← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 211

Sashe 13

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Godiya sosai Sani yayi masa sannan ya koma masau'kin sa dake gidan....yana murmushin jin da'di, cuz shi kansa yana yabawa da karamcin Deen agare shi, bazai ta6a mantawa ba a jinyar mahaifin sa yaci a 'kalla kusan 80 thousand daga Deen 'din da yake aika masa wanda a fa'dar sa wai salary 'din sa ne, sosai yake yaba wa da hakan hatta mahaifiyar sa lokacin da zai taho ta matu'kar jan hankalin sa akan ri'kon gaskiya da amana ta kuma ce ya dinga kula da aikin nasa da kyau saboda ta fahimci ogan nasa na da karamci matu'ka, shi kansa Sani ya san hakan kuma yana yaba masa domin ba kowa keda hali irin nasa ba a wannan zamanin da damuwar junan mu bata dame mu, kowa kansa ya sani, kowa burin sa akansa ne, ka'dan daga cikin mu ne ke damuwa da yanayin halin da wanin sa ke ciki.
(Allah kasa mu dace).

*****
B'angaren Noor kam zuwan Sani bai wani 'da'data ba balle ya dame ta, dan ko ta kansa ma bata bi ba taci gaba da kai 'yar ta school tana kuma 'dauko ta, har tsawon sati biyu bata bi takan Sani ba, duk kuwa da cewa Deen yayi mata bayanin hutawan da Sani zai yi na sati ne da ya bashi daga a fa'dar sa sai ta bashi key amma Noor tayi banza dashi.

A sati na uku ne shi da kansa ya 'kira Deen da batun dan ya lura kallo ma bai ishi Noor ba a gidan, shi kuwa zama wuri 'dayan sai yaji ya ishe shi.

Deen bai yi mamaki ba dayake yasan daman ba kowani namiji bane ke juran zama wuri 'daya batare da wani abin yi ba, baya ga haka ma shi Sani yaro ne matashi tashin 'kauye mai ji da 'kuruciyar sa da wuya ya iya juran hakan.

Noor ya 'kira yayi mata bayani akan cewa Sani zai cigaba da kai Baby school itama sai ta huta ta maida hankali akan nata karatun.

Shiru Noor tayi bata bashi amsar komai ba kasantuwar wani bugu da zuciyar ta tayi da bata san silar faruwar shi ba, sai dai bata raba 'dayan biyu hakan bai rasa nasaba da jin batun sani daga bakin mijinta.

Abu 'daya da ta sani a yanzu kawai shine bata 'kaunar Sani har cikin zuciyar ta ba kuma ta 'kaunar kusancin sa da duk wani abinda ya shafe ta.

Sai da Deen ya sake magana jin shirun nata yayi yawa ne kafin itama ta bu'di baki tace dashi" wai dan Allah yah Deen sai shine zai na kaita?.......ni fa bance hakan ya takura ni ba Yah Deen please kabashi wani aikin daban ni zan cigaba da kai ta ina 'dauko ta".

Da mamaki Deen yace " miye dalilin hakan kenan Nuree?, i thought aikin da ya saba yi kenan a gidan bayan hakan ma kuma wani aikin kike tunanin zan bashi?"

Baki ta turo gaba tace dashi
" Ni dai ka canza masa please Yah Deen, wallahi sam hankali na bai kwanta da Sanin nan ba....ni zan cigaba da kai yarinya ta ina 'dauko ta, idan babu wani aikin da zaiyi kawai ka bar shi ya huta abin sa in yaso sai kana biyan sa tunda baka son rabuwa dashi".

Ran Deen ne ya 'dan fara 6aci saboda jin maganganun nata, a 'dan hargitse shima yace mata" wai me kike nufi ne Nuree?...don't you dare think zaki shiga hakkin naki karatun ne?..... ko angaya miki ban san cewa baki attending 12-1 lectures bane?"

Turo baki ta 'karayi daga 'dayan 6angaren tamkar tana gaban shi tace " ai ba kullum ne nake da 12-1 'din ba sau biyu ne kawai a week".

" Look Nuree....bansan rashin ji kin sani ko? Na riga na yanke decision and that's final, from now on Sani zai cigaba da fita aikin sa....kin fahimta ko?".

Tana shirin sake yin magana ya hana ta da fa'din " shhiiii.... ban son musu please".

'Dan sau'kar da murya yayi yace " ke baki son ki nutsu ne wai".

Fizgar maganar tayi dayake da haushin maganganun sa na 'dazun a zuciyar ta sai tace
" Wani nutsuwa zanyi Yah Deen...bacin yarinya ta bata da wannan damar".

Cike da mamaki Deen yace " kamar yaya kuma....Nuree me kike nufi?"

Tambayar da yayi 'din ne ya sanya 'dan sau'ko wa a 'dan nutse tace dashi
" Yah Deen kabar Sanin nan.....kwanakin can kafin ya tafi 'din nan ba 'karamin 6ata min rai yakeyi ba Allah".
Sai kuma tayi shiru.

Deen folding 'dayan hannun sa yayi a 'kirjin sa tare da fa'din" inajin ki miye dalili?"

" tsiran tafiya min yawo da Jasmine yayi, idan ya 'dauko ta baya dawo min gida sai kusan 1: o'clock koma fin haka, bacin da ba haka yake yi ba ai da da wuri yake kawo ta, kuma ai har makarantar naje na tambaya aka ce da zarar an tashi basu 'kara 6ata lokaci suke kama hanya amma sai ya zarce wani gurin.......kuma fa da wuri yake tafiya 'dauko ta tun 11:30 yake barin gidan nan 12:20 kuma zaka ga har sun dawo, amma a lokacin gaba 'daya sai ya canza yake zarce hakan batare da wani dalili 'kwa'k'kwara ba, dan ko na tambayi jin dalilin ma banda wasu silly excuse babu komai da zai gaya min, 'karshen ta yace sunyi wa wani lift ne ko kuma wai anyi accident suka 'dan tsaya a wurin ko kuma wani abu daban marar tushe.

Bana jin da'din hakan da yake yi sam sannan bamu gama da wannan 6angaren ba ya wani fara bawa Baby ku'di, inda ma Allah ya taimake ni bata iya kashe ku'di ba ai da sabar mata zai yi da hakan batare da na sani ba, ni gaskiya na gaji da halin Sani na tsani abinda yake yi, shi kansa ma na tsane sa dan haka kawai a canza masa wani aikin nafi jin da'din kai ta da kaina Yah Deen".

Deen sai yace " amma kin san babu kyau tsanar musulmi haka kawai ko?"

Cike da haushi tace " na jima da sanin hakan tun ba yau ba, ban san dai ko kaine ka sani yanzu akan Sani ba".

Goshi ya ha'de yace " meaning".

Cikin rigima tace da shi" Ni dai ba ruwana, ai tun a lokacin ma naso sanar da kai amma sai na sha'afa na manta da batun gaba 'daya".

Idanun ta har ja suka yi da ta ke maganar tsaban yanda abin yaci ranta balle data tuna gaba 'daya sai haushin Sani ya 'kara kamata sosai fiye da na baya ma.

Ajiyar zuciya Deen ya sau'ke tare da fa'din" to kiyi ha'kuri zan masa magana kinji, in dai hakane gaskiya baya kyautawa zan mishi magana dole ma ai tunda har yasa ana yimin habaicin abinda ya wuce ta dalilin sa".
Ya 'karasa maganar yana murmushi.

Kwafa tayi in ka ganta zakayi zaton wuri guda suka da shi tace
" wasa ka 'dauki maganar ko Yah Deen ?"

Bayyanan niyar murmushi yayi sannan ya 'kara da fa'din" a ah ni dai ba haka nake nufi ba Nureee ai nace zan masa magana, Allah ya huci zuciyar hasken Deen, ashe kin iya masifa har haka?"

Azafafe ta kara bu'dan baki tace
" Wallahi Yah Deen ni hankali na bai kwanta da shi ba...."
Bata gama maganar ba Deen ya tare ta da fa'din
"Control your anger madam ai nace zan masa magana ko?".

Noor bata sake ce dashi 'kala ba kawai ta yanke 'kiran dan ita ba haka take son ji daga bakin sa ba.

Da kallo Deen yabi wayar sai yayi murmushi a fili ya furta " *NOORUL HUDAH* ta kenan sarkin rigima".

Batare da wani 6ata lokaci ba yayi dialling numbern Sani.

Sani da ke zaune gefen mai gadi yayi saurin ciro wayar sa daga aljihu jin tana rurin neman agaji, sunan _Oga Dini_ da yaga ya bayyana kan fuskar wayar ne ya sashi amsawa cikin hanzari.
"Hello ranka ya da'de.....barka da war haka".

" Uhum Sani barka dai.....kana jina ko?"
Deen ya tambayesa.

Da " ehh yalla6ai inaji" Sani ya amsa shi cike da 'kaguwa ga son jin makomar aikin na sa.

" Nayi magana da mahaifiyar Jasmine tace min sam bata jin da'din abinda kake yi, ba ka kyautawa Sani.....me yasa baka dawo da Baby gida akan lokaci.....tell me".

Sosa kai Sani yayi tare da fa'din " ayi ha'kuri yalla6ai, wallahi akasi ake samu a lokacin amma insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba".

" Batun ku'di fa?"
Deen ya sake tambayar sa a takaice.

Cikin rashin fahimta Sani yace " ku'di kuma wani iri yalla6ai? Inajin wannan ai za6in ka ne sai yadda ka ce".
Ya 'karasa maganar da 'yar guntuwar dariya.

A tsare Deen ya katse shi da fa'din"
ba wannan nake nufi ba Sani, ku'di da kake bawa Jasmine nake magana a kai".

Sani sai cewa yayi " ohh yalla6ai insha Allahu shima 'din
bazan sake ba".

" Ina fatan hakan Sani, dan bama Noor ka'dai ba....ko ni bazan lamunci faruwar hakan a gidana ba, in kuwa ya sake faruwa ina tabbatar maka da kaina zan 'dauki mataki akai".

Cikin tabbatar wa Sani ma yace
"Ayi ha'kuri yalla6ai duk zan kiyaye".

" I hope so".
Kalmar Deen kenan ta 'karshe a hankali ya fa'di tare da yanke 'kiran gaba 'daya.

Sani dake zaune gefen Mai gadi sai ya juya ya kalle shi fuskar sa ko nuna alamun damuwa be yi ba cuz ya san da wuya ne Deen ya dakatar da shi a aiki batare da 'kwa'k'kwaran dalili ba shiyasa bai wani 'daga hankalin sa ba.

Da 'yar dariya yace da maigadi " Ji min matar gidan nan dan Allah, ba'kin ciki take dani shine harda ha'dani da mijin ta".

Mai gadin da yake shima ba wani babba bane cuz har yanzu bai cika 30yrs ba yace da Sani " ai naji kana ta neman afuwa...mene ya faru wai? naga ma tun dawowar ka ba fita aiki kake yi ba"
Chapter 13 · 0% Book details