← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 211

Sashe 4

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murna ta sake saki har 'kananun ha'koran ta na bayyana a fili ta sake fa'din " Daddy kenan bazanje school gobe ba?"

'Dago kai yayi ya kalle ta yana murmushi yace " ehh mana bazaki ba... sai idan mun dawo zaki cigaba da zuwa abinki kinji?"

Jas sai tace " Har da Mummy zamu je ko daddy?"

Da " uhm "
Deeen ya bata amsa a takaice.

Take kuma sai Jas ta 'dan ha'de fuska tace " Daddy.....!"
Deen yace " na'am 'yar gidan daddy".

Sai tace " Daddy kullum idan zamu dawo daga makaranta da Sani ko sai ya dinga........"

"Dukan ki?"
Ya tare ta da tambayar hakan.

Sai ta jijjiga kanta alamar " ah ah" tana mai cinno baki gaba.

Murmushi yayi tare da dafe bayan ta ganin yanayin da tayi da bakin tan sai yace " Sorry kinji, duk abinda yake miki zan yi masa fa'da ya daina kinji?"

Kai ta 'dage sama alamar " toh "

Deen sai yace mata taje ta samu Hauwa ta cire mata uniform 'din jikin ta sai ta dawo.

Tashi tayi ta fita da 'dan hijab 'din ta a hannu, Deen sai ya bi bayanta da kallo yana murmushi tare da tuno abinda yake yawan sata kawo 'karan Sani wurin sa, wato yawan tsokanan ta da Sani yake yi wai " cry-cry mai 'karamin baki"

Tun ba yau ba take yawan kawo masa 'karan sani dan ita sam bata so ace mata cry-cry 'din nan shiyasa ma yanzu bata fiya yin kuka ba dan gudun tsokana dan ko Deen 'din ma wani lokaci har da a tsokanan nata.

Tun farkon da aka saka a makaranta idan an kaita ne sai ta tayin kuka in ta gaji da zama tayi fa'din "Daddy" toh duk lokacin da a kaje 'daukan ta sai a same ta tare da Auntyn su, anan Auntyn zata basu labarin kukan da tayi shine su kuma suke 'dan mata wasa da hakan, musamman ma Sani da kusan kullum sai ya tsokane ta da hakan while
ita kuma Jas bata so....balle da yanzu ta 'kara wayo idan ya tsokabe fushi take yi masa.

Zaton Deen yanzun ma akan abinda zatayi magana kenan shiyasa ya dakatar da ita batare da ya ida jin furucin dake bakin ta ba.

Jas ta 'dan 'dauki lokaci kafin ta dawo cus sai da Hauwa ta yi mata wanka kafin nan ta dawo.

A jikin Deen ta lafe shima ganin Hauwa ta watsa mata ruwa sai kawai ya gyara mata kwanciya ajikin sa dan ta huta da kyau mintina ka'dan kuwa bacci yayi gaba da ita.

12:47pm Noor ta dawo gidan, dama hankalin ta na gida tun fitar ta bata samu nutsuwa ba saboda sanin da tayi cewa Deen na hanya a yau 'din, ji tayi ma badan test 'din da za'ayi ba da kuwa babu inda zata fita dan sosai tayi missing 'din sa a 'dan sati biyun nan a yayi baya nan.

Da sallamar ta ta shigo parlourn inda ta hange shi zaune yasa system a gaban sa Jas kuma na daga gefen sa a kwance tana bacci.

Noor da fara'ar ta ta 'karaso yayin da shima fara'ar dake kan fuskar sa ta sake fa'da'da fiye da na baya ya 'daga kai yana kallon ta yana murmushi tare da maida dukkan.hankalin sa gareta batare da ya motsa ba.

Har ta 'karaso inda yake ta zauna daga gefen sa tare da rungumar daga gefen sa a hankali ta furta " welcome back Yah Deen...tun yaushe ka iso?"

" Na da'de " ya bata amsa a takaice yana kallon cikin idanun ta still yana murmushi.

'Dan 6ata rai tayi tace " haba dan Allah Yah Deen shine kuma baka 'kirani na dawo ba?"

Hannu yasa ya rufe system 'din dake gaban sa sannan ya sake kallon ta yace " me yasa zan 'kira ki kuma keda kike fama da lectures? Yanzu da kika gama bagashi kin dawo ba?"

'Dan juyawa yayi ya kallo Jas yace " Jasmine ta taya ni hira kin gama har tayi bacci".

Kallon Jas 'din tayi itama sai yanzu ma ta lura da ita a cikin ranta ta ayyana yau kam da wuri suka dawo afili kuwa sai ta matsar da kanta jikin sa
Fuskar ta manne da tashi daga gefen kunnan sa ta furta " me ka ci to daka dawo?"

Kai ya juya mata alamar babu komai.

A 'dan razane ta bar jikinsa tana kallon idanun sa tare da zaro idanu tace " haba Yah Deen... meyasa kuma ?"

Ba tare da damuwar komai ba yace
"Jiranki nake yi mana kizo ki bani".
Ya bata amsa yana duban ta shima.

Murmushi tasaki mai 'kayatarwa na jin da'din abinda ya fa'da 'din tare da 'dan sake mai harara ka'dan na zaman da yayi hakan batare da cin komai ba.

Matsar da kanta ta sake yi ta bashi peck a gefen fuskar sa sannan ta mi'ke tsaye tana murmushi.......da sauri Deen ya kamo hannun ta dawo jikin sa yana 'ko'karin kissing 'din ta sai ta jijjiga mai kai tare ta yi masa nuni da Jas dake 'dan motsawa.

Deen murmushi yayi ya sake ta tare da komawa baya ya kishingi'da da jikin kujera yana binta da idanu.

Noor kam dinning ta nufa taje ta fara duba abincin dake wurin, murmushi ta sake saki ganin dagaske 'din bai ta6a komai ba suna nan yanda ta barsu.

Da yake tun safe kafin ta fita ta tanadar masa da abinci da komai da tasan zai bu'kata ko da bata nan, da yake tasan ba mamaki ya dawo bata gidan sai kuma gashi hakan ne ya faru.

Fridge ta wuce ta 'dauko ruwa da lemon zo6o datayi masa mai da'din gaske ta zo ta dire akan table sannan tayi masa bismillah tare da fara zuzzuba abincin.

Har ya taso ya iso wurin bata gama serving musu ba, isowan shin ne yasata ta ja masa kujera amma sai yayi kamar bai gani ba, instead ya zauna ah ah sai ya tsaya daga bayan ta ya rungumo ta ta bayan tare da sau'ke kansa akan kafa'dan ta yana sau'ke mata hucin numfashin sa dake fita a hankali yace " Nureen Deeen "

" umm"
Ta amsa shi dashi tana mai mayar da duk kan hankalin ta gareshi.

" i really....missed.... u"
Ya sake fa'di a 'dan hahhar'de yana goga mata hancin sa a wuyan ta.

Ba tace da shi komai ba sai shine ya sau'ke mata 'karamin kiss a wuyan nata daya sata lumshe idanu.

Sakin ta yayi ya zauna a kujerar da ta ja masan yayinda Noor taci gaba da ha'da masa abincin a gaban sa, bata zauna ba sai da ta zuba nata plate 'din ma sannan ta zauna.

A hankali suke cin abincin fuskokin su cike da annuri har suka 'kare gaba 'daya.

Deen na kammala cin abincin ya shirya ya fita sallan azahar jin an fara 'kiraye-'kiraye.

Koda ya dawo daga masallacin sai ya samu Jas ma ta tashi a baccin har sunyi sallah da mahaifiyar ta.

A gaba yasata taci abinci har ta 'koshi sannan yasa Noor tasake yi mata wanka dan ta warware.....shiri sukayi cikin kyakykyawar shiga mai 'daukan hankali, sky blue captan ya sanya ajikin sa tare da karye hula gefe guda tamkar wani 'dan sarauta ya fito sai walwali ya keyi, yayin da aka shirya Jas cikin wata doguwar riga pink colour mai fa'di da kyau da tsada ga birgewa ga duk wanda ya kalla, 'dan 'karamin farin veil ne a kanta da farin cover shoe abin sai sai wanda ya gani.

Noor photo tayi ta 'daukan su kala tana yaba kwalliyar su tare da mitan itama aje da ita amma Deen yace ah ah wannan fitar ta musammance.

Daga 'karshe sai sukayi selfie dukkan su gwanin birgewa suna dariya.

Sai da suka gama 'daukan photon ne sannan suka fita Jas na yiwa Noor bye-bye tana dariya hannun ta ri'ke cikin na Deen suka fita daga parlourn suka nufi harabar gidan.

Sani driver na hango su ya mi'ke da sauri yana washe baki zaton shi koda tare dashi zasu fita, amma sai Deen ya dakar dashi da fa'din " karka damu yanzu zamu dawo ka huta abinka".

Deen na gama fa'din haka yayi gaba ya bar tsaye agurin, har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya tare da waigowa yace
" Sani!

Da 'dan hanzari Sani ya 'karaso inda suke tsayen yana fa'din " na'am ranka ya da'de!"

Deen na murmushi yace " wato Sani har yanzu baka daina tsokanan Princess 'dina ba ko...'dazun nan ta sake kawo min 'karar ka".

'Dan sosai kai Sani yayi yace
" Insha Allahu baza'a sake ba yalla6ai, yanzun ma ai ta girma ta zama 'yan mata bata kukan ta daina....ko Jasmine?"

Kai Jas ta 'daga masa alamar "ehh"

Deen ma Jasmin ya kalla yace " kinji ai yace ba zai sake ba ko.....so no more complaint.....okay?"

Sai ta sake 'dage kai sama tana murmushi.

Juyawa Deen yayi suka cigaba da tafiya tare da cewa Sani " sai mun dawo to"

Sani ma sai yace
" to yalla6ai...Allah ya tsare yasa a dawo lafiya"

'Dan 'daga murya yayi yace " Jasmin a kawo min tsaraba ko?"

Jas bata waigo ba sai kawai tace " zan kawo maka sweet da choculates "

Deen murmushi yayi yayin da Sani ya sake wangale baki yace " to 'yar albarka sai kun dawo ina nan ina jira"

Jasmin bata sake bi ta kan maganar tasa ba har Deen ya bu'de mata mota ta shiga sannan ya zaga shima ya shiga tare da tada motar, horn ya dannawa mai gadi lokacin da suka isa bakin gate 'din.

Suna fita daga gidan Jas tace
" Daddy tunda ka dawo yanzu kai ne zaka na kaini school ko?"

Deen take sai yace " ah ah.... mamana ni ai soon zan koma, Sani ne zai na kai ki kinji?"

'Dan tura baki tayi tace " Daddy ni fa bana son Sanin nan kullum cinye min........ baki na yake yi"
Chapter 4 · 0% Book details