Sashe 147
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ta gaji da yanayin Miman a zuciye sai tace da ita" Wai ke ka'dai akace miki kika ji haushin abin ne? Ko kuwa son ta kika fi kowa aaka gaya miki? Bana son iskanci idan zaki dame ni anan maza ki shirya ki koma gidan ki na yafe miki zuwan, ai ma munyi sallaman ko..to maza ki tashi tafi gidan ki kije can ki kai 6acin ranki can kin ishe ni".
Mimah sai cewa tayi" Wallahi abin ne da haushi wallahi Anty bazaki gane bane, ji bi 'yar yarinyar nan dan Allah amma ace tun yanzu har an fara raba mata hankali fisabilillahi".
A zafafe Anty Fiddausi ta nuna ta da yatsa tana fa'din" Zanci mutuncin ki anan Mimah idan baki min shiru ba, baki da hankali ne?"
Matsawa tayi nesa ka'dan sannan ta cigaba da fa'din" A a fa Anty ki barni in fa'di abinda yake cikin raina, wallahi abin ne da haushi sosai, yarinya tana ganin mutuncin mu kuma ace ga abinda ya fito ta 6angaren mu ai babu da'di, kuma in ba abin Anty Yusrah bama ina zata je da irin wannan rayuwar?....
Sunan Yusrah ka'dai da naji Mimah ta ambata sai da zuciya ta ta tsinke.
Yayin da ta cigaba da fa'din"....Da gani ma fa bai wuci sa'an ta ba wallahi, amma tsabar duniyanci tabi ta nace masa bacin yana da matar sa a gida".
" Ce miki akayi ita ta nace masa ne..ka fa fita ido na Mimah".
" Anty ai cikin maganganun ta zaki fahimta, koma dai shiyace yana son ta amma ai ita ke damun sa yanzu kam, bakiji complaint 'din ta bane wani wai baya 'daga 'kiran ta idan yana gidan sa harda yi mata warning akan 'kiran sa idan yana gida, wai fa da gangan take yin 'kiran taji mai zai faru wai dan ya hanata.. shima 'din fa da alama saboda matar sa ne yake gudun 'kiran tan amma dan iskanci ta nace masa, ke bakiyi auren ba wa'danda suka yi kuma ki bi ki uzzura musu ki hana su zama da mazajen su lafiya...mtheww ni fa shiyasa tun farko jini na da nata sam bai ha'du ba wallahi, ko kunya ma bata ji wai tazo tana hirar abinda saurayi yake yi mata, fiye da haka ma ya kamata ta gani ai tunda ita bata san abinda ya dace da ita ba...duniyar ai gata nan ta ishi kowa, sa'o'in ta duk sunyi aure ita tana nan tana bin mazan wasu, amma tunda mutumiyar ki ce Anty dan Allah ki bata shawara ta barwa yarinya mijin ta in ba haka ba wallahi sai na gayawa Mummy abinda ke faruwa ba ruwa na...".
Idanu kawai Anty Fiddausi ta zuba mata haka nima har ta dasa ayan maganar sannan Anty Fiddausi ta sau'ke numfashi tare da fa'din" To naji Mimah zan bata, amma please tashi ki ban waje dan Allah kinji?"
Tashi Mimah tayi ta bar 'dakin tana fa'din" ai gaskiya ne Anty, mutune babu abinda suka iya sai biye-biyen maza ko'ina, sai sun je sun kwaso cuta kuma su cuci wacce bata ji ba bata gani ba a 'dauki hakkin ta a banza tana zaune a gida zaman bauta da biyayya...duk sai Allah ya saka musu wallahi".
" Allah ya shiryeki Mimah...Fitinanniya kawai".
Haka kawai Anty Fiddausi tace bayan fitan Mimah sannan ta dawo da kallon ta gare ni tace" Kiyi ha'kuri dan Allah Noor, Mimah duk ta hana mu hira da hayaniyar ta".
'Dan murmushi nayi murya ta har na kakkarwa nace da ita" Lah haba bakomai Anty" Na 'karashe maganar da sunkuyar da kaina na wasa da yatsun hannu na.
Jiki na duk yayi sanyi da maganganun Mimah, ina tsoron kar wannan Yusrahn ta kasance itace da ke 'kiran Yah Deen, in kuwa itace nasan labarin ya riga yasha bambam, ayanda na fahimci aka bayyana halin Yusran to kuwa babu tantama biyu ne suka ha'du dan shima 'din ba baya bane wajen iya bin mace matu'kar tayi masa...Idanu na lumshe da kaina a 'kasa cikin zuciya ta na fara jero Addu'ar" Allah ka rufa min asiri, Yah Allah kasa ba mijina bane, Yah Allah kar ka jiyar dani abinda yafi 'karfin kunnuwa na wanda na gani da idanu na ma sun ishe ni, Yah Allah ka shiryar min da miji na ka raba shi da matan banza".
Hawaye nake jin na son gangaro min amma na matse su 'karfi da yaji kan dole nake tilastawa zuciya ta kawar da tunanin ina maimaita Allah yasa ba shi 'din bane Allah yasa maganganun Mimah basu ha'da ala'ka da Yah Deen ba".
Ina wannan tunanin ne kawai, mma ni da kaina nasan yaudarar kaina kawai nake yi domin ko da bani da hankali a yanda naga Anty Fiddausi ke 'ko'karin kawar da zancen tana kakkarewa nasan akwai dalili, 'kilan bata so ne ni inji shiyasa take 'ko'karin Mimah ma ta 6oye min kamar yanda ita tayi, sai akayi rashin sa'a ita kuma Mimah da yake fushin ta a kusa yake sai ta kasa jurewa.
Anty Fiddausin kanta yau bamu wani yi dogon hira da ita ba, duk sai naga bata sakin jikin ta da ni wanda ni kaina ma a daddafe nayi yinin duk na 'kosa in koma gida.
Koda Mummy ta dawo kuwa sosai ta nuna farin ciki da zuwa na, har kyuatan turaren wuta tayi min mai shegen 'kamshi.
Mimah kam dama bata iya zaman ba ta tattara ta koma gidan saboda haushi.
Da lokacin tafiya ta tayi kuwa sai Anty Fiddausi ta 'dan bani shawarar ina 'ko'karin yiwa kaina da miji na Addu'ah saboda yanzu duniya agur6ace take".
Nace" to Anty Insha Allahu zan ringa yi".
Addu'ah kam ai ba ba'ko na bane, inda sabo ma na riga na saba bazan kuma gaji ba insha Allahu, da kaina nasan akwai ranar da Allah zai amsa min, ko ba yanzu ba wataran Allah zai amsa addu'ah ta zai kuma canza min ba'kin ciki na ya koma farin ciki insha Allahu.
Yah Deen kansa da ya ganni sai da ya tambaye ni" Lafiyar ki kuwa?"
Saboda gani na da yayi wata iri sai nace da shi lafiya ta lau".
Daga haka na maida kaina gefen titi ina kallon.hanya har muka iso gida.
Wannan abin sosai ya dame ni a zuciya gashi bani da wanda zan zauna inyi hirar da shi, sa'a ta ma 'daya yanzu ba sosai nake ganin 'kiran Yusrahn ya shigo wayar sa ba, amma duka da haka a yanayin yanda yake rayuwar sa na fahimci tare suke har yanzu.
Bani da yanda zanyi da shi saboda rayuwar shi, kuma ban isa in sa ko hana shi aikata abinda ya ga dama ba, hakan yasa kawai na cigaba da bibiyan abin cikin raina.
Wani lokacin haushin kaina sosai nake ji ganin yanda duk na damu kaina bacin abin bai shafe ni ba, amma idan na tuna ai miji na ne sai kuma inji erh ai da gaskiya ta.
Idan kinga yanda nacrame har zaki yi mamaki amma ko da wasa ban iya na yi masa magana akai ba ko kuma in nuna masa cewa na san yana tare da wata ba.
Shi kan sa ramar tawa na matu'kar 'daure masa kai amma bai san yanda zai yi da ni ba, idan tambaya ta yace zai yi yasan babu wata amsa gamsashhsiya da zai samu sanin hakan da yai yasa ya cigaba da zuba min idanu kawai.
Sanadin rashin sakewar tawa ya sanya ya fasa zuwa Shuwarin da ni da dama ya ayyana cikin ransa cewar idan zashi wannan karon tare zamu tafi..ta ina zai 'dauke ni a haka ya tunkari Ammi da ni? da kansa ya san ko wurin Alhaji Baba sai ya amsa tambayoyi, sanadin hakan yasa bai ko sanar da ni ba ya fasa abinda ya shirya.
Wasa-wasa sai da suka shafe a'kalla kusan watanni uku suka suna tare da Yusrah, sannan Allah ya taimake ni labarin ya isa kunnan Safwan bayan haka ma da kansa ya sa idanu ya fahimci irin ala'kar da ke tsakanin sun.
Sam bai ji da'di ba dan haka sai yayi saurin datseta da yake yasan asalin halayyar Yusrah ba mai kyau bane dama ta saba biye-biye.
Kuma acewar sa ma yaushe Yah Deen 'din yayi aure harda zai fara raba hankalin sa kashi-kashi, da 'kuruciyar ka ka tsaya kana gur6ata rayuwar ka Mu'een, yace yarinya 'karama da ko haihuwar fari bata yi ba shine zakayi mata kishiya a waje? kishiyar ma irin Yusrah, yace matu'kar Yah Deen bai rabu da ita ba ya 'daukan ma kansa al'kawari har Shuwarin zai je ya gayawa Alhaji Baba in yaso.sai ya san mai zai ce da shi.
Jin hakan ne ya sa Yah Deen rabuwa da Yusraj badan yaso ba, har kuma sai yaga ma wautar sa na 'daure kansa da kansa da yayi, domin kuwa Safwan shine mutun na farko da Yah Deen ya zauna ya bawa tarihin rayuwar sa kaf, har girman matsayin da nake da shi azuciyar sa sai da ya fa'da masa da dalilin hakan, a lokacin bai ta6a zaton akwai irin wannan ala'kar da zata sake ha'da sa da wata ba kwatsam sai yaga Yusrah, ya kuma ji son kasancewa da ita bisa tursawan Shai'dan y kuwa yi galaba akansa har ya leading 'din sa izuwa cimma manufar sa duk da yasan cewa Yusrahn matsayin 'kanwa take ga Safwan, ya 'kara basar da hakn ne ma lokacin da ya fahimci ba shine farkon da ta fara bada kanta ba, ga dukkan alamu ta riga ta saba da hakan.
Safwan kam da yaji asalin halin Yah Deen daga bakin sa sosai abin ya bashi mamaki alokacin, dan yasan bazai ta6a yiwa kansa sharri ba, in hakane kuwa babu 'karya koka'dan cikin kalaman sa, tun lokacin shima ya 'kara jinjina min yake kuma 'kara bani daraja har a zuciyar sa, ya kuma bashi shawaran to ya ri'ke ni da kyau da amana dan bakowa ke sa'an samun irin hakan ba, da 'kyar ka samu wacce zata iya irin hakan ma cikin mata,( ko ita Salmerhn ba iyawa zata yi ba kuwa har ga Allah..lolz Allah ma ya tsare faruwan hakan)