← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 211

Sashe 81

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda Husnah ta so jin sa amma bata same shi ba...hankalin ta ya ta shi sosai gashi bata da number kowa a garin nasu balle ta 'kira taji..hakan sai ya hana ta natsuwa ji take tamkar tayi tsutsuwa taje ta ganshi taga halin da yake ciki.

A daddafe ta 'karasa yinin ranar duk ba'a nutse ba, wani irin so take yi masa mai wuyan fassaruwa.

Shima 'bangaren sa sai da yamma ne kafin suka fita filin ball shi da Imrana dalilin kenan da ya sa shi 'dan warwarewa...har dare kuwa bai kunna wayar tasa ba cuz haushin kowa ma shi yanzu yake ji, ko gida bai koma ba dan baya son ya ganni kuma babu damar hukunta ni a gaban Ammi domin for sure ya san akaina sai ta 6ata da shi, shi kuwa akan wannan munafurcin da yake tunanin ni nayi masa bai ga mai zai sa ya bar ni na sha haka nan ba.

Banda tsantsar kunyar Alhaji Baba da ta cika shi, kunyar sake ha'da ido yake yi da shi, dan yana ganin tamkar yana kallon sa matsayin mai kawo mace gidan sa hakan yasa ko hanyar gidan bai iya ya kama ba har washe gari.

Bai sani ba ashe Alhaji Baba kusan mutane hu'du ne suka ta kai masa gulman abin...da farko baya sa zancen aka.
Dan tunanin sa Muhamad 'din sa ba zai aika ta hakan ba, amma daga baya sai abin ya dame shi yasan idan har ba dagaske bane ba yadda za'ayi ma banbamtan mutane su ta kawo masa magana iri 'daya....shiyasa ya saka ido da kansa a hankali kuwa sai Allah ya nuna masa zuwan yarinyar har tayi parking ta shiga gidan.

Ransa ya 6aci sosai da ganin hakan, yasan babu mamaki mutane zasu masa kallon mutumin banza ne da har zai bar 'dansa ya ke6e yana rayuwa shi ka'dai yana kuma aikata abinda ransa yake so wanda za'a iya 'kira da banzar rayuwa duk kuwa da cewa babu wanda yasan abinda ke kawo yarinyar gidan.

Yayi niyyan tsawatar wa Yah Deen game da zuwan yarinyar ne bawai dan yana zargin sa da aikata sa6on Allah ba illah dan kawai ya tunadar da shi anfanin kare mutunci da kuma nesan ta kai da abin Allah wadai...shi yasa ko da ya nuna shi ba komai bane ke faruwa Alhajin yayi saurin yadda da shi.

*Nasan wasu zasu ce me yasa fa'dan sa ya tsaya iya can....ba cin azahiri abinda Mu'een ya aikata abin a tsawatar masa ne sosai....toh fa nima ina son sanin dalili sai dai nasan duk bazai wuci tsananin yadda da yayi da shi ba* .

Washe gari Husnah bata samu daman fita ba dan mahaifiyar ta ta tashi da zazza6i hakan yasa ta tsaya kulawa da ita gashi ko asbiti ma basu samu ganin likita da wuri ba, damuwar ta biyu ta zama amma dole ta danne 'dayan saboda SAWUN GIWA YA TAKE NA RA'KUMI.

*****
*Bayan kwana biyu*

Tun 'karfe tara na safe Husnah tayi parking 'kofar gidan Yah Deen...yana bayi lokacin yana 'ko'karin hanzartawa ya shirya dan zuwa gaida mahaifan sa cuz ba zai iya 'daukan tsawon lokaci batare da yaje gare su ba ko ma dan ya proving innocence 'din sa ya shi yanke shawarar shiryawa yaje...duk da ya san for now Alhaji Baba ya jima a gidan gona shiyasa ya 'kudira cikin ransa cewa yau 'din har gidan gonar zaije ya bashi ha'kuri ya kuma taya shi ayyuka inda hali ma acan zai taya shi yini bazai dawo da wuri ba har alokacin kuma bai kunna wayar sa ba.

Husnah na shiga ta cire mayafin ta...ta ajiye shi anan parlour da 'yar pulse 'din ta ta tinkari cikin bedroom 'din nasa.

Tana zuwa nan ma sai taga wayam baya nan hankalin ta ya so ya 'kara tashi sai dai sakamakon 'karan ruwa da taji a bayi ya sanya ta saki ajiyan zuciya.

Da baya ta kwanta a kan gadon dake 'dakin tana jiran fitowar sa.

mintina biyar mai kyau basu cika ba kuwa sai gashi ya fito 'kugun sa 'daure da towel fari.

Yanda ta ganshin sai ta ji wani sanyi cikin ranta ya ratsa ta...zaune ta mi'ke tana sake 'kare masa kallo tana murmushi.

Shi kam turus yayi da ganin ta sam bai ji da'din ganin ta ba a wancan lokacin, sai ma haushi da ya kara ji akan wanda ke 'kunshe cikin ransa.
Wani mugun kallo ya bita da shi ya ka'da kai yayi gaba tare da 'kara murtu'ke fuskar sa...haka ya nufi inda yake ajiye 'kananun towels 'dinsa ya zari 'daya ya fara tsane jikin sa da shi...bai ko sake kallon inda take ba.

Bai zata ba kawai yaji hannun ta kan hannun sa tana 'ko'karin kar6an 'karamin towel 'din daga bayan sa, a fusace ya juyo ya hanka'da ta baya ta tafi taga-taga kamar zata fa'di sai Allah ya taimake ta drawern mirror ya tare ta.

Da mamaki ta 'daga kai take duban sa, saman la66a ta furta sunan sa " Mu'een"! Tana 'kan'kance idanu alamun mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar ta.

Yatsa ya nuna ta da shi a fusace yace "..don't ever call my name again....and kiyi tafiyar ki, wa ma yace miki kizo...na 'kira ki nace kizo ne?"

Tsayuwan ta ta gyara cikin marairaita tace " Haba dan Allah Mu'een yau na fara zuwa ne da zaka fa'di hakan?..idan wani abin nayi maka ai sai ka sanar dani in gyara ba wai ka yi treating 'dina ba?"

.....Ido ya lumshe ya kuma bu'dewa cike da takaici ya kalle ta, 'karamin towel 'din ya rataya bisa wuyan sa ya tako gaban ta ya tsaya idanun sa cikin nata yace" Kin san wani abu?"
Husnah bata iya tace da shi komai ba sai ido da ta zuba masa sosai yake bata mamaki.

Bai damu da rashin amsawar ta ba shima kawai ya cigaba da fa'din "...Bani bu'katar sake ganin kin kusanci inda nake Husnah".

'Dago 'kafa tayi da niyyar 'karasowa kusa da shi sosai take sai ya 'daga mata hannu sannan ya girgiza mata kai tare da matsawa baya ka'dan a hankali ya cigaba da fa'din " Kin san abinda zuwan ki garin nan ya haifar min?....kinsan yanda hakan ya ta6a mutunci na Husnah, mahaifina fa da kansa yayi min maganar...kin san nauyin da naji ya kamani a lokacin?"

Kansa ya shafa da hannun sa 'daya tare da furzo iska daga bakin sa sannan ya cigaba da fa'din "....ki kama hanya ki koma inda kika fito and please kar ki kuskura ki sake zuwa gidan nan in ba ni da kaina na na neme ki ba...oyah..."

Ya nuna mata hanyar fita tare da 'kara matsawa baya.

Husnah kam maimakon ta fice a a sai ma ta taho da gudu ta shiga jikin sa ta rungume shi tana sakin kuka cikin salon yaudara....duk yadda ya so ya raba ta da jikin sa ya kasa, dole haka ya 'kyale ta...cikin kukan take fa'din Yayi ha'kuri kar yayi mata haka dan Allah....idan yayi mata katanga da kansa bata san halin da zata shiga ba..."
Da kakkausar murya yace
" Ohh ke kanki kawai kika sani baki san zancen mutunci ba ko....dallah sake ni 'katuwar banza 'katuwar wofi".

Wannan karan da 'karfi ya hanka'da ta sannan ya kamo hannun ta yaja ta zuwa parlour ya tura ta ciki ya koma abin sa ya datse 'kofan ta ciki.

Husnah haushi da ba'kin ciki sosai ya kamata dan haka a fusace ta zari mayafin ta da pause ko rufa mayafin bata yi ba kawai ta fita da 'dan gudu-gudu tana kuka.

Bata tsaya ta lura da mutumin da ke tsaye jikin mota daga gefe ka'dan da ita ba kawai ta shiga ta tada motar ta fizga da gudu tayi gaba bayan ta ha'da uban 'kura a wajen.

Zuciyar sa tamkar zata faso saboda takaicin halin da mafi soyuwa acikin zuciyar sa yake aikatawa, in bama shi ba ina shi ina wannan matar, ai da gani ba sa'ar rayuwar sa ba ce in ba biyewa zuciya ba.

Ya kai tsawon mintina uku bayan tafiyar tata kafin Alhaji ya shiga motar sa bai koma gidan gona ba sai ya wuce gida zuciyar sa na ta azalzalar sa dan 6acin rai.

Parlour yaje ya zauna shiru Ammi na ciki bata san da zuwan sa ba....ya kai mintina talatin da zuwa gidan sannan Ammi ta fito ta ganshi...da mamaki ta iso inda yake tana tambayar sa " Alhaji Lafiya kuwa?".

" Ba komai "
ya bata amsa a ta'kaice.
Ammi kam jan bakin ta tayi tai shiru cuz ta san tunda yace bakomai ga dukkan alamu ba hurumin sa ba ne.

Ruwa taje ta kawo masa ta ajiye gefen sa sannan ta zauna, tana shirin zata sake magana yayi saurin 'daga mata hannu.

Tsaye ya mi'ke yana safa da marwa cikin parlourn ransa ya kai 'kololuwa wurin 6aci...bai san me ze ce game da wannan lamari ba.

Yana cikin hakan Yah Deen yayi sallama, Ammi ce ka'dai ta amsa shi.
Shi kansa sai da yaji wani iri ganin Ammi ta buga tagumi ga kuma Alhaji tsaye cikin yanayi na damuwa....tunanin sa ko tun fa'dan shekaran jiyan ne bai 'kare ba hakan sai ya sashi tsarguwa.

A 'darare ya 'karaso gaban Alhajin yana niyyan durkusawa dan gaida shi sai kawai yaji sau'kan mari saman kuncin sa....daga Alhaji Baba.

Cikin ka'duwa ya dafe fuskar sa yana kallon Alhajin da cikin idanun sa ka'dai zaka kalla kasan cewa yana cikin yanayi na tsananin 6acin rai, yanayi ne da ya jima bai shige shi ba.

"....Waye ubanta?..Muhammad ka gaya min 'yar waye?"

Cikin rashin fahimta ya 'dago idanun sa da suka koma jaja ya zubawa Alhajin da alamar tambaya sannan ya juya ya kalli Ammi ma da ta mi'ke tsaye tun sanda Alhaji ya mare sa.

"...Irin rayuwar da kaga ta dace ka za6ar wa kanka kenan ko Muhammad?...mutunci na kake son zubar min agarin nan shiyasa ka nuna min ban isa da kaiba, inace da kaina na garga'de ka akan ban son in 'kara ji ko ganin tazo ko ba ji da kai muka yi maganar ba?"
Chapter 81 · 0% Book details