baki cikin maganar su ba illah idan taga yayi shiru yana tunani sai ta bashi ha'kuri da kalamai masu da'di da kwantar da hankali tana kuma sake nuna masa muhimmancin dangin sa agare shi.

Musamman ma da yake tasan cewa lafiya ba isan sa tayi ba.
Ciwon hawan jini yake da ga kuma Diabetes duk shi ka'dai.

Shekarun Husnah 15 lokacin tana Ss1 aka yi kidnapping 'din ta...imaging fa tashin farko 50million aka nema daga wurin iyayen ta, sosai hankalin mahaifin Husnah ya tashi...hakan yasa ya tattaro duk abinda ya san mallakin sa ne ya dun'kula ya samo million hamsin.

Tun faruwar abin sau 'daya tak wansa yazo yayi masa jaje, waya ma sai sai dai mahaifin Husnah ya 'kira shi idan ya matsu, lokacin da ya tattara ku'da'dan kwanan Husnah hu'du a hannun kidnappers 'din, amma idan kaga mahaifan ta sai ka tausayawa yanayin yanda suka koma saboda damuwa.

A bayan mota ya jefa jakar da ku'din ke ciki, yana tunanin hana shi sako hukuma da akayi cikin lamarin, haka yaja mota da kansa ya nufi gidan wansa da nufin sanar da shi cewa ku'din sun kammalu zai kai.

A gida ya same shi a can 6angaren sa dake da girman gidan da wasu iyalai kimanin mutane goma zasu iya rayuwa cikin farin ciki a ciki...kishingi'de yake idanun sa a lumshe, a haka mahaifin Husnah yaje ya tarar da shi, bayan sun gaisa sai yake sanar da shi cewa ku'din sun samu zai kai yanzu ya kar6o Husnah.

Fuskar sa babu alamun alhini yace" To shikenan sai ka dawo, gashi sun ce kai ka'dai suke bu'kata ba dan haka ba ai da na raka ka mun je tare"

" Bakomai Yayah..."

Bai kai ga rufe bakin sa ba Alhaji Mamman ya tare shi da fa'din" Amma ka tabbatar ba ka sa hukuma cikin lamarin ba kamar yanda suka bu'kata ko? dan banaso a salwantar min da rayuwar 'ya a banza ".

Mahaifin Husnah cikin sanyin jiki yace
" A a Yayah ban sa da su ba ni ka'dai zani"
" To to je ka Allah ya bada sa'a, idan ka kar6o ta ka kawo min ita nan gidan dan na lura ku jin da'din ku kawai kuka sa agaba baku damu da rayuwar ta ba, idan baku so ni ina son kaya na".
Ya 'karashe maganar a masifance.

Mahaifin Husnah fita kawai yayi yana fa'din" sai na dawo" Tare da ayyana wai har wani ne zai iya kwatanta irin son da yake yiwa Husnah ya kuma ce wai baya son ta bai damu da ita ba?...shi kansa sa yasan soyayyar da yake yi mata ya rinjayi wanda yake yiwa kansa ma.

Da wannan tunanin ya fice daga 6angaren ya nufi inda yayi parking motar sa..wan nasa ko irin ya biyo shi yaga ku'din ma bai yi ba.

Har ya bu'de mota zai shiga kuma sai yaji tsoro ya diran masa nan take, rufe motar yayi ya koma 6angaren Yayan nasa da nufin ro'kon sa akan ya taimaka suje tare ko zai 'dan ji 'kwarin gwiwa ajikin sa.

'Kofar babban parlour a bu'de take sai labile da ke sau'ke hakan yasa shi 'dagawa ya shige ya tunkari bakin sitting room da ya samu Yayan nasa aciki 'dazu.

_Sai dai me?_

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *45*

Irin kalaman da yaji Yayan nasa na furtawa ne suka matu'kar jijjiga shi, take ya 'dimauce idanun sa suka firfito waje, jijiyoyin kansa suka yi ru'du-ru'du....

Da hannu ya nuna inda Alhaji Mamman ke tsaye ya juya masa baya yana amsa waya bai ma san da cewa ya dawo 6angaren ba...dan haka sai ya cigaba da amsa wayar sa cikin kwanciyar hankali yana sake bada orders 'din yanda yake so abin ya kasance.

Bai san meke faruwa ba kawai sai jin fa'duwar abu yayi a 'kasa wanda ya sanya shi waigowa a rikice cikin hanzari da firgicin kar wani ne ya jisa har bai san lokacin da wayar ta fa'di a hannun sa ba ta tarwatse a 'kasa.

Ai kuwa ganin 'kanin sa Alhaji Hamza kwance a wurin ya matu'kar 'dimauta shi, ga dukkan alamu ma suma yayi, gumi ne ya fara karyo masa nan take saboda tashin hankali.

Kafin ya gama tantance abinda ya kamata yayi sai ga uwar gidan sa Hajiya Kareemah ta shigo 6angaren nasa da sallamar ta, ganin baya palourn ya sanya ta direct ta nufi hanyar bedroom 'din sa sai dai bata 'karasa ba lokacin da ta iso daf da 'kofan sitting room 'din sa sai tayi tunanin ko yana ciki, hakan yasa ta 'dage labilen kawai da yake dama da nufin dubawa kawai da le'ka so lokaci guda ta 'daga labilen gami da sallama a bakin ta.

A dai-dai lokacin Alhaji Mamman na shirin cire babbar rigar da ke jikin sa saboda yanda yaji tamkar ta takurashi tana sha'kesa, yayin da mahaifin Husnah ke kwance a 'kasa baya numfashi.

A rikice ta 'karaso ciki tana binshi da idanu bakin ta cike da tambayar abinda ya faru amma ta kasa furtawa.

Da 'kyar ta iya harha'do kalmar " Lafiya...Alhaji me ya faru?"

Ko 'kala bai iya yace da ita ba tsabar yanda ya ru'de, fuskar sa ka'dai zaka kalla ka fahimci ba a dai-dai yake ba.

Bayan fahimtar cewa suma Alhaji 'karami yayi yasa Hajiya Kareema da 'dan gudu-gudu ta nufi fridge ta 'dauko ruwa mai sanyi tazo ta yayyafa saman fuskar sa, yayin da Alhaji Mamman ke tsaye yana faman firfita da hular sa dake ri'ke a hannun sa, ji yayi komai ya kwance masa.

A hankali mahaifin Husnah ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su akan fuskar Hajiya Kareema then kan Yayan sa da suke uwa 'daya uba 'daya wato Alhaji Mamman.

Rintse idanu yayi a hankali hawaye ya gangaro ta gefe da gefen idanun sa saboda takaici...".... _Zai zo wurin ku ya kammala ha'do ku'da'den, yanzun nan ma ya bar wuri na bayan ya sanar da ni..so ku kula da komai bisa tsari saboda 'dan uwa na ne shi ban son ku bar kafa ko ka'dan da za'a iya fahimtar cewa da hannu na cikin lamarin..... sannan ina fatan baku illata yarinyar ko ka'dan ba ko?"_
Bai ji abinda aka fa'di daga 'daya 6angaren ba sai ji yayi Alhaji Yayan nasa yace" _To shikenan ku dai ku tabbatar bai zo da kowa ba kafin a sake ta dan bana son hukuma ta shiga cikin maganar kasan tonuwar asirin ku tamkar tonan nawa asirin ne and i hate that..."_

Abinda kawai zai iya tunawa kenan da yaji wan sa ke fa'di...wanda tashin farko kalaman yayan nasa suka bayyana masa cewa yana da hannu dumu-dumu kan sace Husnah da akayi.
Chapter 91 · 0% Book details