← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 211

Sashe 71

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin gida ma Ammi zaune tayi cikin natsuwa take ro'kon Ummah ta akan tayi ha'kuri bawai raba ta da 'yar ta take son yi ba kawai tsananin sha'kuwa zata duba dan girman Allah ta bar mata ni, tace hankalin ta kasa kwanciya yayi yau ka'dai da bata ganni kusa da ita ba, tasan badai-dai bane hakan bai kamata ta nuna damuwar ta ba tunda hannun iyaye na nake amma duk da haka ta kasa jurewa sai da tazo ta ganni.

Ina lafe gefen ta take maganar tana shafa kaina a hankali dan nima tunda naji muryar ta fito da gudu na rungume ta... daga yanda take maganar zaka fahimci cewa daga can cikin zuciyar ta maganar ke fitowa kuma babu zancen wasa a ciki.

'Dan takaitaccen tunani Ummah tayi....tun zama na agidan ban ta6a kawo 'karar abinda aka min wanda bai kama ta ba, ban ta6a zuwa nayi complaint ba akan wani abu da ba dai-dai ba, zama na nake a sake tamkar gidan mahaifina wanda ko makaho ya ganni zai san cewa hankali na kwance yake bani da wata damuwa a gidan

Comment.
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Wannan shafin naki ne Antyn mu ( Anty MAIMOUNATH O.G MAHNOOR)*
*Allah ya 'kare mana ke a duk inda kike.* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *36*

   ........Dan haka dan me zata hana ni?...dan me zata raba ni da jin da'di na?..ina ma laifin mai son naka?..ai wanda yaso naka ma tamkar kai yaso, in ba mai 'kaunar ka ba waye zai yi maka hakan....idan maganar mutane kuma zaka biye zaka da'de bakayi abin kirki ba, dan su mutane komai ka aikata to a wajen su kuskure ne dole sai ka samu masu zagin ka, in zaka yi abu to kawai saki ranka kayi abu saboda Allahn ka ba wai dan gudun abinda za'a fa'di ba tunda ba haramun a ciki..."

Muryar Ammi ne ya katse tunanin da Ummah ta ke yi...inda Ammi tace " Dan Allah Umman Saudah karki ce a'a..kinga gidan yanzu bakowa sai ni ka'dai, idan ma bazaki bar min ita ba to ki bani aron ta  mu cigaba da zama zuwa wani lokacin insha Allahu da kaina zan dawo miki da ita...i ll bring her back to u safely kamar yadda kika bani ita insha Allahu.."
Ammi tayi maganar cikin kwantar da muryar ta.

  Murmushi kawai Ummah ta tayi sannan ta biyo bayan sa da fa'din " haba karki damu Ammi, ai 'da na kowa ne...Hudah kam yanzu 'yar ki ce, ga tanan Allah ubangiji ya baki ikon kulawa da ita..Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi".
Iya abinda Ummah ta fa'di kenan daga haka kuwa taja bakin ta tayi shiru.

Take Ammi ta washe baki ta fara godiya wa Ummah ta gami da 'kara janyo ni jikin ta ta rungume ni sosai.

Alhaji Baba yau har cikin gidan mu suka shigo shi da Baban mu, shima Alhajin 'kara mi'ka godiyar sa ga Ummah yayi cike da jin da'di, haka ma Ammi ta ringa zuba godiya.

Kafin su tafi ya ciro ku'di ya ajiye wa Ummah ta duk yadda tayi kan ya bar ku'din amma Alhaji Baba ko kulawa bai ba, Ammi ce tace " Haba Ummahn Saudah...idan kina haka kuma ai sai ya zama tamkar ba'a zama 'daya ba...dan Allah ki bar shi ki siyawa jikokin ki alawa dashi".
Su kam su Alhaji tuni sunyi waje inda suka sake fita tare da Baban mu.

Ko ranar kuwa ban kwana a gida ba muka wuce da su Ammi...sai 'kara jana ajiki ma da takeyi kamar zata maida ni cikin ta.

Tun daga ranar Ammi ta ninka komai da take yi min ada, komai nawa sai da ya fita daban, ta shagwa6ani ta riritani tamkar ni ka'dai ce abu mai sunan 'da data fara gani a fa'din duniya, sosai Ammi ta 'kaunace ni ta nuna min soyayya na zahiri, sai dai duk abin nan bai sa na zama mara kunya ba, sai ma shiru-shiru da na 'kara zama a ko'ina...Ammi ta hanani yawan surutu sosai take kwa6a ta a fa'dar ta wai tafi so in dinga yin komai da 'kwa'kwalwa ta.

Ma'kwabtan mu kuwa da yake ranar da abin ya faru kan idanun wasun su ne sai hakan ya sanya suka canza akalar zancen su da fa'din wai su Ummah ta saida ni sukayi ganin Alhaji Baba ya bawa Ummah ta ku'di...mutanen duniya sam ba'a iya musu wallahi...(na lura abin ma harda hassada a ciki).

     *****
     Zaune suke, Ummah ta, Baban mu, Yaya Usman dan shima wannan karan yazo gida har Addah ta Saudah dake gidan mijin ta...

Baban mu ne yake neman shawarar su game da sabon gidan gona da suka bu'de a can Jos wanda Alhaji Baba yake so ya 'dora shi akai amma shi yana ganin tamkar shekarun sa sunja ya kuma manyan ta yana ganin kamar bazai iya ba.

Yah Usman ne ya dinga bashi 'kwarin gwiwa da nuna masa irin babban cigaban da hakan zai kawo a rayuwar su, yace hakan ai hanyar alkhairi ne kuma ya yadda da kai ne shiyasa karka watsa masa 'kasa a idanu Baba".

" Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa hakan shine mafi Alkhairi ga rayuwar mu gaba 'daya"
Ummahn mu abinda kawai tace kenan sai dai batun zama acan ne tace ita kam a a babu inda zataje tsofai-tsofai da ita ga 'ya'ya da jikoki..tace gara shi namiji ne, kuma ai dama su maza da nema aka sansu duk namijin 'kwarai baya zama...kuma komai nisan wuri matu'kar ka kyautata niyyar ka to Allah zai isan maka".

Da haka suka rabu da Yah Usman ya koma gidan sa ya barsu nan zaune Baban mu dumu-dumu cikin tunani.

Haka ma Addah Saudah da ta kasa fa'din komai har taron ya watse, farga take yi na yadda abin zai kasance a bakunan mutane...anya ba'a yi kuskuren saurin amincewa ba kuwa?"

Shi kam Baban mu  tunanin sa na can batun da Ummah ta tayi ne, yana ga hakan cigaba zai kawo a rayuwar sa, to amma ai zama zai iya kuwa, a wannan shekarun nasa yana ga ba mutuncin sa bane yin rayuwa shika'dai a wani wuri daban da ba cikin iyalan sa ba...kuma Alhaji yace an gama komai hatta muhalli an tanadar acan.

Ummah kamar tasan meke cikin ransa kawai tayi 'karfin halin bashi shawarar cewa ya samu wata kawai ya aura sai su tafi tare tace kaga ko ba komai bazaka rasa abincin da zaka ci ba duk sanda zaka bu'kata.

Bece da ita 'kala ba kawai ya tashi ya wuce 'dakin sa.

Hakan kuwa akayi kafin cikar sati biyu har an 'daura auren Baban mu da wata mai suna Jamila,  mijinta rasuwa yayi ya barta da yara biyar....ana 'daura auren da sati guda suka tattara suka koma Jihar Plateau da zama.

Umman mu kam ita ka'dai ta san yanda take ji har azuciyar ta ba ta san me zata ce da familyn Alhaji Baba ba, 'kauna ce wannan ko kuwa akasin haka, komai yana faruwa ne da mutuntaka,  girmama juna da kuma zumunci, amma daga 'karshe duk ciwon abin kanta yake komawa, farko Hudah, 'karfin abinda yasa ta bar ni da Ammi kawai yawan damuwa ta ne ita kanta tana so in daina a wancan lokacin, zaton ta ko ri'keni da Ammi zatayi na 'dan wani lokaci ne, amma sai gashi abin ya juya ya koma zaman da bashi da iyaka dai-dai yake da a 'kira shi na dindindin dan bata san ranar dawowa ta gare ta ba...and ita ka'dai ta san ciwon hakan da taji.

   Sai gashi kuma karo na biyu abin kan Baban mu ya koma, kuma ko wannan 'din ma zallar 'kauna ce da kuma yadda aka nuna, tunda dukiyar sa ya 'dauka ya dam'ka a hannun  Baban mu, amma sai gashi tun ba'aje da nisa ba abin ya koma kanta, tun zaman su da Baban mu bai ta6a ko tunanin yi mata kishiya ba balle aje ga yin ta, yanzu kuwa tashin farko sanadin Alhaji Baba gashi an mata kishiya, duk da cewa ita ta kawo shawarar amma dole da ciwo hakan nan kamar jira ake ba'a 'dau wani dogon lokaci ba komai ya kammala.

Sosai abin yake cin zuciyar Ummahn mu, wani sa'in sai taji tamkar dan ita su Alhaji Baba suka dawo garin mu, tunda gashi dumu-dumu an sar'ke ta ta 6angori biyu masu girma, an wargaza mata gidan ta ta yanda sake dun'kula shi zai yi mata wahalar gaske.

Duk kuwa yanda abin ya dami Ummah bata ta6a hirar da wani ko wata ba ciki kuwa hatta yaran ta, ta ri'ke ne daga ita sai zuciyar ta da fatan Allah yayi jagora kawai...idan hakan Alkhairi yake nufi ubangiji Allah ya tabbatar da shi.

*****
   'Bangare na kuwa bani da matsalar komai cuz duk abinda nake so shi ake yimin, hatta da gashin kaina sai da ya san da banbamci dan kuwa ba 'karamin kula yake samu daga wurin Ammi ba, har yanzu kuwa na kanje gidan mu, ni ka'dai wataran kuma da Ammi muke zuwa, lokacin da su Saif suka dawo hutu ma sai da muka je dasu Ammi ne tace muje mu gaida Ummah ta.

Ummah bata ta6a nuna min komai ba dake cikin ranta, haka zamuje mu gama iya zaman mu tana nan nan damu da nuna farin cikin zuwan mu a fili...bazaka ta6a fahimtar alhinin dake 'kunshe cikin ranta ba.
Chapter 71 · 0% Book details