← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 211

Sashe 123

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
   Washe gari da yamma aka zo aka tafi dani gidan Ammi..bayan an min kwalliya ta na gani a bada labari...ko kafin atafi da ni sai da aka ha'da ni da Baban mu awaya ya sake kwantar min da hankali gami da nasihar ha'kuri da kuma kawar da kai...duk wannan abin bai sa na sake zubda hawaye na ba...har sai da mukaje gidan Ammi aka ha'da ni da Yah Deen wuri guda lokacin bayan sallar Isha'i ne, Alhaji Baba da kansa ya zauna yayi mana Nasiha mai shiga jiki tun anan nafara kuka na harda shashshe'ka cus yanzu na fahimci kowa nasihar zama da Yah Deen yake min...kenan dagaske daga yau zama tare da shi zan koma yi...kamar yadda Saif ma ya fa'di.

Ammi ce ta fitar dani rungume ajikin ta bayan Alhaji Baba ya sallame mu sai ta wuce dani 'dakin ta muka bar Yah Deen ka'dai da Alhaji Baba, bansan me suka tattauna tsakanin su ba amma sun shafe a'kalla kusan mintina ashirin suna tare da shi.

Nima 'din Ammi lallashi na take yi a 'dakin ta tana sake lalla6ani yayinvda nake mata shagwa6ar ni bana son zama da shi tace kar akaini gidan sa...Ammi kam lalla6ani ta ringa yi da kalamai masu da'di har na rage kukan da nake yi, cikin hakan tasa na 'daukan mata al'kawarin duk abinda yamin wanda banji da'din sa ba ko kuma na cutarwa bazan 6oye mata ba...tace in kwantar da hankali na insha Allahu bazata ta6a bari ya cutar da ni ba matu'kar numfashin ta na aiki...ni dai kawai in masa biyayya matsayin sa na miji na kar na raina shi...saboda shine tsanin aljannah ta daga yanzu....tace aure na dashi ya riga ya zama rubutaccen 'kaddara ne baya ga da ko ita da kanta bazata ta6a bari hakan ta kasance ba...sai dai yanzu kam babu yadda zatayi tunda ba'a jayayya da yin ubangiji kuma shi yasan dalilin faruwar komai...tace min idan na kwantar da hankali na na zauna dakanta zata sa ya siya min waya mai kyau wanda zan na 'kiranta kullum muna gaisawa.."

Jin hakan da ta fa'di ne ma ya 'dan sanyayar min da hankali na har na kwantar da kaina kan cinyar ta ina maida numfashi yayin da ta ringa shafa min kaina tana sake lalla6a ni.

" Ammi" na 'kira sunan ta a hankali.
Sai ta amsani tare da bada hankalin ta gare ni..
Nace " Banga su Saif ba Ammi.."
Tace
" Kar ki damu zaki gansu ai uwata har gidan ki zasu je su gaida ki kinji?"

" To"..nace 'kasan ma'koshi na ina sake tunanin rabuwar mu da Saif ta jiya.

'Karfe tara da 'yan mintina aka tafi dani gidan Yah Deen da sunan gidan aure na, bansan me yasa ba amma sai na kasa tsaida hawaye na...sanda za'a shigar dani gidan kuwa fargaba ce ta shige ni mai tsanani musamman saboda sanin halin sa da nayi hakan yasa kuka na ya tsananta.

Gashi babu wanda zai kwana tare dani dan haka koda suka kawo nin ma basu zauna ba shiga suka yi suka lalle'ka cikin gidan sannan daga bisani suka dawo nan kuma suka fara niyyar tafiya, nan kuka kuwa naji hankali na ya tashi sosai...tunanina ta yanda zan iya zama tare da shi a gida 'daya.

Addah ta Maryam na rungume ina ro'kon ta kar ta tafi ta barni tsoro nake ji..haka ta dinga yimin nasiha tana sake tuna min kalaman Baban mu da Ummah ta...still ban sake ta ba na cigaba da kuka na..wayo tamin tace in bari ta tafi tunda dare yayi yanzu amma gobe insha Allahu da sassafe zata dawo mu yini.
Nace mata ni tsoro nake ji ni ka'dai dan Allah kar ta barni..sai tace min to bari ta dubo Mu'een idan baya nan sai ta kulle 'kofa ta dawo...da jin haka sai na sake ta ina share hawaye na.

Daga haka ban kuma jin motsin ta ba.

Allah ma ta taimake ni dan tamkar ha'din baki da fitar su basu jima ba sai ga shi shima ya shigo gidan da farko ma da naji motsin 'kofa nayi tunanin ko Addah Maryam 'din ce..but jin sallamar sa da nayi wanda yayi ta daga bakin parlour 'kasa-'kasa tamkar ma bazaiyi ba hakan ne ya sani fahimtar shine.

Ai kuwa ban ko amsa ba na cigaba da kuka na..sai ma ganin san ya sake tada tsimin kukan nawa na fara yi tamkar an doke ni ne.

'Karamin tsaki yaja da jin irin kukan da nake yi...ko kulani bai yi ba balle in saka ran ya san da zama na, abin hannun sa ya ajiye kan center table dake tsakiyar parlourn daga haka ya sa kai ya wucewar sa ciki.

Tsawon mintina kusan biyar sannan na sake jin muryar sa daga baya na a tsawace yace " Ki min shiru...".

Yi nayi kamar banji ba na cigaba da kuka na ina share hawaye...'dan takowa yayi ka'dan yana sake ha'de fuska yace " Wallahi 6allaki zanyi idan kika dame ni banson hauka ni".

Ji da ganin hakan ne yasani saurin mi'kewa tsaye ina yarfa hannuwa na cikin kukan nake fa'din" Ni dai Ammi na.."
Tsakani na da Allah nake bu'katar komawa wurin Ammi har zuciya ta...yaushe zan zauna da mutumin da ko dariyar kirki ma zan iya irga sau nawa naga yayi ta tsawon zama na a gidan su..kwatsam kawai ace yau gani ga shi matsayin ma'aurata.
Da wani tsawan naji ya sake fa'din
" Dan ubanki na 'daure ki ne ko ni ne na kawo ki gidan da zaki dame ni?"

Dalili guda biyu kacal ne suka hana ni nufan hanyan fita saboda nasan already ya rufe 'kofar bayan da ya shigo, sannan kuma nasan a lokacin dare yayi, wa'dannan dalilan ne suka sanya ni cigaba da rera kuka na kawai batare da na nufi hanyar waje ba.

Tsaki yaja sannan ya sake komawa ciki...da shigar shi sai ya rage kayan jikin sa cikin hanzari dan duk ji yayi ransa ya 6aci, bayi ya shiga sai dai bai jima ba ya sake fitowa.

Da yake lokacin da za'a kawo kaya na kaf aka fitar da kayan sa a gidan aka kai gidan Alhaji Baba  so bashi da ko da kayan bacci ne yanzu anan dan haka kawai sai ya zauna da boxern dake jikin sa da nufin bacci da shi.

A hakan kuma ya dawo parlour inda nake da yake ya saba da zama hakan tun asali.

'Bangare na kuwa a lokacin na daina kuka sai dai ajiyan numfashi zaune nake kan gwiwoyina nake a 'kasan parlour sai faman murzan idanu kawai nake yi...a haka naga ya fito ya nufo inda nake.

Da ganin sa hakan sai nayi 'kasa da kaina tare da  saurin rintse idanu na cuz ni baya ga shi ban ta6a ganin wani namiji cikin irin wannan yanayin ba...cikin raina nake mitar halin sa.

Yanda zuciya ta ke harbawa ya sanya nake jin wani sabon tsoron sa na sake kamani da ban na menene ba...daga nesa dani ka'dan ya zauna yana sake ha'de ransa cikin ba'kin hali ya ce..." Kin yi sallah ne?" Da sauri na 'dage masa kaina alamar " Erh" ...sai yace " Abinci fa?"
Nace " Naci" Still idanu na a rufe.

" To maza ki tashi ki je ki kwanta banson sake jin wata rigima kuma in ba haka ba zane ki zanyi...".

Daga fa'din hakan ya tashi ya koma ciki ya bar ni zaune a wurin kamar yadda ya samo ni.

Sai da na tabbatar ya fita sannan na bu'de idanu na ina sake kallon inda ya tashi.

Baki na ta6e na kawar da kaina gefe...na 'dauki a'kalla kimanin mintina sha uku kafin na mi'ke na cire mayafi da 'dan kwalin kaina nayi kwanciya ta kan doguwar kujera

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *60*

Baki na ta6e na na kawar da kaina gefe....na 'dauki a 'kalla kimanin kusan mintina sha uku kafin na mi'ke, mayafi da 'dankwalin da ke kaina na cire daga nan nayi kwanciya ta kan doguwar kujera.

Take kuwa bacci yayi awon gaba da ni....Yah Deen ma bai sake bi ta kaina ba har sai da gari ya waye bayan ya 'dauro alwala sannan yazo ya tashe ni inda ya bubbuba 'kafafuna yana fa'din" Ke..."
Firgigi na tashi na zauna ina ha'de raina cuz ni ban saba da irin wannan tashin ba..Ammi na ba haka take tashi na daga bacci ba.

Tuno cewa wai yanzu da shi zan zauna a gidan ya sani na sake jin wani iri har cikin zuciya ta..bansan ranar da zan saba da Yah Deen ba ni.kam a rayuwa ta.
" Ta shi kije kiyi sallah?"
Abinda kawai yace dani kenan sannan ya juya ya koma ciki.

Ko motsawa ban yi ba daga inda ya bar ni har ya idar da tasa sallar ya kuma fitowa ina nan na takure wuri guda tamkar almajira abin a tausaya min.

Ga shi fitsari nake ji sosai kuma na kasa zuwa inyi saboda fargaba...tamkar daga sama naji muryar sa akaina yana sake fa'din" Har kinyi sallar ne?"
Saurin girgiza kaina nayi ina sake matse fitsarin da ke damuna.
" Lokacin kuma jiran ki yake yi ko?.."
Ya sake fa'da daga inda yake tsaye.

Ban san me zan ce da shi ba dan haka sai na 'dan waigo ka'dan na kalle shi, tsaye yake ya ri'ke labile a hannun sa daga bakin 'kofar shiga cikin, fuskar sa ba yabo ba fallasa amma ban wani tsaya na 'kare  masa kallo ba na kawar da kaina cikin raina nake 'kun'kunin" ta ina zan wuce to bayan ka tare hanyar"..

Tsaye na mi'ke hannu na ri'ke da shirgin kaya na mayafi da 'dan kwali na...shahada kawai nayi  na nufi bakin 'kofan bedroom 'din cikin sanyin jiki kaina a 'kasa...nasan duk tsiya ai idan anzo zai matsa in shiga.
Chapter 123 · 0% Book details