Sashe 132
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kan yi 'ko'kari wajen ganin ya kaucewa hakan kamar yanda ya kaucewa Husnah abaya amma abin ya faskara, sosai yake jin wani abu na fisgar sa izuwa gare ni da ya jima bai tsinci kansa cikin irin yanayin ba.
Kamar yanda yayiwa kansa al'kawarin rabuwa da Husnah hakan ne ya faru, duk dama ya daina ganin ta a school bai kuma san dalili ba, amma koda wasa bai ta6a gwada 'kiran layin ta ba balle yaji meke faruwa, shi da kansa yana so ya nemi yafiyar ta bisa abubawan da suka ta faruwa abaya, amma ya san koda ya 'kira ta yanzu bazata ta6a yadda da duk abinda zai fa'da mata ba shiyasa kawai ya 'kyale ta.
Kuma bai iya ya tattauna batun ko da Ishaq bane haka ya bar lamarin cikin ransa, sannan yayi 'ko'karin tsare zuciyar sa daga fa'dawa tarkon wata macen bai bari ko wacce mace ta birge shi ba balle yayi wani tunani akanta tunda ya koma karatun sa kawai ya sa agaba.
*****
Ranar da na cika kwanaki na na takwas da fara kwana wurin sa ranar cikin farin ciki nake jin zuciya ta saboda nayi waya da Baban mu da daren ranar har ma yayi min albishir 'din ya kusan zuwa Shuwarin domin yanzu jikin sa Alhmdulillah da sauqi, jinin ya 'dan sauqa, da yake tunda jimawa baya jin da'di har Alhaji Baba ma yaje can Jos 'din ya dubo shi haka ma Yah Usman yaje.
Alhaji Baba ne da kansa ya ha'da ni da shi a wayar ko yau 'din ma, inda bayan mun gama waya da Baban mun yace dani insha Allahu zai siya min waya ta nima in huta da ta aro tunda mijin nawa bai san yayi abinda ya kamata ba.
Farin cikin nawa sai suka zama tagwaye, sosai naji murna ta kamani, take kuwa naje nayi wa su Ammi albishir da su Saif ina murna ta.
Alhaji Baba kam murmushi kawai yayi ya girgiza kansa.
Haka har na tafi 'dakin nasa fuska ta da walwala, yau sallama ta ma da 'dan sauti nayi ta, yana kwance akan gadon yana daddana wayar sa.
Sallama ta tace ta sa shi ya mi'ke zaune da mamaki yana kallo na.
" Ina yini "
nace da shi, sai amsa da lafiya a takaice.
A hankali na 'karasa bakin gadon 6angaren da nake kwana ina shirin kwanciya ya dakatar da ni da fa'din sunana " Noor" yace madadin Hudah da kowa ke 'kira na da shi.
" Na'am" na amsa shi tare da waigowa na dube shi.
" Je kawo min ruwa na sha".
Yace cikin natsuwa.
Bance komai ba kawai na mi'ke na yi waje kaina da hijabi na kamar kullum, tun lokacin da naga yanayin halitta ta ya 'kara canzawa shikenan na 'kullawa hijab kamar wawiya, musamman ma da yanzu nake zuwa wurin sa bacci haka nake kwana in tashi da abu na a kaina.
Yanzun ma da idanu kawai ya raka ni har na 'karasa fita daga 'dakin, haka na dawo na same shi kamar yanda na barshi a zaune.
Wajen sa na nufa da sassanyan ruwan faro da na 'dauko na mi'ka masa.
A hankali ya 'dago hannun sa na dama ya dam'ki ruwan tare da lumshe idanun sa duk biyu...bansan me yasa ba nima karo na farko tunda na fara kwana a 'dakin sai yau naji inaso inga fuskar sa da kyau musamman da yanzu yake kusa da ni, a hankali na 'dago idanu na na sau'ke su akan nasa lumsassun idanun" Masha Allah".
Naji zuciya ta na fa'di a sirran ce...motsin da bakin sa ya fara ne sani maida idanu na wajen bakin na sa.." Yayi sanyi sosai..'dauko min wani please".
Ya fa'di tare da bu'de idanun sa dake lumshe take sai muka yi 4 eyse dashi...bazata kawai naji harbi a 'kirji na da ya sa 'kafafu na yin sanyi 'kalau nan take sandaiyyan sanya 'kwayar idanu na cikin nasa.
'Kasa nayi saurin yi da nawa idanun sannan can ciki na amsa shi da fa'din" to"...ina shirin juyawa sai naga ya ajiye ruwan da na kawo masan kan side drawer, sannan da hannun sa mai sanyin naji ya kamo hannu na, da sauri na 'dago na kalle shi da mamaki 'karara kan fuskata, ina 'ko'karin fizge hannun nawa daga nashi naji yace" Me ya faru kuma?"
Banyi magana ba kawai na kalli hannun san inda ya ri'ke ni, shima sai yayi 'kasa da idanun sa zuwa wurin, murmushi 'kayatacce yayi sannan yace" ba kyaso?"
Nayi shiru.
" Me yasa to?"
Still ban bashi amsa ba illah 'ko'karin cire hannu na daga cikin nasa da nake ta faman yi amma na kasa.
Da 'dayan hannun sa ya 'dauko ruwan daya ajiye 'din sannan ya bu'de hannu na ya samin na ri'ke" Ki tafi da shi".
Still bai sake min hannun ba ya 'dago ya kalli idanu na yana murmushi yace da ni" Kije in kin dawo zaki fa'da min me yasa kike son zama da hijab 'din nan akanki".
Da fa'din haka ya saki hannu na...sai naja baya da sauri ina sake kallon sa, idanu ya lumshe take ya kuma bu'dewa yana murmushi, sai na juya na fita daga 'dakin zuciya ta na dokawa.
Ina tafiya har sar'kewa 'kafafuna suke yi saboda ru'danin da na shiga, zuciya ta ta kasa tantance min abinda ke damin Yah Deen a yau 'din gaba 'daya.
Yana yin abu ne tamkar ba shi ba.
*Fatan Anyi Sallah lafiya.....Allah ubangiji yasa ibadun mu su kasance kar6a66u* 🙏
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce*😍
https://www.facebook.com/106273870926057/posts/149762286577215/?app=fbl
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *64*
Yanzu Ammi ta daina damuwa da ni saboda taga na 'dan saki jiki na, kuma ko na shiga wurin san bana sake fitowa.
Abu 'daya dai da kullum baya raba ni da ita shine kafin in shirya in tafin sai ta tisa 'keya ta nake tafiya wanda burin ta kawai a kullum yanzu shine taga tafiyar na tafin matu'kar na riga na shiga 6nagaren nasa shikenan itama sai ta wuce shiyasa ma ko da ya aiko nin 'dauko masa ruwan tun fitowa ta na farko ban tadda ta a parlour ba.
Yanzun kuwa da na fito jin yanda 'kafafu na ke sar'kewa da yanda 'kirji na ke dokawa ne ya sanya ni samun wuri na zauna akan kujera na 'dan maida numafshi na.
Sai da na tabbatar na samu natsuwa kafin na tashi na canzo masa ruwan, ko da na shiga 'dakin kuma sai ban gan shi ba.
Da'di naji har cikin raina, da sauri na 'karasa dan inyi in ajiye masa inyi baccin 'karya kafin ya tuhume ni amma tun kafin in 'karasa tsakiyan 'dakin na gansa ya fito daga bayi kamar dama jiran shigowa ta yake yi, take wata fargabar ta sake kamani mai tsanani.
Jikina sanyi 'kalau na 'karasa na ajiye masa ruwan gefen da na same shi 'dazu ko iya sake kallon inda yake ban yi ba...'dagowa nayi da niyyar isa nawa 6angaren in kwanta sai naji nayi karo da mutun ta baya na, da sauri na waigo cike da firgici da ya bayyana har kan fuska ta.
Kafin nayi wani yun'kuri sai naji hijab 'di na ya bar jiki na gaba 'daya.
'Kan'kame jiki na nayi zan saki kuka sai yayi saurin dakatar da ni da tsare ni da idanu tare da tsaida yatsan sa saman bakin sa.
Taimako 'daya Allah yayi min kayan bacci na masu yalwa ne riga mai botila da kuma dogon wando farare ne masu zanen flowers maroon amma duk da haka sai naji na kasa sake wa a gaban sa.
" Miye matsayi na a wajen ki?"
Naji ya tambaye ni bayan ya cire hannun sa daga bakin nasa.
Ban bashi amsa ba sai nayi baya ka'dan ina dama fuska ta amsar da zan bashin sam banji ta cikin brain 'dina ba.
Biyo ni yayi da taku 'daya zan sake matsawa baya kawai sai naji ni jikin bed na...take hawaye ya gangaro min tsoro ya kamani cuz ba wurin guduwa kuma.
Yanda naga yake kallo na ya sani sake yun'kurin neman hanya inda na sake yin baya zuciya ta cike fal da tsoron sa, cikin rashin sa'a sai na fa'di da baya na kan bed 'din ina neman hanyar zamewa sai naga ya matso daf da ni, fuskar sa kusa da tawa, kallo na ya tsaya yi daga idanu na zuwa dukkan ilhirin fuska ta...yayin da zuciya ta ta cigaba da dokawa da sauri da sauri jiki na ya fara kakkarwa sosai.
Da hannun sa naga ya shafo kansa tare da juya idanu..." Ba ance ni mijinki ba ne?"
Naji ya sake fa'di cikin jan maganar kamar dole aka sanya shi.
Saboda ina so ya 'kyale ni nayi saurin 'daga masa kaina sama alamar " Erh"
Sai yace" To daga yau banson wannan abin a inda nake.. kinji ko?"
Yayi maganar tare da 'dago hannun da ya ri'ke Hijab 'dina da shi dayake har a lokacin yana na'de a hannun sa.
Kaina na sake 'dagewa ina bin hannun san da idanu kuma har a lokacin jiki na bai daina rawa ba, buri na kawai inji ya bar kusa da ni...shiru ya 'dan biyu baya na sakanni, yayin da ya cigaba da 'karewa fuska ta kallo batarecda ya 'karacfa'din komai ba idan na yun'kura sai ya tsare ni da idanun sa dole na ha'kura illah hawaye.
Sa ban fahimci komai daga yanayin da yake ciki ba a lokacin ko ka'dan, ni dai damuwa ta ya 'kyale ni ne kawai, hakan yasa hawaye na ya kasa tsayawa.
Da yatsa 'daya ya shafo hawaye na dake gangarowa, a hankali cikin sanyin murya yace dani" Kukan fa na menene?"
Ban bashi amsa ba na yi shiru saboda ni agani na tambayar tasa bata da amsa a waje na... cikin idanu na ya kalla na tsawon sakanni uku kafin a hankali naga ya mi'ke tsaye tare da juya min baya sannan yace" Je ki kwanta".