Sashe 174
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko motar da Uncle Ja'afar ya siya masa ma sai da 'dora Baby akai tana zaune ta sha wata jar riga mai kyan gaske ya yi mata pic ya kuma sawa aka 'dauke su tare da shi ya turawa Uncle J da emojin dariya 'kasan Pic 'din yasa hope watarana jirgi Baby zata ciyo mana.
Ranar Uncle Ja'afar yasha dariya a fili ya furta shai'danin yaro kawai...kar kayi fatan Allah ya azurta ka ka siya ka tsaya maula a 'kar'kashin yarinya, nan gaba ai idan kaga na siyi abu to ita da kanta zata anfanu da shi ba kai ba.
Dariya shima Yah Deen 'din yayi masa...Allah sarki, ashe zaman ta tare da mu na 'dan lokaci ne. Yau gashi babu ita.
Hankalin Noor bai tashi ba sai da dare yayi ta kasa bacci...idan ta rufe idanu Baby kawai take gani sai tayi saurin bu'de idanu tamkar zata ganta gaban ta amma shau babu ita, hawaye ta ringa yi tana daga kwancen take tuno maganganun da suka yi da ita da safiyar yau 'din inda tace"...Mummy ina Daddy na? Waye ya saki kuka Mummy? Anjima zan gayawa Daddy na ya rama miki kinji?...'kwalla ta share tana sake tuno lokacin da Baby tace mata" Mummy ki daina kuka..." A lokacin sosai tsigar jikin ta taji ya tashi ashe daga lokacin Baby bazata sake rarrashin ta ba, shiyasa ma ta yi ta kallon idanun ta amma bata gane komai ba duk da kallon da baby ke ta binta da shi...Ashe amsar tambayar da ta bata bata yi kuskure ba lokacin da ta tambaye ta cewa tana so su koma gida ne Baby sai tace da ita" Ni ba dake zanje ba...".
Allah sarki rayuwa gashi ta dawo gidan kuma bata dawo da ni ba...shikenan bazan sake kallon ki ba Mama na? Shikenan kema kin tafi?"
"... _ban yi Pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi_ ..."
Wannan maganar da ta tuno ne ya toni asirin kukan ta, sosai take jin ciwon wannan abin, gani take har abada babu wanda zai 'kara yi mata cutar da zata kai mata wannan abin, Sani da Ubangidan sa sun cuceta, cuce mafi tsananin ciwi a zuci, gashi sanadin su ta rasa Baby, rashi na har abada..."..
Kuka sosai take yi sahf ta mance da cewar dare ne ba rana ba.
Ammi ce ta ta shi ta cigaba da kwantar mata da hankali ha'de da nasiha mai ratsa jiki. Wanda tun faruwar lamarinbsai yanzu ta iya yi mata magana mai tsayi har ma da Nasiha mai sanyi.
Kwana tayi tana tunane-tunane batare da ta iya rintsawa ba, ko gaisuwa idan anzo sai dai su Hafsat su amsa da su Ammi amma ita kam bata iya fa'din komai.
Cikin Alhaji Baba da Ammi kuwa babu wanda ya sake waiwayen inda Yah Deen yake ko su damu da halin da yake ciki, tausayin sa ko misqala zarratin babu shi a zuciyoyin su.
Da yamman ranar su Zaidu suka iso, a bakin Safwan suka ji halin da yake ciki take kuwa sai hankalin su ya 'kara tashi, sosai suka ji mutuwar Baby har cikin jinin su, dan kuwa babu wanda be zubda 'kwalla ba, ganin basu ga 'dan uwan su bane ya sa suka tambayi Alhaji Baba sai yace da su shima be sani ba.
Safwan ne ya girgiza kansa sannan yayi musu bayanin komai ganin kamar hankalin su ya tatshi da rashin ganin san, zaton sa ko sanar da su in zai sa su samu natsuwa.
Ai kuwa take ya 'karya ta batun sa dan kuwa kuka suka ringa yi kamar 'kananun yara, abin duk ya musu bazata, da yake su sun taho ne kawai jin cewa Jasmine tayi accident amma har suka iso basu san cewa already ta rasu ba, basu gama wancan jimamin ba kuma ak 'kara musu da wani sai kuma 'dan uwan su na can jikin na'urori bai ma san da batun rasuwar Baby ba.
Zaid kam bai iya ya motsa zuwa ko ina ba, ya zauna a wurin karban gaisuwa, cikin ransa yake ro'kon Allah akan ya tausayawa Yah Deen ya sassauta masa wannan abin, gani yake tamkar sun yi masa yawa damuwan dole zai illata shi, tun ma bai san da batun jinyar baby ba gashi ya shiga coma ina ga yasan cewa Precious Babyn sa ta tafi ta bar shi...tausayin sa sosai Zaid yake ji yayin da wani 6angare na zuciyar da ke jin haushin Yayan nasa da ya 'dauki drivern da be iya tu'ki sosai ba gashi ya salwantar musu da rayuwar Yarinya a banza...a ganin Zaid kamar rashin iya tu'ki ne ya kawo accident in.
Saif kam kasa natsuwa yayi domin dauriya yasawa zuciyar sa ya danne komai ya danne damuwar rashin Baby musamman da yasan cewa ko ya damu kansa ma Jasmine ba dawowa zatayi ba so da me rai ake yi dan haka hankalin sa duk ya tattara ya dawo da shi kan 'dan uwan sa...cikin zuciyar sa yake juya amsan da Alhaji Baba ya basu game da Yah Deen in, dole yasan akwai wani abu amma haka kawai Alhaji Babab bazai ce bai san inda yake ba bacin zaman kar6an gaisuwan 'yar sa ake yi, babu ammaki akwai laifin da yai masa shiyasa har ya fa'di hakan game da shi.
Abin sosai ya dame shi, Zaid kam ma ko aka bai sa ba, balle yayi wani tunani akai.
Saif ne ka'dai yaje har asbitin ya dubo shi a daren ranar batarecda ya bari ya kwana ba, wanda har a lokacin ma ya tarar da shi ne bai san waye akan sa ba...duk yanda ya so ya danne batun rashin Baby amma ya kasa, sosai yake ji da Jasmine yake sonta fiye da yanda yake son kansa, hakan yasa tunanin ta kan yawaita zuwa brain 'dinsa lokaci kan lokaci zaki ga yana share hawaye da fatan Allah ya ji'kan ta, ashe haka rayuwa take?"
Sani ma tuni ya farfa'do yayin da Dr.Felix ya cigaba da bashi kulawa, cikin sa'a akayi aikin kuma anyi nasara sai fatan Allah ya kiyaye na gaba...sani.ya zama mai hannu 'daya, sa'an sa 'daya ma hannun hagun aka cire aka bar shi da dama.
Tunda ya farka kuwa hawaye yake zubdawa,.nadama sosai ya shige shi matsannanci, da kansa yake Allah wadai da halayyar sa, yasan idan Umman sa taji abinda ya aikata ma da 'kyar ne idan zata yafe masa...kaico na...na bi son zuciya gashi ta kaini ta baro ni...sai gashi tun a duniya naga sakamako na ..Yah Allah ka yafe min, Yah Allah ka ji 'kaina, ka bani lafiya ka kuma bani 'kwarin gwiwar da zan iya dur'kusawa gaban oga Deeni in nemi yafiyar sa bisa cin amanar da nayi masa, in ce Maman Baby ta yafe min raina mata hankali da nayi, In ro'ki Jasmine tai min afuwa badan hali na ba, nayi al'kawarin zame mata bawa har 'karshen.rayuwa ta matu'kar zata yi min afuwa ta yafe min abinda na yi mata.."
Kuka yake yi sosai wanda ya rasa mai lallashin sa, bashi da kowa da zai ce masa kayi ha'kuri daga shi zai tarin nadamar sa a zuci.
Washe gari Sai ga Su Ishaq tun daga Maiduguri inda sun taho dan Alhaji Baba da kansa ya sanar da Ishaq rasuwar Jasmine cus duk cikin abokan Deen Ishaq yafi kwanta masa sosai.
Tare suka taho da su Imam, Anas da wasu daga cikin abokan su na makaranta da duk ya sanar mawa.
Kowa yaji labarin rasuwar Baby da kuma rashin lafiyan Mu'een Noor ake fara tausayi, saboda dole ansan sai ta shiga wani hali sakamakon rashin 'yar ta ga kuma ga Miji can kwance shima rai a hannun Allah.
Kwanan sa biyu kafin ya dawo hayyacin sa..da salati abakin sa, abu na biyu da ya ambata shine sunan Noor followed by 'yar sa Jasmine...
Safwan aka yi saurin nemowa yazo lokacin da ya iso hannun Yah Deen dafe kansa yana yayyamutsa fuska duk jikin sa wani iri yake jin sa...yana jin muryar Safwan sai yace"...Kaina Safwan ciwo".
Matsawa Safwan yayi kusa da shi yana yi mar sannu tare da nema masa sau'ki daga wurin Ubangiji.
Bai jima da farkawan ba sai ga Saif ma yazo dam baya iya yin awa biyar masu kyau batare da yazo yaga halin da 'dan uwan sa yake ciki ba.
Sosai yake bashi tausayi dan yasan a zahiri Yah Deen sai yafi kowa jin ciwon mutuwar Baby Jasmine.
Tausayin 'dan uwan nasa ne ya sanya shi kuka yana tsaye daga bakin 'kofa yake share hawaye, Yah Deen sai tsura masa idanu yana kallon sa da lumsassun idanun sa amma bai furta masa komai ba.
Ganin hakan ne yasa a hankali Saif ya 'karaso ya matso kusa da shi sannu yayi masa cikin tausayawa yana me kawar da kai dan baya so ya fahimci halin da ake ciki tun yanzu.
Baya jin ciwin komai sai 'kirjin sa ka'dai da yayi masa nawi sai kuma kansa jikin sa dake ciwo kuwa yasan ba komai bane face gajiya da kwanciya wuri guda da yayi, dan haka da kansa ya yun'kura ya tashi ya zauna, cire zcannular dake hannun sa yayi...Likitan sa da Safwan na yi masa fa'dan baya bin ka'ida kamar be san dokar aiki ba.
Ko tanka su bai yi ba, a fa'dar su ma wai ya tsaya tukunna a gama tabbatar da sau'kan ciwon kafin ya tashi..." Kaina ka'dai ke min ciwo..".
Daga fa'din hakan bai damu ba kawai ya tambayi Safwab iya kwanakin da yayi a kwance Safwan yayi masa bayani sai ya jinjina kai tare da mi'kewa tsaye ya nufi bayi da dubara ya 'dauro alwala ya fito.
Haka yayi sallolin sa batare da jan dogin surori ba dan jiri baya barin sa 'kafar sa ma rawa take yi masa sosai...idan yayi sai ya tsaya ya huta kafin yake cigaba da jerowa.
Saif ne ya tsiyaya masa fresh milk mai 'dan sanyi ka'dan amma ya 'ki sha shi wai Coffee zai sha, duk yanda Safwan yayi 'ko'karin nuna masa muhimmancin shan fresh milk in ammaYah Deen 'kin amincewa yayi..sai da yaga Saif na hawaye kafin ya ansa ya 'dan sha yana kawar da kansa.