Sashe 15
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan faruwar hakan ne Deen yazo da kansa inda yazo wa Noor da batun, tare da 'ko'kon sa na barar ha'kuri akan 'kiran ta da Jiddah tayi, cuz ya san kallon sa take yi da hakan koda kuwa bata furta ba.
Babu bu'katar yi mata 'karyan cewa Jiddah ba budurwar sa bace dan haka shima bai 'dauki wannan layin ba kawai sai yace da ita shi bai san lokacin da har Jiddah ta 'dauki Number a wayar sa ba, tare da 'ko'karin nuna mata cewar ai shi da Jiddan ba wai wata 'ka'k'karfar ala'ka bace tsakanin su... kawai dai ta kan yawai ta zuwa office 'din sa ne, yace ba mamaki a irin hakan ne ta samu daman 'daukan numbern nata....cuz so many times ya kan bar wayoyin sa kan table cikin office idan zashi wani wurin.
Noor bata wani damu sosai ba, dan ita kanta tasan dama abu ne mai wahalar gaske ace Deen bai da budurwa a Abuja kamar yanda da yake da wahala ace shine da kansa ya bada numbern ta, ko kuma ace da yardar sa wata ta 'kira layin ta, sai dai in baya cikin hayyacin sa ne, dan haka har zuciyar ta tayi masa uzurin wannan batun.
Abu 'daya ne damuwar kuma shima tunda bata da hurumin goge shi dole ta sanya wa ranta ha'kuri akai....wato the fact that Deen yana neman Jiddah.
Sosai tayi 'ko'kari wajen nuna masa rashin damuwar ta akan hakan ta kuma 'kara da fa'din kar ya wani damu ita bata sa batun ma aranta ba, ai shi 'din mijin mata hu'du ne, matu'kar zai iya da su sunnah ce babu wanda ya isa ya hana shi......"
Abinda yafi tsaya masa arai shine da ta 'karasa maganar da fa'din " ai da wani irin rayuwar ma gara kayi auren yafi mana gaba 'daya".
Da kansa yasan magana ta gaya masa inda ta bashi statement 'din a hannun sari, kuma sosai ya sara da ku'din sa, dan kuwa ya fahimce ta, amma bai damu ba tunda itama ta fahimce shi akan batun wayar Jiddah.
Wannan ne ka'dai damuwar sa a lokacin dan zai zama ne kamar cin zarafi akayi mata shiyasa ya kwantar da kansa gareta.
Itama Noor bata sanyawa ranta komai ba duk ta share su illah sunan Jiddah ka'dai ne da bazata ta6a iya mantawa da shi ba a rayuwar ta, tuni ta sanya ta cikin jerin sunayen dake zane cikin allon zuciyar ta.
Duk wannan abin ya faru ne cikin sati biyu kacal bayan ta bawa Sani ragamar kaiwa Jasmine makaranta, duk ta watsar da komai ta zuba a dustbin ta fuskanci rayuwar ta.
Domin a fa'dar ta har yaushe zata rayu cikin farin ciki matu'kar tace zata sanya damuwar wasu a kanta, dole ne ta fuskanci nata rayuwar itama ta nutsar da nata rayuwar, addu'ah ce ka'dai bata ta6a gajiya da yin ta kuma tana da ya'kinin Allah zai waiwaye ta komin daren da'dewa, tun yanzu ma tafara ganin sauyi tattare da rayuwar Deen, domin duk wani kulawa da ya dace yanzu yana bata shi ita da 'yar ta, yanzu ko 2weeks baya kaiwa a Abuja yake zuwa weekend, duk sati yana Bauchi.
Idan ta dubi rayuwar su farin cikin su da kuma canjin da ta 'dan fuskan ta game da Deen kawai sai dai ta godewa Allah " Alhamdulillah kawai take furtawa, daman tasan addu'ah makami ce ta mai imani, kuma garkuwa ga duk mai yin ta, ta sani dama wataran Allah zai dubi al'amuran ta ya amsa addu'o'in ta.
Lectures 'din ta kawai tasa agaba da kuma batun carryover 'din ta, dan so take ta gyara su tun yanzu ba sai tayi gaba ba.
*****
*Bayan sati shida*
Ya kasance ne ranar Wednesday .....rana na biyu da bazata iya mantawa dasu ba cikin ranakun ba'kin cikin rayuwar ta, bama su da dalilin mantuwa ita a ganin ta muddin rayuwar ta.
Ranar tun kafin a 'kira assalatu ta farka daga bacci, bata san dalili ba amma haka kawai taji baccin ta ya yanke, kuma duk da haka bata iya tashi ta ta6uka komai ba tsurawa Jasmine idanu kawai tayi tana kallon ta cikin so da 'kaunar 'yar tata, yanayin baccin ta irin na yara ya 'dan saka Noor murmushi inda ta ha'da bakin ta ta cura shi gaba tana baccin kamar wacce ke fad'a da wani.
Tsawon lokaci tana kallon 'yar tata wani farin ciki take ji can 'kasan zuciyar ta data ke kallon Jas 'din, domin kusan itace sanadin farkon samun farin ciki a rayuwar ta iya zaman ta tare da Deen, lokuta da dama ta kan ji da ganin ta ne matsayin sanyin idaniyar ta.
Juyi tayi ta komar da kanta 'dayan 6angaren daya ke tana hutun sallah ne so har akayi sallah a masallaci aka idar bata bar kan gadon ba, azkar kawai take ta jerowa cikin ranta.
Sai da gari ya 'dan fara haske kafin ta yun'kura ta tashi, bathroom ta wuce ta watso ruwa inda tafito bayan ta kintsa kanta, shirin ta tayi cikin simple doguwar riga na atampa mai kalar sararin samaniya.
Jasmine ta tayar itama tayi mata wankan basu fito ba sai da ta sata tayo alwala sannan suka fito daga bayin.
Sai da ta goge mata jiki ta shafa mata mai tare da sanya mata pant da wata riga ha'di da hijab 'din ta tace tayi sallahr asuba.
Kai Jasmine ta 'dago ta kalle ta tare da fa'din " Mummy yau ma ni ka'dai zanyi sallahn?"
" ehh mamana yi abinki kinji, ni 'din tun 'dazu na tashi kina bacci nayi nawa sallahr".
" Nima to Mummy ki ringa tashi na muna yi da wurin tare kinji".
Sai Noor tace
" to naj...amma kiyi na yau 'din karki makara".
Ganin Jas ta fara sallah ne yasata barin 'dakin ta nufi kitchen sai data kammala ha'da musu breakfast kafin ta ha'da wa Jasmine na makarantar ta ta shirya komai, kintsa ko'ina tayi a kitchen 'din sannan ta fito.
Koda ta dawo 'dakin ma sai ta tarar da Jasmine har ta gama saka uniform 'din ta, dayake Jasmine akwai wayo sau da dama bata jira wai sai an sanya mata, sucks ne dai bata iya sanya shi a dai-dai sai Noor ta gyara mata tare da yaba wa 'ko'karin ta.
Parlour suka koma ta bata break 'din ta wanda basu jima da zuwa parlourn ba wayar Noor ta fara ruri, dayake tasan wannan 'kiran sassafen na Jasmine ne sai ta 'dauka tare da ha'da shi da kunnan ta.
"Hello Daddy!
Cewar Jasmine da ke 'ko'karin kaiwan 'dan gutsuren soyayyan 'kwan da ta gutsura yake hannun ta.
Noor tace "haba Jas bar abincin mana kuma sai kin gama wayar ko?.
Mayar wa Jas tayi ta ajiye tare da maida hankalin ta hankalin ta gaba daya kan wayar.
" Baby ya kike?"
yace daga 'dayan 6angaren.
Sai tace " lafiya... Daddy good morning".
Murmushi Noor tayi da jin salon Jas 'din da ta riga ta saba dashi a yanzu.
Kamar yanda suka saba kullum yau ma 'din hakan ne yakan 'kira yaji muryar tane kawai kafin ta tafi makaranta inda daga k'arshe kullum ya kance "Allah ya bada sa'a ya albarkaci karatun Baby" .
Watarana shiru take yi masa koda yayi addu'ar amma mafi yawan lokuta ta kance da shi "
Amin"
Sa6anin yayu da Jasmine cikin farin ciki ta amsa addu'ar tashi da fa'din "Amin Daddy...Allah ya kawo ku'di ka kaimu makkah da Madina da ni da kai da Mummy".
Deen ma da fara'a ya amsa ta da fa'din" Ameen ya rabbi mama na, Allah yayi miki albarka"
Noor dake jin su ne tayi saurin amsawa da "Ameeen-Ameeen".
7:00am suka fito daga parlourn suka nufi wurin motar da ake kai Jasmine makaranta, kamar yanda kullum Noor ke rakota yau ma d'in hakan tayi, wanda kullun sai taga bayan motar kafin take komawa ciki ta fara nata shirin tafiyar.
Yau 'din kuwa sai akayi rashin sa'a domin motar da Sani ke kai Jasmine makaranta sam ta'ki tashi.
Sani yayi-yayi amma duk 'ko'karin sa a banza.
Ganin kamar lokaci zai tafi ne ya sanya Noor komawa ta 'dauko key 'din motar da take tafiya dashi Benz ce mai tinted glass ta bawa Sani, ta kuma ce dashi ya kai Jasmine 'din dan ita sai 10:00 take da lecture yau, in yaso idan ya dawo sai itama ya kaita ya dawo gida da motar in lokaci yayi sai ya wuce ya 'dauko Jasmine 'din kafin a duba 'dayan motar.
Sani kar6an key 'din yayi suka shiga Jas nayi wa Noor bye-bye har suka bar gidan sannan ta koma ciki.
Da yake bada wuri zata shiga school ba yau 'din shiyasa koda ta shiga ciki sai tayi zaman ta a parlour tare da bu'de data 'din wayar ta.
Sa'kwanni ka'dan ne suka shigo wayar cuz ba da mutane da yawa take chat ba ita contacts'din ta 'yan 'kalilan ne.
A hankali tabi ta dudduba chat 'din har da na group 'din da take dashi na class mates 'din ta na makarantar da ta kammala secondary school 'din ta.
Sai wasu friends 'din ta na yanzu da ta yi a school.
Wata new number data gani ne 'karshen bu'dewa ganin messages har hu'du aka turo akai wanda tana bu'dewa sai taga ashe uku daga ciki duk pictures ne yayin da 'dayan ya kasance video ne na 49seconds aka turo kuma duk sun bu'du inda suka samu kyakykyawan mazauni cikin ma'danar pictures dake cikin wayar tata.
Arba da idanun ta suka yi da wanda ke kan pics 'din ya sanya ta bugun zuciya mai tsananin gaske, amma haka ta daure ranta dan wannan ba ba'kon lamari bane agare ta, daurewa tayi ta bu'de Video 'din duk da kuwa tana jin idanun ta sun k'an'kance suna barazanar daina gane mata komai.
20 seconds bata iya kaiwa tana kallon Videon ba ta ji komai nata ya tsaya cak har yana 'ko'karin tsayar mata da numfashi......bugun zuciya, tashin hankali duk suka ziyarce ta a lokaci guda, hatta yawun bakin ta sai da ya kafe kaf.
Rintse disassun idanun tayi ta kuma bu'de wa akan fuskar wayar still babu abinda ya canja, abinda take gani 'din gaskiya ne ba 'karya ba.