← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 211

Sashe 53

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya mi'ke ya kama hanyar fita daga 'dakin, yana share hawaye da takaicin duk shine sanadin auren ta,  bai ma san mai ya kaishi shiga rayuwar Mu'een a wancen lokacin ba da har abubuwan da suka faru suka faru, haka kawai ya tsinci kansa da tsanar Mu'een batare da wani dalili ba a wancan lokacin, yasan kuwa hakan ba komai bane face sharrin shai'dan, sai gashi ta inda Mu'een ya biyo masa, ta inda zuciyar sa bazata iya 'dauka ba....sam baiso ayi auran Rahma tun yanzu ba yaso ace tafara karatun gaba da secondary, yaso ta fita daban agidan nasu amma duk shirin sa ya watse cikin 'kan'kanin lokaci, sai gashi da kansa ya jagoranci aurar da Rahma tun kafin ta kammala secondary 'din ma, tun kafin hankalin ta ya gama daidaita balle ta kai wani matsayi na musamman.

Daf da zai 'karasa barin 'dakin yajiyo muryar Rahma cikin sanyi ta 'kira sunan shi....cak ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta, tana hawaye shima haka, tsaye ta mi'ke  sannan cikin sanyib murya tace dashi " nayi al'kawarin yiwa mijina biyayya, insha Allahu bazan tozarta maka niyyar ka ba Yayah, zan kula da duk abinda ya kasance hakkine ta 6angare na, nayi maka al'kawarin mantawa da Mu'een mantuwa ta har abada...amma yayah please kace da Amin kar ya hanani 'karasa karatuna inaso in gama yaya......"
Ta 'karashe maganar da sheshshe'ka.

Hayatu kam take ya cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa, har ma bai san lokacin da ya iso gaban ta ba ya fara share mata hawayen ta.

Bai furta komai ba kawai ya janyo hannun ta a hankali suka fita daga 'dakin, direct 'dakin mahaifin su ya kaita, dukkan su kuka sukeyi yayin da mahaifin nasu ya tsura musu idanu yana kallon su.
Hayatu ne ya fara magana da muryar kuka yace
" Daddy ka yafe min dan Allah, idan abinda nayi ba'a son ranka bane, bansani ba ko dai-dai na aikata Daddy, yau gashi zan dam'ka Rahma a hannun mijin ta zata tafi ta bar mu, Daddy ko cikin ranka ne ka daure ka sanya mata albarka...."

Ido Daddyn nasu ya lumshe ya kuma bu'desu nan take hannun sa da suka kama ya dam'ke da 'karfi ga dukkan alamu magana yake son yi amma babu dama....wanda hakan sai ya 'kara 'karya zuciyar Rahma take ta sake sakin wani sabon Kuka....cikin kukan take fa'din " Allah ya baka lafiya Daddy, ubangiji Allah ya tashi kafa'dun ka...."

Anan 'dakin sauran 'kannen mahaifin nasu suka suka tarar dasu, harda kaka.

Nasiha suka sake yi mata inda ta ringa kuka sosai duk kwalliyar da Antyn ta tasa akayi mata duk sun wanku babu su tas, ba'a kuma 'kara bi takai ba kawai aka sake yi mata shiri, kukan da takeyi bai bari an sake yimata kwalliya ba a hakan aka 'dauke ta aka tattara a'kalar rayuwar ta aka dam'kawa Amin inda ya kar6eta da hannu bibbiyu cikin farin ciki.

〰〰〰
Zaune suke dukkan su a dinning Ammi na shirin serving musu abinci kamar kullum sai Mu'een yayi 'yar dariya ka'dan.....Alhaji Baba ne ya kalle shi duba irin na tambaya domin a yanda ya lura 'yan kwanakin kullum cikin farin ciki yake.
   Yayin da ya gumtse dariyar tasa yana kallon Ammi yace " Ga dukkan alamu fa Ammi kin samu kan wainar nan, to danni kike yi ne ko kuwa dama kullum haka akeyi agidan..."

Ammi bata fasa zuba abincin da take yi ba ba kuma ta kalle shi ba kawai tace
" Tambaya kakeyi ne ko.kuwa neman sani? "
" Duka biyu Ammi ni duk inason sani, haka kawai kullum baza muji 'kamshin suya ba sai da muga waina...kamar fa sau 'daya ne kawai akayi fashin yin waina agidan nan tun zuwa na?"
Ammi ce ta sake fa'din
" To laifi ne hakan kuma ko?"
" Ah ah ni ban ce laifi bane...ai wainar taki tana shiga sosai Ammi har Allah Allah fa nake gari ya waye in gamu dashi dan nasan babu fashi".
Alhaji Baba kam shiru yayi kawai yana ji da ganin su yana murmushi.
Ammi ce tace
" kai de kasani..."
Dai-dai lokacin da take zubawa 'yan biyun nasu abincin...
'Dagowa tayi ta kalle shi sannan ta 'kara da fadin " in ba yaudaran kai ba yaushe ka ta6a ganin na soya waina a gidan nan......ni ba ni keyi ba siyowa akeyi har kunun ma gaba 'daya".
Ammi ta fa'di lokacin da take 'ko'karin jan kujera ta zauna bayan tagama zuzzuba musu.

Ido Mu'een ya zaro da mamaki yace" siya kuma Ammi....har daga ina haka?"

" Can wani gida mana kana tambaya ta kamar wanda idan na fa'da mai gidan zai sani...."

Alhaji Baba ne ya tari maganar da fa'din " gidan abokina akeyi " M. Jaji wanda ranar ka gansa a gidan gona.."

Baki ya ta6e ha'di da fa'din ni banganeshi ba wallahi".

" Amma ai kasan yarinyan nan Hudah da kullun take zuwa gidan nan da safe ko..?"

Kai ya 'daga a hankali yana kallon Alhajin da tunanin dama ya rasa dalilin da ke kawota gidan kullum safiya......Alhaji Baba sai yace masa " to mahaifiyar ta ke yi kuma ita ke kawowa, idan kanaso sosai sai adinga kawowa da yawa".

"...Haba Ammi dan Allah... yanzu dama ba ke keyi ba shine kuma ba'a ta6a gaya min ba?"

" Ai kaji yau kam".
Ammi ta bashi amsa cikin halin ko in kula.

Shiru yayi bai sake magana ba haka kuma bai kai komai bakin sa ba har kowa ya gama ya tashi a table 'din ya rage saura shi ka'dai da Ammi...shima kansa kuwa bai san me ya hana shi barin table din ba.
Ammi ce ta dube shi tace
" Idan baka son wainar ga Tea da bread ka ha'da barin soya ma 'kwai yanzu sai ka ha'da ka ci?".

Kai ya girgiza mata alamar "a'a" " to me zaka ci?"
" ba komai" ya bata amsa a takaice.

Ammi 'kyale shi tayi ta mi'ke ta tafi kitchen dan soya masa 'kwan...amma ga mamakin ta kafin ta fito daga kitchen 'din yayi tafiyar sa domin koda ta dawo bata same shi ba a inda ta barshi......har 'dakin sa ta duba bata same shi ba, shi wai a dole fishi yayi sosai harda barin gidan.

Bai dawo gidan ba kuwa sai 'karfe uku sannan yazo nan ma da 'kyar Ammi ta sashi agaba kafin ya ci abinci ka'dan.

Cikin ranta tace " silly boy....bacin ya gama santin kunu da waina abaya kuma yanzu zaimin iyayi... mthew" ta 'karashe da jan tsaki duk cikin zuciyar ta.

A fili kuwa nan nan ta ringa yi dashi dan bata son mutun ya rin'ka zama da yunwa.

*****
     Bayan kwanaki uku.....ban fasa zuwa gidan ba kamar yadda ban daina kawo waina da kunu ba....na kanzo kamar yanda na saba muyi wasan mu da su Saif in koma gida abina....amma har ib tafi wani lokacin bana ganin sa.

Ban sani ba yanzun ashe Deen ya daina zuwa dinning da sassafen nan tunda ya ji cewa ba wainar Ammin sa yake ci ba...yanzu ko ya dawo daga gudun safen sa ma 'dakin sa yake shigewa abinsa sai kusan 10 yake fitowa yasha ruwan tea.....duk yanda yaso ya daure amma ya kasa ya riga ya saba da 'dan'danon waina da kunun nan.

Sati guda yana a haka duk 'ko'karin da yake yi wajen sharewa amma ya kasa watarana da sassafe yayi tsaye akan Ammi wai dole sai tayi masa kunun gya'da da kanta...." kajira anjima ka'dan za'a kawo sai ka sha".
Ammi ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

'Bata rai yayi yace "  ni Ammi naki nake so dan Allah".
....kallon sa tayi da mamaki tace " haba Mu'een....ka ta6a ganin nayi kunun gya'da da hannuna ne a gidan nan fisabilillahi?"
" to shikenan kiyi min waina abar kunun".
" Ni duk ban iya ba"
Ta fa'di da 'kosawa...
Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din  " in zaka saki ranka ma gara ka saki ranka dan ni babu abinda na iya...ubanka ma ai yana cin wancan 'din balle kai".
Ta 'karashe da masifa...

   Tamkar zai yi kuka haka ya juya ya bar mata kitchen 'din, gaba 'daya ma sai yaji garin ya fita ransa, Antyn sa Zainab ce ta fa'do ransa dan yasan ita duk ta iya su tunda lokaci-lokaci takan yi musu idan ta ga dama, sai dai wancen da yake ci 'din ko kama 'kafar wannan bai yi ba a da'di...amma dai duk da haka a yanda yake jin son waina da kunun yasan idan ya sami na Antyn ba zai 'ki ba.

    Abu 'daya ke taka masa birki shine son yarinyar nan baya so ya tafi ya daina ganin ta domin a duk ranar da ta kasance ganin ta yayi masa wahala to kuwa shima wahala yake sha da zuciyar sa, wani irin so yake yiwa yarinyar mai wuyan fassaruwa.
    Bai ta6a tunanin a wannan shekarun nasa zai yi sha'awar yin aure ba har sai da ya kamu da son Nannen mu, 22yrs yake amma yana jin da Uncle Ja'afar zai yadda masa da auren ta zaiyi ya killace ta a gidan sa shi ka'dai ya ringa kallon ta.

     'Karfi da yaji yayiwa kansa katanga da wainar mu, duk kuwa da cewa yana tsananin son ta amma haka ya daure ya cireta cikin ransa.

Satin sa shida a Shuwarin Uncle Ja'afar ya 'kirashi ya sanar da shi batun computer certificate 'din zai fara, afa'dar Uncle Ja'afar in so samu ne nan da kwana uku ya dawo yayi registration.

   Mu'een yaji da'din wannan labarin sosai domin kuwa zama haka a gidan ya ishe shi sai dai gefe daya yana jin tamkar zai bar 6arin zuciyar sa....tun daga ranar ya fara shirin tafiyar sa sai dai rashin natsuwa da ya ziyar ce shi zuciyar sa tun yanzu har ya fara kewar Nanne.

     Ana gobe zai tafi a lambu ya yini wurin Alhaji Baba, suna zama suyi hira sosai da Mal. Jaji amma bai ta6a sanin cewa shine mahaifin Nanne ba....to ko ranar ma tare suka wuni dashi yana bashi labarin irin yadda suke samun cigaba a duk lokacin da aka fitar da kayan lambu ko kaji dake gidan gonar.
Chapter 53 · 0% Book details