Sashe 127
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko yanzun ma zuciya ta cunkushe nake tafiya ina sake jin wani 6acin rai da fargaba suna sake shiga ta, har na shigo gidan ban daina jin hakan ba, dalilin ma kenan da ya sanya ko sallama ban iya tunawa nayi na.
Da yake mafi yawan ranaku idan na dawo bacci zan tarar yake yi wasu ranakun kuwa ban samun sa agida so ban cika samun amsar sallama ta daga bakin sa ba...sai dai duk ranar da yasan zai fita yakance da ni in tafi da key holder saboda bai san lokacin dawowar sa ba.
Ko takalman 'kafata ban tsaya na cire ba kawai na 'daga curtain na parlourn sannan na sa kaina na shiga ciki.
Ciki-ciki nayi sallamar kamar wa kaina nayi ta kaina a 'kasa nake tafiya, nasan in ba ganin ahali na nayi ba bazan ta6a iya daina kewar su ba, kullum sune cikin raina safe rana da dare.
Sam ban lura da inda na saba ganin sa kwance ba cuz damuwa ce fal zuciya ta hakan yasa na cigaba da tafiya har na isa tsakiyan parlourn sannan na yi tunanin dubawa ko yana nan...nan take nayi gamo da mugun gani, abinda har 'karshen rayuwa ta bazan ta6a iya daina ganin sa cikin idanu na ba.
Ji nayi kawai kaina na juyawa jakar makarantar dake hannu na ma ban san lokacin da ya bar jiki na ba ya fa'di 'kasa...kafin kice miye hawaye ya wanke min fuska ta....duk da 'karancin shekaru na amma hakan bai hanani fahimtar mummunan abu suke aikatawa ba.
Fa'duwar jakar tawa ne ya fargar da su, da sauri Yah Deen ya mi'ke yana dafe goshin sa da hannun sa...
Ni kam da 'karfi na rintse idanu na amma sai na kasa barin su a hakan saboda ko na rufe ban daina ganin abinda na gani ba.
Hakan yasa na sake bu'de wa nan na sau'ke su akan fuskar budurwar sa Husnah wacce na sani tun ba yau ba, ita kanta fuskar ta babu alamun walwala sannan ta wani takure wuri guda siraran hawaye na bin kuncin ta.
Ko ka'dan banji tabani tausayi ba illah haushin ta da ya cika min zuciya, gani nayi yana 'ko'karin nufo inda nake hankalin sa a matu'kar tashe...sam ban son ya zo kusa da ni, haka kawai sai naji ina 'kyamar sa, wata tsanar sa naji ta shiga zuciya ta fiye da tsanar da nayi masa abaya, da sauri na fara yin baya-baya ina shashshe'kan kuka idanu na na kansa.
Ganin da yayi fita nake da niyyar yi ya sanya shi fara 'kiran sunana cikin sanyin murya" Noor"! Yace tare da yimin alamu da hannu akan inzo.
Da jin hakan sai na
juya na fita da gudu ina kuka..." OMG... Ke Noor"!
Ya sake 'kira na da 'karfi cikin tashin hankali.
Ko kallon gabana ban yi na ringa sauri sai da na tabbatar nayi nisa da gidan kafin na 'dan saita tafiya ta, ban zame ko'ina ba sai gidan Ammi.
Na same ta a 'daki idar da sallar ta kenan ko tashi daga kan daddumar ma bata yi ba na same ta.
Sallama ta da shigowa ta duk lokaci guda....jikin ta na fa'da na rungume ta sannan na saki uban kuka wanda da kajishi zaka fahimci cewa cike yake da 'dacin zuciya.
Ammi kam hankalin ta tashi yayi matu'ka, rikicewa tayi tana tambaya ta abinda ya faru amma ban iya nace da ita komai ba illah kukan da na cigaba da yi mai cin zuciya.
Ammi tayi lallashin tayi tambayar ina Yayan nawa, in gaya mata abinda ya same ni amma duk abanza har lokacin bance da ita komai ba...balle tasan ainahin damuwa ta.
Gajiya tayi da tambayar tawa, gashi itama zuwa lokacin hankalin ta ba 'karamin tashi yayi ba, dan haka sai ta barni ta tafi ta 'dauko wayar ta ta 'kira layin Yah Deen, jin layin sa ya shiga ya bata daman sauraren sa da kyau domin taji yanayin sa, domin tayi tunanin ko wani abu ne ya same shi.
Ai kuwa jin sautin muryar sa da yayi mata sallama cikin sassanyar murya yasa ta adake tace da shi" Kana ina ne?"
Yace " Ina gida Ammi".
" To kazo ina neman ka".
Shi kam " _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ " kawai ya iya furtawa cikin zuciyar sa, yasan dama dole yarinyar nan sai ta fa'da, abinda ya tsana kenan shine tonuwar asirin sa musamman wurin iyayen sa.
Sai ga shi dan iya shege yarinyar ta rasa inda zata nufa da maganar nan sai gurin Ammi...
Ai da kunya ma ace duk abubuwan da suka faru tsakanin sa da iyayen sa ace kuma tun ba'aje ko'ina ba ya watsar da duk maganar su ya aikata same laifin da suka hane shi da aikatawa..wanda dalilin hakan ma suka ha'da shi zama da ita, yanzu kuma me ze je ya ce da Ammi fisabilillahi, da wani idanu zai dube ta?"
Ji yake tamkara ya shirya kawai ya bar garin batare da kowa ya sani ba, amma yasan yin hakan tamkar yayi prooving laifin sa ne...sam ya rasa mafita, takaicin zaman sa da ita ne ya shige shi, yasan da badan ita, ba da babu abinda zai tona masa wannan sirrin a yanzu..sai gashi ita ta tona, sha'afa ma yayi da lokacin dawowar tan da bazai bari ta samo shi yana aikata wannan abin ba, ita da ba amfanin komai take yi masa ba sai ma haifar masa da tashin hankali koda yaushe.
Tun 'dazu yake zaune dafe da kansa ya kasa tsinanawa kansa komai,
Husnah ta wuce tuntuni amma shi har yanzu bai iya yin koda wanka bane saboda damuwar da ta cika masa zuciya...." Mtheww" ya ja tsaki afili gami da mi'kewa...da tashin sa sai ga shigowan 'kiran Ammi wayar sa.
Koda ya ga 'kiran Ammi fargabar sa 'karuwa tayi akan na baya, da farko kamar ba zai 'dauka ba amma yasan yin hakan ma 'karin wani laifin ne.
Sai da ya koma ya zauna kafin ya 'daga wayar gami da sallama.
Tashi jikin sa sanyi 'kalau ya ta shi ya shiga wanka bayan sun gama waya da Ammin... yasan yau kam ta faru ne ta 'kare kankat, bai kuma san mai su Ammi zasu ce da shi ba bayan duk nasiha da warning 'din da suka yi masa amma ya watsar...shi kansa kunyar kansa ma ya fara ji yanzu.
Wata zuciyar tasa ne tace da shi" ai ba laifin ka bane taya za'a ha'da ka da 'yar yarinyar nan matsayin mata kuma ayi tunanin zaka iya kame kanka bacin ansan yanayin ka?...yasan wannan ba hujja bace da ya kamata ace ya ri'ke amma ta wani 6angaren zancen yayi masa aganin sa ai hakan 'dinne ba shivda laifi.
Sharp-sharp ya shirya ya fita zuwa gidan Ammi...inda yaje ya tarar da Ammi zaune a parlour ranta ya kai 'kololuwa wurin 6aci tana zaune kurum ta rafka uban tagumi, yayin da ni kuma nake cikin 'dakin ta na daina kukan a lokacin illah ajiyan zuciya...tun 'dazun.kuma Ammi.bata sake tambaya ta wani abu ba, haka kawai taji aranta cewa shine bashi da gaskiya...'kilan duka na ma yayi.
Hakan ka'dai da tasa cikin zuciyar ta ya sanya 6acin ranta ninkuwa akan na baya da yake tasan halin sa bashi da sau'ki wurin hukunci.
Yana shiga tun kafin ya rufe bakin sa daga sallamar da yayi Ammi ta fara jero masa tambayoyin tuhuma game da ni.
Marairaice murya yayi jin tambayar sa Ammi take ba nuna masa laifin da ya aikata ba, hakan ne yasa shi fahimtar itama labarin bai shiga kunnan ta ba tukunna.
Wani sanyi yaji cikin zuciyar sa shiyasa ma ya samu 'karfin gwiwar 'karasowa kan kujera yana shirin zama ya ba Ammi amsa a tsare da fa'din" Ammi ni kuma me zan mata kawai fa rigima ce ke damun yarinyar nan?"
Da yaren su ta fara yi mai masifa saboda bata so inji abinda zata fa'da masa, yayin da ya Yah Deen ya zauna dafe da kansa yayi shiru yana sauraren ta duk da ya fahimci bata san komai ba amma still ya kasa sanya idanun sa cikin nata.
Ammi kam ta inda take shiga bata nan take fita ba masifa ta ringa yi masa akan sam baya bani kulawa shiyasa zai zo yace da ita bai san me ya same ni, in ba haka ba dubi yarinya ko uniform bata cire ba ta taho tana wannan uban kukan kuma yace bai san komai ba?"
Daga 'karshe Ammi 'kwalla min 'kira tayi, sai nayi banza da ita kamar banji ba, sai da ta sake 'kira na kafin na taso na fito idanu na jajazur.
Yah Deen kam ko 'daga kai ya kalle ni ma bai yi ba saboda tsananin kunya da ta cika shi...nima 'din kuma ban kalli inda yake ba dan ysananin haushin sa nake ji yanzu.
Cikin fa'dan Ammi kaf baiji abinda ya 'daga masa hankali kamar ganin yanayi na ba, saboda a maganar Ammin bai ji abinda ya danganci lamarin ba...sai dai ganin yanda duk na fita hayyaci na ya matu'kar 'daga masa hankali.
Ta wani 6angaren godiya yake ga Allah da yasa ban riga na gaya mata ba yana kuma fatan fa'dan nata ya tsaya iya nan kar Alhaji Baba yaji, ni 'din kuma kar na fa'di komai.
Gefen Ammi nazo na zauna tare da kwantar da kaina a jikin ta na 6oye fuska ta..." Ta shi ki sanar da ni Abinda ya miki banaso ki 6oyemin komai kinji mama na".
Ammi tayi maganar tana 'ko'karin tallafata.
A hankali da rawar murya nace.
" Bakomai Ammi".
Kwafa tayi gami da sake 6ata ranta tace.
" Ina wasa da ke ne?"
Sai na yi saurin fa'din " Ammi dagaske ba abinda ya min..ni gida kawai nake so nake so in dawo".
Yah Deen bai iya ya bayyana farin cikin sa da jin hakan daga bakin Noor ba amma idan kana fuskantar sa zaka ga yanda ya lumshe idanu yana 6oyayyan murmushi na farin ciki.
Cikin ransa ya furta" Allah yayi miki albarka Nuree".
A fili kuwa yana nan a zaunen sa bai ko motsa daga yanda yake ba.