Sashe 138
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Wai sai yaushe?"
" Ba rana dai inajin?"
" Kuma uban wa zai je mata makarantar?"
Ya fa'di a hassale.
Zaro idanu Anty Zainab tayi sannan tace
" 'Kaniyar ka Mu'een da ni fa kake magana.."
'Dan sosa kansa yayi yana fa'din
" Sorry Anty...amma please kice mata ta dawo ko dan saboda makarantar ma".
" Kai me ze hana ka gaya mata da kanka?"
" Ok Anty zan gaya mata.."
Daga haka suka yi sallama da shi.
Ammi ya 'kira itama yayi mata maganar tace da shi ba yanzu zan dawo ba.
Ai kuwa sosai ransa ya 6aci da jin amsar da Ammi ta bashi.
Shi laifin ma ba nawa ka'dai yake gani ba har da na sauran saboda ai kowa yasan an yi resuming school, tunda kuwa sun san zan 'dau lokaci to dan me yasa za'a barni na tafi kuma? Kuma tsabar na raina shi ma yace da ni 1 week shine na yi banza da zancen sa nayi zama na...haushi na da yaji cikin zuciyar sa hatta su Ammi basu tsira ba, bai sani ba ashe ni ban sanar da kowa batun 1 week 'din da yace min ba.
Ko da Ammi ta 'kira ni tambaya ta tayi cewa wai dama bama waya da Mu'een ne?"
Sai nace da ita" a a Ammi muna yi fa kwana biyun nan ne kawai be 'kirani ba".
" Me yasa to?"
Ta tambaye ni sai nace nima bansani ba Ammi ni dai kawai be 'kira ni ba".
" 'Kyale shi..na san wataran ko ance yayi miki hakan ma da kansa zai ce a a..."
Cewar Ammi kenan cike da jin haushi sai nayi 'yar dariya kawai musamman tuno cewa ko Anty Zainab ma irin abinda take yawan fa'da min kenan...takan ce da ni _watarana da kansa zai godewa wanda ya ha'da auren mu da shi, tace raina 'yar Ammin nan yayi ni kuma nasan bakowa ke sa'an samun irin ta ba..._ "
Anty Zainab kan yawan fa'da min haka ne musamman saboda ta kwantar min da hankali na...kuma har raina nake jin maganganun ta idan tana yi min shiyasa nake jin da'din mu'amala da ita.
Duk da nasan ni ba komai bace, kuma mawuyacin abu ne abinda Anty ke fa'da ya faru ni agani na amma duk da haka nakan ji da'di idan ta fa'di hakan har cikin raina.
Ko yanda muka yi kan batun tafiyar ma dana gaya mata cewa 1 week wai yace zanyi dariya kawai tayi tace rabu da shi ki huta abinki...Bai san cewa ke matar sa bace sai wurin bada umarni ka'dai sannan yasan da haka..."
Ban kai 'karshen tunanin ba na tsinkayi muryar Ammi na fa'din" Amma yaushe kika shirya dawowa ne?" Ammi ta tambaye ni.
Wanda da jin hakan take sai na 'dan shagwa6e murya ta sannan na bata amsa da fa'din" Ammi ni fa gaskiya ba yanzu zan dawo ba garin akwai da'di wallahi".
Murmushi Ammi tayi tace" Nasani Mama na...amma ai kinga karatu na ta wuce ki a school ya kamata ki zama a kusa, ko shi ma Mu'een 'din complaint 'din da yayi 'dazu kenan".
Sake shagwa6ewa nayi nace" Ni dai dan Allah ba yanzu zan dawo ba Ammi..."
" Sai yaushe kenan?"
"May be nextweek".
" Kai Mama na har da may be kuma?"
'Yar dariya nayi ka'dan tare da fa'din" To nextweek zan dawo Ammi na".
Murmushi tayi daga 'dayan 6angaren sannan tace
" Shikenan to Allah ya kaimu...amma ki gaya masa fa dan kar ya ishe ni da mita kinji".
Da" to" kawai na amsa ta ba wai dan zan sanar da shi 'din dagaske ba.
Haka na cigaba da zama na gidan Addah Maryam hankali kwance batare da damuwar komai ba, ban damu sam da lamarin sa ba, ni lokuta da dama ma in ba zancen sa akayi min ba sam ban tunawa da shi.
Har gara ma in Addah Maryam ta sani gaba da darussan ta na kan zurfafa tunani akan sa cikin raina na kance Addah kenan, ita har yanzu bata san waye Yah Deen ba.
Na kan yawaita fa'din hakan ne idan naji tana ikirarin wai maza ba komai suke ba wajen matayen su matu'kar mace ta san kanta to namiji bai isa ya raina ta ba balle wani abu makamancin tsawa ya shiga tsakanin su..."
Har dariya take bani idan ta fa'di hakan, domin.ni ban hango faruwar hakan ga nawa mijin.ba sam, gani nake ba ranar faruwar hakan.
Tambaya nake jefa mata da fa'din" Addah kuma har da Yah Deen shima?"
Kwafa Addah Maryam take yi sannan ta bani amsa tace" hadda shi mana shi 'din ba namiji ba ne...wallahi in kika tsaya lusaranci haka har abada zaku cigaba da rayuwa bazai ta6a baki kima ba balle ya daraji ki, amma idan kika tsaya kika nuna masa ai kema mace ce mai aji da kanki sai kinyi mamakin biyayyar da zai miki".
Yawancin idan irin wanna n maganar ta zaunar da mu to da dariya muke tashi awurin domin ni kam gani nake Addah Maryam son ranta kawai take fa'di bakomai ba.
*****
Ko bayan yin wayar mu da Ammi ban 'kira shin ba kamar yanda ta fa'da, haka kawai ni sai banji son 'kiran nashin ba har cikin zuciya ta, balle ma da na samu Anty Zee na 'kara 'dora ni akan wai in cigaba da share shi, tace yanda ya raina ajina 'din nan idan ina shishshige masa watarana abinda zai min har sai ya girmi tunani na.
Shawarwari da maganganu da yawa nake ji game da shi daga mabanbantan baku na wa'danda kuma duk nake da tabbacin baza su cutar da ni ba.
Nasani kowa yana bani shawarar ne bisa la'akari da halayen sa amma bansan meyasa ba haka kawai duk sai nafi jin na Anty Zainab yafi kwanta min a raina saboda nata babu tsanani a ciki, babu abinda zai gagareni aikatawa domin bata sani yin abinda ban da ra'ayin sa.
Addah ta kuwa a kullum ilimin zaman aure gaba 'dayan sa take 'ko'karin ganin ta koya min, na kan zauna in saurare ta tas wasu lokutan ma har kunya maganganun ta ke bani musamman idan ta fara canza 6nagare wannan kam bana yi mata musu ko jayayya ko nuna 'kin amincewa ta shiru nake in saurare ta, amma har cikin raina gani nake babu ranar da irin hakan zai faru da ni.
Duk 'ko'karin Addah ta bai wuce nuna min hanyoyin da zanbi in ja hankalin miji na ba..musamman da yake kowa yasan halin sa, kowa yasan cewa shi 'din manemin mata ne, duk da bata fito fili ko sau 'daya ta furta hakan.ba amma a yadda take karkata zantukanta da kaina fahimci kallon da ake yi masa, wanda ni kaina ma shaida ce ta gani da ido akan halayayr sa..'kilan dalilin kenan da yasa take 'ko'karin wayar min da kai ta 6angaren zamankewar aure.
Ban 'kira Yah Deen ba haka shima bai 'kira ni ba har na cika kwana goma sha 'daya a Darazau, sai a ranar ne ma da 'karfe tara saura na dare naga waya ta na haske, da yake silent take shiyasa bata yi 'kara ba, kwance muke na gama shirin bacci na, duk ma yaran Addah ta sunyi bacci saura ni ka'dai na rage ni 'din ma bacci ne cike a idanu na hasken da wayar ta fara ne yasa na 'dan bu'de idanu na lalu6o ta.
'Dago wayar nayi batare da na ko duba ko waye me 'kiran ba na sada wayar da kunnuwa na tare da fa'din" Hello".
cikin muryar bacci.
" Shiru naji ba'a amsa ni ba, sai na sake fa'din" Hello!!
Ina ha'de raina jin ba'a amsa ni da farkon ba.
" Kin dawo ne?"
Abinda naji ya tambaya kenan da ya sani saurin gwalo idanu na, ciro wayar nayi daga kunne na na sake dubawa tamkar wanda aka ce min zan ga photon sa a ciki.
Maida wayar nayi jikin kunnen nawa sannan da rawar murya nace" Na'am...Yayah..." Tuni baccin nawa ya kama gaban sa.
" Nace kin dawo ne?"
Ya saki fa'di a 'dan tsawace.
Sai na girgiza kaina tamkar ina gaban sa kafin na 'kara da fa'din" a a".
Sai yace
" Saboda kin raina ni ko?"
Nayi saurin bashi amsa da" a a".
" Yaushe nace ki dawo dama?".
Shiru ina 'kif-'kif da idanu na'ki yin magana.
" Wallahi 2days kika yadda kika 'kara a wancen garin zaki ha'du da ni, in ba hauka ba baki san ana zuwa school bane da zaki je kiyi zaman ki a can 'din?"
" Na sani.."
" Owk u just want to proof ur mentality ne ko?"
" um- um".
" Ki yi yadda kika ga dama amma wallahi if kika kuskura kika tsallake ranar dana gaya miki ke da kanki kin san sauran..."
Yana shirin datse wayar sai kuma ya dakata yace" da zaran kin koma ki gida ki sanar da ni kinji ko baki ji ba?...".
" Naji?"
Nace ina tura baki na sai yace
" Aha"
Daga haka ya yanke 'kiran...jiki na duk sai naji wani iri a lokacin, sakamakon rasa tunanin da ya kamata inyi ne ya sanya ni mitar " Ni me ruwan ka da ni to.."
Tun lokacin nayi niyyan sanar da Anty Zainab saboda a tunani na itan zata ce dani inyi zama na ne kar in tafi cuz ita a kullum abinda yafi kwanta min itama shi take so, amma ganin kamar dare yayi ne ya sanya ni fasa 'kiran nata na bari zuwa safiya.
Ai kuwa washegari sassafe ina idar da sallah na 'kira ta na gaya mata cewa Yah Deen ya 'kira ni jiya da dare.
Dariya Anty Zainab tayi tace" 'Dan duniya yaga dama kenan?"
'Dan ha'de raina nayi nace" Masifa fa yai min Anty".
Dariya sosai Anty tayi tace" Me kika yi masa to?".
Nace" Bakomai fa kawai wai dan ban koma ba shine ya ce wai dole in tafi gobe".
Nayi maganar kamar zanyi kuka.