Sashe 207
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai ya 'kagu ya gansa gaban matar shi amma abu ya gagara gashi ko waya basa yi da ita.
Anty ma ke yawan 'kiran sa shima yana 'kiran ta amma ko ta ha'da shi da Noor bata cewa komai..Anty duk bata san hakan ba dan da ta ha'da su take barin wurin ta tafi sabgar ta, shima 'din yanzu ba magana sosai yake yi ba dan haka duk shiru suke yi babu me ce da wani uffan.
Sau tari ita ke gajiya ta kashe wayar ko kuma ku'din dake wayar ya 'kare abanza sannan 'kiran ya yanke.
Idan yaga haka sai yayi murmushi kawai, wani sa'in yace" Zan kama ki ai yarinya bari kizo hannu na".
Barin Shuwarin yayi ranar wata litinin da sunan zashi Abuja duba wurin aikin sa daga nan kuwa daya kammala abinda yake yi sai ya nemi ticket ya wuce malesia ko Anty bata san zai zo ba sai 'kiran ta yayi ya sanar da ita cewa ya shigo.
Anty kam mamakin sa ne ya kamata dan bata ta6a zaton zai zo a wannan lokacin ba...bata san cewa ya samu 'karfin jiki har da zai iya doguwar tafiya irin haka ba.
Sai bayan ya iso kafin ya 'kira ya sanar da su Ammi yana dariya.
Ammi ma dariyar tayi tace" Kaji kunya ai...sai kace wacce bazata dawo ba Mu'een?"
'Yar dariya yayi yana sosa kansa.
Ammi sai tace" Antyn ka dawo to itama ta huta wa ranta da yi ma gadin mata tunda ka wanki 'kafa kaje..".
Dariya kawai yayi yana cire wayar a kunnan sa yace" Anty kinji Ammi wai ai sai ki koma gida tunda nazo".
Murmushi Anty Zee tace.
" Dama fa Umrah zamu wuce wai da ita da ta 'kare karatun .."
Take ya yatsina fuska gami da fa'din" A a Anty ni dai ban yadda ba kawai kiyi tafiyar ki, bacin ni nawa Jasmine al'kawari da kaina kuma sai ariga ni ki bari kawai zamu biki daga baya...Yau she ma akayi shawaran tafiyar ni ban sani ba, wato da banzo ba sai dai kawai inji kun tafi..ai kuwa ba da ita za'a yi wannan tafiyar ba".
" To ai shikenan zan yi magana da Baffan ku inji me ze ce shi kuma, kasan tafiyar daga wajen sa ne..".
Zama ya gyara yana duban Anty yace" Kice masa wurin wani likita na nazo kuma sai an yi 2months ana duba ni kafin in koma kar yace taho bada sanin sa ba..kuma kinga idan yaji cewa zan 'dan jima 'kila ya yadda bada Noor za'a Umran ba".
Dariya Anty Zee tace
" Ba wani ni nan..ni dai bazan yi 'karya haka kawai ba".
" Haba my one nd only Aunt dan Allah kiyi ha'kuri..ni ne fa?"
" Kai 'din dai".
" Anty please ki taimake ni kinsan halin sa fa yanzu sai kiji yace ban gama warkewa ba ina yawo bana son surutai wallahi".
" Toh dama me yasa ka tahowa gashi ma ko su Ammi basu san da batun ba".
" Ganin matata nazo Anty kuma ma ai na sanar da da su yanzu..".
" Amma yaushe zaka koma..?"
" Gaskiya ba rana".
Idanu Anty ta zaro tana duban sa sai yace" Erh mana...dan nifa gaskiya Anty 'kafa ta 'kafar mata ta haka kawai zama ya'ki 'karewa da banzo bama da shikenan anyi da ni tunda gashi shirin tafiya wata 'kasar ma kuke yi abin ku da Allah ne ka'dai yasan ranar da zan ganku..ni bawan Allah".
Ya 'karashe da karkata kansa.
" Kai kasa ni ai, dududu wata nawa ne, kayi shekaru biyu ma baka ganta balle watanni biyu kacal?"
" Su 'din Anty sai kiga sun fi yi min tsawo..".
" Hmm" kawai Anty tace tana murmushi.
Noor na school lokacin da ya iso so koda ta dawo ma bata san cewa gidan da ba'ko ba haka kuma Anty ma bata sanar da ita ba...har suka gama zaman su a parlour sai da ta shiga ciki dan kimtsa jikin ta kafin taga jaka a 'dakin ta.
Zaro idanu tayi da mamaki ta sake fitowa tace" Anty waye yazo kuma naga ja'ka a 'daki na?"
Fuskar Anty Zainab da murmushi tace" Mijin ki"!.
Tattare goshi tayi take ta ha'de ranta ta cike da salon shagwa6a tace..." Sai a 'daki na kuma Anty dan Allah?"
" Ina kike so ya sau'ka to Noor? 'dakin naki ai shine ya dace da shi".
" Anty dama me yasa sai nan gidan zai sau'ka ga kala-kalan hotels meyasa be sau'ka can ba?"
" Ki bari idan ya dawo kya tambaye shi..amma ni banda wannan amsar tambayar taki".
" Ni dai Anty 'dakin ki zan koma wallahi bazan zauna dashi a 'daki ba".
Tayi maganar ne tana juyawa ciki ranta a matu'kar 6ace.
Haka Anty na gani ta dinga kwaso kayan ta da duk wani abinda tasan zata bu'kata tana maida shi 'dakin Anty Zainab kamar wata me juju.
Anty Zainab kam binta kawai take da kallo tana murmushi cikin ranta ta ayyana" bari kuma in bar muku gidan sai inga inda zaki shiga".
Bata tanka ta ba har ta gama kwaso dukkan kayayyakin ta ta mayar 'dakin Anty.
Gefen ta tazo ta zauna tana sau'ke numfashin gajiya" Sannu".
Anty Zainab ta ce da ita tana 'karewa fuskar ta kallo.
Sai tayi murmushi ta kawar da kanta.
Ko da ya dawo kuwa bai yi mamakin ganin yanda 'dakin ya 'kara fili ba fiye da 'dazun yasan wannan ka'dan ne ga aikin Noor, be wani damu ba tunda yasan gida guda suke dan ta raba musu 'daki wannan ba zai zama damuwa ba.
Bai ga ko idanun ta ba har sai da dare lokacin suna zaune da Anty Zainab suna hira ya shigo.
Ha'de rai tayi sosai ita mantawa ma tayi da wani batun sa, da yake baya zama sosai a gidan yau 'in nan ya iso amma fitar sa ta kai sau uku.
Gaida Anty Zainab yayi yana zama gami da sau'ke numfashi yace" Wallahi Anty na gaji sosai..abani ruwa".
Shima ko kallon inda take be yi ba tunda ya shigo haka kuma itama, kanta 'kasa tana kan harha'do kalaman bakin ta wanda zata gaida shi da su.
" Aba ni ruwa Please".
Ya sake maimaitawa.
" Noor kawo masa ruwa"
Anty Zainab ta umarce ta.
Tsaye cak ta mi'ke bata ko dubi inda yake ba ta nufi kitchen tana 'kun'kuni..shi kam dama kawai so yake ya ganta da kyau shiyasa ya nemi ruwan dan yasan dole itace zata kawo.
Da idanu ya bita har ta lume sannan ya 'dan waigo nan yaga Anty Zainab kanta 'kasa ma ko kula da shi bata yi ba...ita gani take ma kamar zata takura musu gashi gidan ba asake yake ba hakan yasa ta fara tunanin komawa can gida in yaso ta taho Umrar daga can.
Dawowa tayi da ruwan ta mi'ka masa wanda yana kar6a ta furta" Ina yini?"
Bai amsa ba illa kallon fuskar ta da yake yi ita kuwa sam taki yadda ta ha'da ido da shi.
Yana amsan ruwan ta 'dauki wayar ta ta shige ciki.
Da shigan ta sai ta bu'de system 'din ta ta fara karatu wai dan kar tunani ya dame ta dan har ga Allah haushin zuwan nan nashi taji sosai..kafin Anty ta shigo kuwa har bacci yayi gaba da ita.
Washegari bayan tafiyar ta shima sai ya fita..nan Anty Zainab ta samu daman ganawa da Uncle Ja'afar ya kuma fahimce ta yace nan da jibi ta dawo gida toh.
Gadan-gadan ta hau shirin ta Noor da ta fahimci hakan ai sai kuka gashi ita da sauran kusan 10 days ya rage mata kafin ta 'kare exams gaba 'daya, haka har ranar tafiyar Antyn bata nutsu ta kwantar da hankalin ta ba.
Tana jin tamkar za'a barta da makashin ta ne agidan.
Tun tafiyar Anty kuwa sai ta daina ganin sa sosai domin bata zaman palour, idan ta shiga 'daki kuma datsewa take yi daga ciki.
Wataran yini take yi ta kwana ma bata sashi a idanun ta ba, lokaci-lokaci take ganin sa wataran da safe wataran kuwa sai Azahar take ganin sa.
Gaisuwa ka'dai ke ha'da su, gaisuwar ma sai ya ga dama yake amsata, domin sama-sama yake amsawa tamkar baya son gaisuwar tata ne.
Idan taga haka sai ta yatsina fuskar ta tayi gaba tana ta6e baki.
Sam Yah Deen bai takura ta ba musamman da ya san cewa exams take yi a lokacin haka zaman su ya kasance har lokacin da ta 'kare karatun..nan ta fara shiri cuz dama abinda ya ajiye ta kenan.
Lokacin da ya fahimci shirin da take yi nan ya dakatar da ita yace babu inda zata je sai ya kammala abinda ya kawo shi kafin su koma tare...dukkan abubuwan amfanin ta ya tattare a wurin sa bata san lokacin ba sai gani tayi kawai babu su..ba ATM 'din babu ticket da su I.D card 'din ta duk ya tattare.
Bata son jan magana tsakanin su hakan yasa taja baki tayi shiru bata tanka ba.
Wasa-wasa sai da suka shafe sati guda cur amma shiru bata ga alamun yana da niyyan tafiya ba kullum sai dai ya fita yawon sa ya dawo sai aukin kawo mata kayan ciye-ciye tun bata kulawa har ta fara dubawa idan ya kawo sai 'dauki abinda taga zata yi ci ta bar sauran anan..idan taga bai kula ba kuma da kanta zata koma ta canza musu wurin ajiya.
Gashi dole ya tilasta mata yin abinci da shi haka badan taso ba take yi ta ajiye masa..sai kuma yazo ma yace baya so tana ajiye masa a parlour ta ringa kai masa ciki.
Lokacin da ya gama fa'din hakan ya juya harara ta bankawa bayan sa tana tura baki..sai wani tsatstsare ta yake yi ga uban bada umarni.
Yanzu abincin nasa cikin 'daki take ajiye masa kusan kullum ma idan ta 'dauko sai taga ba sosai yake ciki ba amma tasan idan bata kai ba jan maganar zai yi.