Sashe 185
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *84*
'Bangaren Noor kuwa tun lokacin da taga an kawo mata kayan ta jiya da dare da ku'di wai daga Alhaji Baba sai taji hankalin ta ya kasa kwanciya cuz bata san dalilin hakan ba.
Tana cikin tunani taga 'kiran Ammi ya shigo mata, take zuciyar ta ta tsinke sai ta fara tunanin ko Yah Deen ya sake ta in ne kamar yanda ta bu'kata.
Da rawar murya tayi wa Ammi sallama tare da gaida ta nan Ammi ke shaida mata sa'kon Alhaji Baba cewa ta shirya gobe da sassafe driver zai zo ya kaita Azare daga nan ta wuce Taraba gidan Anty Zainab".
Bata yi musu ba duk kuwa da cewa abin ya mata bazata amma sam baza ta iya ja da Ammi ba balle Alhaji Baba da kansa...Ammi 'karasawa tayi da bata ha'kuri gami da kwantar mata da hankali.
Murmushi tayi tace" Haba Ammi bakomai ai..".
Suna gama wayar ta yiwa Ummah bayani...Ummah kam dama tasan bakomai zata ce ba, ai kuwa kawai cewa tayi" Allah ya kaimu goben".
Daga haka shikenan bata 'kara fa'din komai ba, ita kam bata san ranar da rayuwa zai daidaita wa Noor ba, tausayin yarinyar a kullum 'kara ratsa ta yake yi, yarinya ce 'karama amma abubuwa na neman fin 'karfin shekarun ta...sau tari shiru kawai take yi ta bisu da idanu ba wai dan bazata iya sanya baki cikin maganar su ba a a..haka kawai wani bin sai taga shirun yafi mata koda kuwa abin ya ta6a zuciyar ta ne.
Kamar dai wannan, tafi so taji inda matsayar auren Noor yake amma kuma sai aka 6ullo da batun tura ta wani.garin daban, bata so hakan ba dan tasan still da aure akan Noor kuma bazata so a keta haddin Allah ba amma dayake suke da ita yanzun hakan yasa kawai tayi shiru da bakin ta.
Tun cikin daren Noor ta gama shirin ta tsaf washe gari kuwa 'karfe shida Alhaji Baba ya aiko mota aka kaita inda ta hau mota.
Batasan dalilin tafiyar ba amma cikin zuciyar ta take jin kamar ba haka kawai bane aka ce ta tafin, ko gwada 'kiran da su Safwan ke tayi mata ma ba wai ta kashe wayar ta bane a a kawai dan tana kan hanya ne shiyasa ba' a samun ta.
Bata sani ba ashe Alhaji Baba yayi gudun ha'duwar ta da Deen ne, ya sani matu'kar tana gidan Ummah toh Mu'een ba zai sha wahalar shawo kanta ba da yake yasan mata da rauni shiyasa yayi tunanin tura can in.
Tun adaren ma ya sanar da Uncle Ja'afar isowan ta da kuma garga'din kar su yadda su sanar da kowa cewa tana nan.
Alhaji da kansa ya fa'di hakan kuma Anty Zainab ma da kunnan ta taji dan haka sosai ta kame bakin ta cuz ko da wasa bazata yadda ta yiwa Alhaji kuskure bisa hukuncin sa ba.
Tana isa Taraba aka taho da ita gida dayake already Uncle Ja'afar ya tura a 'dauko ta.
Anty Zainab kam murna ta samu abokiyar hira a gidan dama ka'daici ya dame ta sosai, murnar ta kasa 6oyuwa tayi ita da kanta ta 'kira Ammi ta sanar da ita cewa Noor in ta iso.
Ammi kam cewa tayi" To dan Allah ki kula min da ita har zuwa lokacin da yaron nan zai sakar min ita, naji ma Alhaji na zancen makarantar ma 'kila acan zatayi dan Allah amanar 'yata Zainab, marainiya ce, ga kuma maraicin 'ya data ke ciki banda damuwar dake 'kunshe cikin zuciyar ta dan Allah ki bata kulawa kinji...
" Insha Allah kar ki wani damu".
"Kuma kar ki yadda Mu'een yasan cewa tana wajen ki takura ku zai yi sakin ta nake so yayi bazan kuma barin ta zama da shi ba..".
" Bazai sani ba Insha Allah ki kwanatr da hankalin ki"
Anty cecda fa'di hakan da tunanin.kuskuren da Mu'een ya aikata, sam bata son zancen rabuwa tsakanin su, bata do taji Ammi na wannan ikirarin amma ga dukkan alamu haian ka'dai Ammi ke muradu har cikin zuciyar ta a yanzu, bata damu ba indai za'a hora shi koda na shekara nawane amma bata so sam taji wai rana auren su za'a yi....
Tana cikin tunanin taji Ammi na fa'din" Yauwa bani Hudahn mu gaisa..".
Mi'ka mata wayar Anty Zainab tayi tana sakin ajiyan zuciya gami da murmushin 'karfin hali.
" Ki saki jikin ki wurin Antyn ki kinji, bata da matsala ni kaina nasani, kuma ki rage yawan damun kanki with time komai zai wuce kinji?"
" Toh Ammi".
Noor ta bata amsa cike da girmamawa yayin da Ammi ta cigaba da fa'din
" Kuma ko ya 'kira ki kar ki yadda ki sanar da shi inda kike Alhaji da kansa ya hana asanar da shi, bama shi ba duk wanda zai 'kira ya tambaye ki garin da kike plz Hudah kar ki fa'diwa kowa kinji?"
" Toh Ammi insha Allahu zan kiyaye...nagode sosai..".
" Bakomai".
" Ubangiji Allah ya 'kara girma.."
Daga haka suka yi sallama da Ammi.
Anty Zainab kam.kanta ta tallafa da hannu tana binta da idanu zuciyar ta cike da tunani...har gobe ladabin.Hudah na birge ta, yarinyar nada hankali sosai, me yasa su Ammi zasu yanke wannan hukuncin da wuri haka? A ganin ta raba shi da Noor sam bazai kawo gyara ba..kamata yayi a zauna a sake tunani..ita kam Noor da Mu'een duk cikin.zuciyar ta take jin su, bata sani ba ko dan Allah bai ta6a bata haihuwa bane shiyasa hakan oho, ko da wasa bata so taga 'dayan su cikin 'kunci in ba ya zama dole ba, ko 'kiran sa da bata 'dauka a yanzun ita ka'dai tasan yadda abin ke cin ta cikin zuciya, sai dai babu yadda zata yi ne kawai tunda ance dole sai an hora shi shiyasa take biye musu dan dole ba wai dan tana so ba.
Cikin zuciyar ta ta bar batun bayan ta yanke shawaran da take ganin yafi mata.
*****
Anty Zainab kam ba ya ita, Noor har kasa ganewa take yi cikin ita da Ammi waye yafi sonta, ha'ki'ka ba 'karamin dace tayi da iyayen miji masu tsananin 'kaunar ta ba, sai da kash 6angaren mijin ne aka samu babbar matsala domin sai a hankali.
Rayuwar ta take yi cikin kwanciyar hankali bata tare da damuwar komai yanzu, gidan Anty Zainab babu aikin komai dan duk house maid 'din ta keyi kuma haka suka saba abin su.
Girki ka'dai ne take yi shima 'din Anty Zee bata ta6a barin Noor tayi ita ka'dai.
Da yake dama sun jima da yin sabo da Anty Zainab so ba wani ba'kunta, Anty Zainab kam sai da nutsu ta fahimcevta sosai, da kanta ta gane Noor ma yanzu.bata 'kaunar sake zama da Mu'een hakan yasa ta ringa binta a yanda take so amma a kullum burin ta ba wuce taga ta gyara wannan auren ba sai da; ta lura cewa sai tabi a sannu.
Cewa tayi tun bayan rasuwar Baby ta lura Noor bata gyara jikin ta sosai, da yake Anty Zainab 'yar gayu ce ta gaske bata wasa da gyaran jikin ta, hakan yasa ta ja Noor suka je suka yi mata siyyaya na kayan gyaran jiki da mayuka masu kyau da tsada wanda zai dace da fatar jikin ta itama ta rara amfani da su.
Duk kuwa fitan da suke yi sosai Noor take 'ko'karin ganin ta kare martabar auren ta, bata ta6a barin kafar da za'a yi tunanin babu aure akanta da yake tasan har yanzun Mu'een bai sake tan ba.
Ammi kam na cana.mam sam hankalin ta ya kasa kwanciya musamman da yake tasan Mu'een 'dan gaban goshin Anty zainab ce, tasan a kullum abinda yake so shi take yi masa, hakan sai yasa take ganin kamar zata iya bashi daman ganawa da Noor batare da sun sani ba.
Saboda gudun kuskure ko kuma abinda kan iya zuwa ya dawo yasa ta bawa Noor shawaran kwashe numbobin ta dake kan Layin ta sai ta canza sabon Sim ta fara amfani da shi kafin zuwa wani lokaci.
Ai kuwa Noor bata yi musu ba tashin farko tayi na'am da wannan shawaran musamman da ta tuno 'kiran da yayi mata kafin tahowar ta Taraba.