Sashe 137
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya 'dan biyo baya na 'tan sakanni.. daya ke wayar ba'a speaker yake ba so Addah Maryam sai ta zaci ko shirun da nayin sauraran maganar sa nake yi dan haka bata ce da ni komai ba...yayin da ni kuma cikin zuciya ta aikin harha'do maganganun da zan furta agare sa nake yi ko zan yi sa'a ya bar ni in bi Addah ta.
Kafin nayi magana sai ya rigani da fa'din" Ba wata matsala ko ?" Girgiza kaina nayi kamar yana kallo na sai daga baya kuma nace" a a bakomai".
" Ok...Ya su Mama".
" Lafiyan su qalau".
" Da kyau".
yace sai kuma ya 'kara yin shiru.
Jin yayi shirun ne ya sani nayi niyyan yi mai magana take kuma sai naji jiki na yana 'kai'kayi tamkar marar gaskiya, 6ata raina nayi nace..." Ya..yah".
Yace
" Ina jinki...ya akayi?"
"....Addah Maryam zata koma Darazau gobe...".
Batare da wata damuwa ba yace
" Owk Allah ya kaimu goben akwai matsala ne?"
Sai nace
" a a...ni dai ina so in bita ne..."
" Ki bita kuma? Me zakiyi acan 'din?".
" Bakomai ni dai ina so inje ne kawai".
" Shine aka ce sai kin gaya min?"
" Ummah bazata barni ba inje ba wai sai ka yarda shiyasa".
Shiru yayi na 'dan lokaci sannan yace" Kwana nawa zakiyi?"
" 2months kawai".
" Ban yadda ba...1 week zakiyi ki dawo kinji?"
"Uhum".
Nace a hankali ba dan na amince da hakan ba.
Shiru ya 'dan biyo sai can yace " Dan haka kika 'kira ni ko?"
Shiru nayi masa ban bashi amsa ba dan ni 1week 'din da yace 'din sam bai game ni ba sai ma naji ya 6atan raina gaba 'daya duk da bawai zancen ya hau kaina bane.
Jin nayi masa shiru ne ya sa shi fa'din " Toh bye..sai na dawo ko?".
Bance 'kala ba har ya kashe wayar tasa.
Kallon Addah ta nayi da ta zuba min idanu tana kallo na...ina 'dan ha'de rai nace da ita yace inje".
" Yauwa ko ke fa...ai dama nasan ba zai hanaki ba, kawai ke 'din ce dai wata iri...daga haka ta 'kara 'dora min wasu lectures 'din cikin 'kwa'kwalwa ta.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce*😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *66*
Bayan mun rabu da Addah Maryam sai na 'kira Ammi...ko yau 'din ma bata 'daga ba sai da nawa 'kiran ya yanke kafin ta 'kirani daga baya, gaida ta nayi sannan na sanar da ita cewa na tambaye sa kuma ya amince wai inje.."
" Owk...yayi kyau..ni na fiso ki tafin ma ai kije ki huta abin ki Mama na".
Cewar Ammi...yayin da na 'dan yi murmushi daga 6angaren da nake.
Tambaya ta tayi" yaushe ne ma dama ranar tafiyar ?" sai na bata amsa da fa'din" Gobe ne fa Ammi".
Tace" To shikenan Allah ya kaimu"
Da" Ameen" na amsa ta a ta'kaice...daga hakan bata ce da ni komai ba kawai sai sallama da muka yi.
Da yamma ban zataba kawai naga Ammi ta aiko min ku'di har 10k da tsarabar da zan tafi da shi wai, take kuwa na 'kira ta na sanar da ita cewa ai akwai ku'di a guri na tun wanda Yah Deen ya aiko min farkon tafiyar sa ma suna nan ban yi komai da su ba harda wanda ake aiko min ma".
Tace" Wancan ai naki ne Mamana wannan kuma ni na baki kuyi ku'din mota".
" Ammi ai zasu yi yawa to..."
Ban 'karasa rufe baki na ba ta tare ni da fa'din wai na koyi musu yanzu..."
Jin haka ya sa na bata ha'kuri gami da godiya daga haka ta yanke 'kiran daga 6angaren ta.
Ummah ta kam tunda taji cewar Yah Deen ya bar ni yin tafiyar bata ce da ni komai ba, ashe ita dama damuwar ta shi 'din ce kawai, bata fito fili ta bayyana hakan bane saboda ita tunanin ta babu hanyar da zan sanar da shi cuz bata ta6a ji ko ganin ina waya da shi ba shiyasa kawai ta yanke shawarar hana ni tafiya saboda babu bakin mijina.
.....Ummah ta kullum tausayi na take ji cikin ranta musamman da ta fahimci cewa babu wata sha'kuwa ta kirki tsakani na da Yah Deen, tasan dama zama na dashi zai matu'kar bani wahala cuz ni ba kamar su Addah Maryam nike ba, kaf cikin 'ya'yanta babu wacce ta gado halayyar ta sama da ni, sanyin hali da kuma rashin sawa rai abu.
Shiyasa take ganin da 'kyar ne zaman mu yayi saiti saboda shima 'din bai wani nuna alamun son auren ba koka'dan, a 'dan zaman da nayi agidan ta fahimci auren na mu suna kawai ya tara ba muhimmanci ke gare shi wajen mijin nawa ba balle tayi tunanin ko watarana zai yi kyau...shiyasa a kullum take sani cikin addu'ar ta akan Allah ya daidaita tsakanin mu in har kasancewar mu taren alkhairi ne in kuma ba alkhairi bane ta kance Allah kai kasan yanda zakayi da auren nan Yah Allah babu wanda ya isa yace maka ga yanda zaka yi..Allah kayi mana jagora cikin al'amuran mu ka bawa yarinyar nan kariya.
Addu'ar da Ummah ta ke yawan yi min kenan kusan koda wani lokaci cikin sallar ta.
Kaya na da nake amfani da su wanda aka kawo min daga gidan Ammi da su ka'dai na shirya tafiyar, dan musamman ma Ammi ta 'kira ni tace ya kamata in zo in duba wasu kaya wa'danda yakamata inyi tafiyar da su sai nace mata a a wanda nake tare da su ma ka'dai sun isa..ta so ta nuna 'kin amincewar ta da hakan saboda a fa'dar wai ai sun sha ruwa sai na nuna mata ai ba abinda ya same su ni ban ma fiya amfani da su ba sai dogayen riguna ka'dai, haka dolen Ammi ta 'kyale ni ba dan ta so ba.
Washegari kuwa ni da Addah Maryam muka wuce Darazau cikin kariyar ubangiji muka isa lafiya lau batare da matsalar komai ba.
*****
Tun tafiya ta ban yi waya da shi ba har na kwana biyar a can, bai 'kira ni ba sam ganin hakan yasa nima kuma ban yi 'kiran sa ba, na kanyi da waya da Ummah, Anty Zainab da kuma Ammi na kusan kullum amma banda shi...ko Addah Maryam sau biyu take tambaya ta cewar mun yi waya da shi ne?"
Sai nayi saurin bata amsa da fa'din" Erh" saboda bana so ta sake sani a gaba tace sai na 'kira shi.
Haka nayi ta faman 6oye mata gaskiyar lamarin ina kaucewa duk dalilin da zai sa ta fahimci tsakani na da shi.
Sau tari idan saif ko Ammi sun 'kira ni matu'kar tare muke da ita na kan yi basaja na tashi daga inda take tamkar shine ya 'kira ni sai na koma can cikin 'daki na amsa wayata cikin kwanciyar hankali, hakan da nake yi kuma sai ya 'dan kwantar da hankalin Addah ta har sai ta ma daina tambaya ko munyi waya domin a tunanin ta shine ke 'kira na.
Sosai Addah Maryam ta zage dantse wurin fahimtar da ni sirrin da ke cikin aure, wasu lokutan nibkam har mamaki take bani yanda ko 'dar bata ji ballantana taji kunya ta, a mafi yawan lokuta idan ta gama tsara min karatun nata nan nake bar mata su saboda nawin da suke wa 'kwa'kwalwata sai inji sam wannan ba hurumi na bane bama zan iya ko abu 'daya daga cikin su ba.
*****
Ranar dana cika mako guda acan aranar Yah Deen ya 'kira Anty Zainab yake tambayar ta wai yaushe rabon da muyi waya da ita?"
Dagangan tace da shi" Ai ko yau ma bamu da'de da yin waya ba, wani abu ne ya faru?"
Ta 'karasa da tambayar sa sai yace a a ba komai kawai ya tambaya ne..
Shiru ya 'dan biyo Anty kam so kawai take yi taga iya gudun ruwan sa, yayin da shi'din kuma sai yakasa ha'kuri da maganar saboda yanda yake jin abun na tawo cikin ransa sai yace" Anty wallahi wannan yarinyar ta ba 'karamin raina ni tayi ba"
" Me kuma ya faru Mu'een kai kullum ba'a rabaka da masifa me yasa ne?".
" Haba Anty! tun tafiyar ta fa ko 'kira na bata ta6a yi ba, ba dan Allah ma yasa kuna waya da ita da kuma Ammi ba ma ai da ko halin da take ciki bazan sani ba, fisabilillahi hakan ya dace kenan...?"
Anty sai tace masa
" To kai me yasa baka 'kira ta ba?..ai idan.ita bata 'kiraka ba kai da kake matsayin sama da ita kai 'din sai ka 'kira ta kaji halin da take ciki, kuma ma fa kai da kanka kasan yarinya ce Hudah har yanzu me ta sani har yanzu da sauran ta..."
" Yarinya ce Anty amma ai ansan hakan kuma akayi mata aure".
Ya tari bakin ta da fa'din hakan a masifance.
'Dan.murmushi Anty Zainab tayi sannan tace" to ni kam Mu'een miye laifi na yanzu cikin maganar nan? matar ka ce fa yanzu she is your responsibility kai ke da alhakin kulawa da ita lafiyar ta da komai, balle gashi yarinyace 'karama abubuwa da yawa kaine zaka fahimtar da ita...".
" Anty ai shiyasa tun farko ni banso auren ba..lokuta da dama idan na tuna wai wannan yarinyar ce aka 'daura min aure da ita Allah kar kiga yanda nake ji a raina, yaushe zan iya da ita? yarinya 'karama ta maida ni tamkar ni tsaranta?..."
"...kana son girma sosai kaima, kuma tunda kasan yarinya ce me yasa kai baka yi 'kiran ta ba kaci girman?"
" Hmm" kawai yace da ita..sannan ya 'dan sau'kar da murya yace..." Ai yau zata dawo ko..zata gamu da ni ne..".
Anty kuwa sai tace
" Ba dai yau ba kam dan bata ce da ni yau zata koma ba".