← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 211

Sashe 16

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jifa tayi da wayar da k'arfin gaske wanda da ace ha'duwa wayar tayi da tiles ko kuma bango da labarin wayar tuni ya shu'de, amma sai a kayi sa'a ta sau'ka akan kujeran dake fuskantar ta a parlourn.

Bata kuma bi ta kan wayar ba ta dafe kanta da dukkan hannayen ta biyu, _innalillahi wa innah ilaihi raji'un_ take son fa'di amma sai ta kasa bakin ta sosai yayi mata nauyi.....sunan sane kawai ya iya zuwa bakin ta a wannan lokacin, inda da 'karfin gaske ta furta
" Yah Deeen!"
Da ce kusa suna da neighbour na kusa da babu abinda zai hana aji amon muryar ta.

Daga nan kuwa sai hawaye zir ya sauko mata kamar sau'kan fitsarin da ba'a shirya masa ba.

Fitan hawayen ne ya bata damar iya jero salati cikin kuka ta zube da6as k'asan tiles 'din dake parlourn tana kuka tana furta _innalillahi wa inna ilaihi raji'un............._

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍
[11/20/2019, 5:00 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Wannan shafin naku ne Team NOORUL na baku kyauta musamman saboda tsananin 'kaunar ku ga NOORUL......._ _ina son ku sosai_ 😍
*_Fatan alkhairi masoyana Allahu ya bar 'kauna_ 🤝*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *9*

Husnah kawai take hangowa a idanun ta lokacin da take faman kukan.
Wancan rayuwar, wancan lokacin, ashe ba'kin cikin ta bai 'kare ba har yanzun, ashe zata sake ganin wannan mummunan abin da idanun ta.

Ta kai 20mins tana zaune a a gurin, wanda tuni kukan nata ya riki'da ya koma na zuci, ga 'karan wayar ta tana ji yana ringing amma sam ta 'ki ko da kallon inda wayar take ma balle har taje dubawa, ganin kamar 'karan wayar na gauraya da damuwar ta yana sake 'daga mata hankali ne ya sanya ta barin parlourn ta koma cikin bedroom 'din ta.

Zuwa yanzun kam kukan ya tsaya mata sai dai na zuci, shiru ta zauna tana tunani kanta tallafe cikin tafukan hannayen ta, wai da gaske Yah Deen ne ta gani ko wani daban?

Tambayar da kenan take yiwa kanta take kuma son warware ta, sai dai bata jin zata sake iya kallon wayar tata ma ballantana har ta bin ciki abinda ke ciki.

'Karfin halin tashi tayi kamar an tsikare ta inda ta nufi closet 'dinta ta fara ha'da kaya nata da na Jasmine cikin akwati guda domin bata jin zata iya sake zama a 'kar'kashin Deen matsayin matar sa ta aure, ji tayi gaba 'daya ya fita aranta gaba 'daya.

*****
B'angaren Sani kuwa koda ya sau'ke Jasmine a makaranta niyyar sa ya dawo gida da motar amma sai yayi wani tunani.

Agogo ya duba sai yaga ai da sauran lokaci kafin tafiyar Madam nata makarantar dan haka sai ya zarce inda ake saida wayoyi, dama tun jiya yayi shawaran canza waya, yana da 'yan canjin sa naira dubu biyu shine yake tunanin idan ya ha'da da tasa wayar da kuma ku'din zai iya samun wata daban cuz tashi wayar na 'dan cijewa sosai take bashi haushi wani lokacin.

Koda yaje wurin saida wayoyin kuwa sai bai yi sa'an samu da wuri ba, inda ya 6ata kusan 2hrs 30minute yana ta faman dubawa da k'yar kafin ya samu wayar da tayi masa.

Ganin lokaci ya ja sosai ne ya sanya shi kar6a a gaggauce, speaker, mouthpiece da gurbin saka caji kawai aka gwada masa ganin komai normal ya sanya shi jefa wayar cikin aljihu kawai daga nan ya kamo hanyar gida batare da ya sake 6ata lokacin komai ba.

Da 'dan hanzari ya shigo gidan yana yin parking kuwa ya nufo mai gadi yana tambayar " matar nan ta fito bana nan ko Bala?"

" Wace mata kenan?"
Mai gadi ya jefa masa tambaya shima as if bai gane wacce Sani yake nufi ba.

Sani sai ya 'dan juya kai ka'dan tare da fa'din
"Kai da Allah ni ka fiya shirme wallahi kai, matar gidan nan nake nufi mana".

" ohh Hajiya wai?"
Mai gadi ya sake tambaya yana kallon sa.

Sani ma sai yace
"Koma wacece ni, tambaya nayi kawai ta fito ne?"

"Ah ah bata fito ba tukunna".
Cewar Bala maigadi tare da kawar da kansa .

Ajiyan zuciya Sani ya sau'ke tare da fa'din " yauwa barka".
Sannan ya zauna.

Sai kuma yaci gaba da fa'din " kasan ta da jaraba, yanzu sai ace nayi laifi bandawo da wuri ba, nima 'din wallahi ina ta sauri in ga nadawo da yake tun kafin na fita ta sanar dani 'karfe goma zata fita makaranta, to kuma sai na 'dan samu matsala kasan abinka da jama'ah sai a hankali....."

Hannu ya kai cikin aljihun sa domin ciro wayar tasa yayin da mai gadi ke binsa kawai da idanu.

Sani cigaba yayi da fa'din " waya na je na sauya amma nake gaya ma da 'kyar na dace da wannan, akwai dayawa amma basuyi min ba".

Maigadi bai kar6i wayar a hannun sa ba cewa kawai yayi" ba laifi ai dan gata bata wani sha jiki ba kuwa...Allah ya sanya alkhairi".

Da " Ameen" Sani ya amsa tare da maida wayar cikin aljihun sa sannan ya mi'ke tsaye, ha'di da fa'din " bari in kama ruwa ina zuwa, idan ta fito da Allah kayi min magana, in kuma bata fito ba to zan 'dan tsaya watsa ruwa ".

" Sai ka fito to".
Cewar mai gadi tare da komawa ya kishingi'da kamar yadda yake tun farko.

Shiru-shiru har sha 'daya Sani bai ga Noor ta fito ba, har yayi wankan ya fito ya sake zama da maigadi amma shiru.

'Dan 'karamin tsaki yaja tare da mi'kewa tsaye yace " bari kaga in yiwa matar nan magana tun 'dazu naga shiru, kaga in bazata ba nima in hutawa raina".

Yayi maganar yana me cigaba da tafiya ya tunkari cikin gidan.

Sallama yayi daga bakin 'kofar parlourn tare da turawa ya shiga, sai yaga babu kowa, sallama ya dinga dokawa kusan sau hu'du amma shiru.

Noor na daga ciki duk ta gama hautsina ko'ina garin shirye-shiryen kayan su ita da Jas, tana jiyo sallamar Sani amma bata jin zata iya amsawa sai ma wani 'karin takaicin da taji ya sake kama ta musamman data ji sallamar tasa ta'ki 'karewa.

A 'dan zuciye ta ture takardun dake gaban ta ta taso ta nufo parlourn kamar wata jaruma, tana isowa parlourn sai taga Sanin ya juya yana 'ko'karin fita ga dukkan alamu gajiya yayi da jero sallamar ne.

A dake tace " Sani!.
Ciki-ciki tayi maganar amma hakan bai hana Sani jin muryar ta ba.

Sai ya juyo kafin yayi magana sai ta riga shi da fa'din" ya akayi?"

Ta sake tambayar sa fuskar ta ko alamun fara'a babu, daman ma yaya asali ba fara'a take yiwa Sani ba ballantana yanzu da take jin ranta yake 'kololuwar bace.

Shi kansa Sani da yaga yanayin fuskar ta sai da yagane cewa ba a dai-dai take ba.

Bu'dan baki yayi yayi yace....
" Hajiya naga baki fito bane har yanzu, kuma naji 'dazu kince 'karfe goma zaki shiga makaranta shiyasa nazo in tuna miki".

"Karfe nawa yanzun?"
itama ta sake tambayar shi.

Sai yace " Sha 'daya fa har ta gota Hajiya".

Kauda kai tayi gefe tare da fa'din
" Ni 'din bazani ba, amma please ka hanzar ta zuwa 'dauko min 'yata zamuyi tafiya ne".
Tayi maganar cikin 'karfin hali sosai wai dan kar ya fahimci halin da take ciki.

Da " to" kawai Sani ya amsata tare da juyawa ya nufi hanyar fita.
" Ka hanzar ta dan Allah".
Ta 'kara fa'di tare da juyawa ta koma ciki.

Kamar yanda ta fa'da 'din batare da wani 6ata lokaci ba Sani ya shiga mota kai tsaye ya nufi makarantar su Jasmine da tunanin 'kila ko mutuwa akayi musu shiyasa dan yaga idanun ta sunyi ja alamar tasha kuka, kuma ma in ba haka ba bai ta6a ji ko ganin sunyi irin wannan tafiyar ba.

11:25am ya isa makarantar su Jasmine, shi kansa yaje ne a lokacin dan cika umarnin ta amma bawai dan cewa yaran sun tashi ba.

'Karamin tsaki ya saki a fili daya tuna cewa zai yi zaman jiran su a 'kalla na kusan mintina 30.

Jikin kujera ya kwantar da jikin sa tare da 'dago 'kafafun sa ya 'dora a gefen stairy, wa'kar 'yar budurwa nasu M.Shareef ya kunna ha'di da kunna A.C ya wani lumshe idanu yana saurare tare da bin bakin wa'kar a fili tsawon mintina uku.

'Karan shigowan sa'ko dayaji cikin wayar sane ya katse shi a hankali ya lalu6o wayar ya duba sai yaga ma ashe sa'kon MTN ne.

Koda ya ga sa'kon sai kuma bai maida wayar tasa cikin aljihun ba ya cigaba da duba ciki dan tunda ya siya bai ga komai a wayar ba, Sim 'din sa ka'dai ya sanya ciki.

Sa'konnin dake inbox 'dinsa mara sa anfani kaf yabi yabi ya goge su sannan ya koma cikin file manager 'din wayar.

Gani yayi kan wayar da akwai abubuwa da 'dan dama da ba'ayi clearing ba kafin a siyar da wayar, kama daga kan videos har photuna da kuma wa'ko'kin audios ka'dan.
A fili ya furta " sai kace ba a shirya saida wayar ba.....mthew"
ya 'karashe da jan tsaki.

Duba wa ya rin'ka yi yana goge abubuwan da basuyi masa ba yana kuma barin na bari.

Cikin haka har ya iso wani folder dake 'dauke da videos guda uku, bai yi wata-wata ba kawai ya shiga ya bu'de, ai sai yaga ashe porn videos ne duka ukun a jere.

Batare da wani tunani ba ya dinga bi yana kallon su 'daya bayan 'daya, in ya gama sai ya sake maimaitawa, abin babu kyan gani amma Sani kam sosai suka 'dauki hankalin sa harma bai san cewa lokaci yaja sosai ba domin ba k'aramin shagala yayi da kallon ba.
Chapter 16 · 0% Book details