Sashe 124
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki ya ja guntu sannan ya saki labilen ganin na tunkaro sa...nasan bai wuci yayi tunanin zamana da shi zqi takura masa ba shiyasa naga ya wuce ni a 'dan fusace ya 'karasa shiga cikin parlourn batare da ya ko sake kallon inda nake ba.
Yayin da ni kuwa hakan shi yafi komai yimin da'di cuz dan da ganin ya bar bakin 'kofan nayi saurin shigewa ciki, da yake dama ri'ke nake da fitsari...ai su mayafin ma duk watsasu nayi kan bed nayi saurin shigewa bathroom.
Ko da na fito rasa yadda zanyi nayi sallar nayi, gashi sai da na tsaya na watsa ruwa ban kuma son maida kayan da na cire cuz suna da nauyi, gashi ba wasu ban san kayan da zan saka ba a wannan lokacin.
Tsaye nayi ina tunani gami da kalle-kalle cikin 'dakin tamkar zanyi kuka 'kasa-'kasa nace" Waiyo Ammi na dan Allah kizo ki tafi dani...wardrobe na nufa duk da banda tabbacin samun abinda zai min amma sai naji raina ya kwanta da in bu'de 'din, kamar wasa kuwa da na duba sai naga kaya ne jere aciki.
Duk da bansan na wanene ba amma take sai naji farin ciki ya lullu6e ni, abaya ba'ka na ciro na sanya tare da Hijab babba pitch colour da na gani shima cikin kayan rigar kuwa daidai tsayi na tayi min dai-dai, daga haka na wuce kn dadduma na tada sallah ta.
Har na idar na zauna kan daddumar ina karanto Azkar 'din da muka saba yi da Ammi har a lokacin kuma Yah Deen bai dawo 'dakin ba...sai dai banyi mamaki ba cuz daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin T.V na tashi nasan babu mamaki abinda ya 'dauki hankalin sa kenan.
Na 'dauki a'kalla kusan mintina ashirin zaune a wurin kafin na mi'ke izuwa parlourn dan na gaida shi.
Kishingi'de na same shi 'kafafun sar'ke da juna 'daya kan 'daya yayin da ya 'dago su saman kujeran yayi musu masau'ki, hannun sa 'daya ri'ke da remote yayin da gaba 'daya ya bada hankalin sa kan T.V 'din yana kallo.
Ko sallamar da nayi ma da 'kyar in yaji ta ni dai ban damu ba saboda sanin halin sa da nayi.
A hankali na 'karaso nesa ka'dan da shi na zauna na takuru cikin hijabi na...da rawar murya nace " Ina kwana Yayah".
Cikin sa'a kuwawannan karon ya jini duk da yake ma ba da 'karfi sosai nayi maganar ba, amma hakan nai hana shi jin abinda na fa'di ba, na fahimci yajin ne ta dalilin waigowa da naga yayi ya kallo ni, sai dai bai amsa ba gani kawai nayi ya sau'ko da 'kafafun sa ya dire su a 'kasa still kuma suna sar'ke da juna, sai a lokacin ma na lura ashe rigar Jumpan sa na jiya ce a jikin sa har yanzun, sai dai bai saka dogon wandon kayan ba...'dauke idanuna nayi da sauri na mayar da shi 'kasa ina kallon tiles dake 'kasan 'dakin zuciya ta na dokawa, a hankali na sake maimaita gaisuwar da nayi...
Yayin da ya amsa ni da fa'din" Lafiya lau".
Inda ayi maganar ne batare da ya 'dago ya dube ni ba.
Muryar T.V naji ya rage sannan ya dube ni a lokacin yana wani cin magani yace" Ya ma sunan ki?"
" Hudah"
Na bashi amsa a ta'kaice kaina a 'kasa...a 6oye nake ta6e baki cikin raina nake ayyana wannan shi baya ri'ke sunan mutane ne?" Cuz ni dai nasan tuntuni yasan sunana.
Ko da yake ma ai ban ta6a ji ya 'kira ni da sunan ba 'kilan ya manta ne"
Ni ka'dai nayi magana ta kuma na warware ta, har a lokacin kuwa zuciya ta bai bar bugu ba.
" Wani irin suna ne kuma Hudah?"
Shima naji ya tambaya da alamun rainin hankali cikin maganar tasa, idan ka gansa a lokacin zaka yi zaton ko wani abin da bai so aka ambata masa ko kuma irin bai ta6a jin ko da kalar sunan ba.
Baki na na 6ari na amsa shi da fa'din cikakken sunana wato" *NOORUL HUDAH* ..."
" What ever.." ya fa'di yana wani kawar da kansa...." Ni dai ki saurare ni da kyau kiji..kin san waye ni ai ko baki sanni ba?"
" Na sani"
Na bashi amsa a ta'kaice
Yace
" Gud...kar kiga an ha'da ni zama gida 'daya dake kiga kamar kin samu hanyar raina ni ko wani abu, sanin kanki me bazan ta6a 'daukan wannan ba kinsanni... wallahi 6a66ala ki zanyi matu'kar kika ce zaki tsiro min da wani hali, ko kuma kika yi saken da har na ci karo da wani abinda bai game ni ba kin san sauran ba sai na miki bayani ba...Ina nan da hali na da kika sanni da shi wannan Deenin ne har yanzu ban canza ba, dan haka be careful...kar inji kuma kar in gani cewa kin 'dauki magana daga gidan nan kin kai wani wuri dan nasan irin ku 'din nan ba 'kananun munafukai bane...so ki kiyaye ni...ban ce ki samin idanu cikin rayuwa ta ba balle har kiyi tunanin shiga gona ta..bana ma tunanin ba saboda sa idanu aka ha'dani zama da ke ba dan banga abin da zai sa ayimin aure da ke ba in ba haka ba...wallahi kika kuskura naji sunana ya fita daga gidan nan ta 6angaren ki ki kuka da kanki...sannan bansan 'kazanta kina jina ko?..zaman ki anan ma na 'dan lokaci ne da an gama gyaran gidan gaba 'daya zaki koma wani 6angaren daban amma kafin hakan ban son takura sam...dan haka ki kiyaye..kinji ko baki ji ba?"
Da sauri na 'dage kaina sama tare da bu'dan baki nace" Naji.."
" Gud".
Kawai yace tare da sake maida hankalin sa kan kallon da yake yi bai sake bi ta kaina ba.
A hankali na tashi na fita zuwa harabar gidan ganin cewa gari ya riga yayi haske.
Tausayin kaina nake ji sosai yanzu...wai yau gani ga Yah Deen matsayin ma'aurata...sauran sahashin gidan da ba'a kammala 'din ba na tsaya ina kallo..ji nake da ma ayi a kammala gyaran ayau-ayau dan kawai in bar zama tare da shi.
Ban koma ciki ba nayi zama na a waje har lokacin da naji an turo 'kofar gida...da sauri na 'daga kaina sai naga Zaidu kamar daga sama.
Bana shiri da shi amma har ga Allah da na ganshi sai da naji wani sanyin farin ciki ya lullu6e ni...take na washe ha'kora na nufe shi ina fa'din" Zaid".
Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya amsa ni ban damu ba na taho da sauri na kar6i bakset 'din dake hannun sa ina fa'din" Ya su Ammi..?"
" Lafiyan su"
Ya bani amsa ata'kaice sai na sake fa'din" Yah Saif bai zo ba to sai kai ka'dai".
Yace
" Nima 'din Ammi ce ta tilastani wai sai na kawo muku abinci".
Daga haka naga ya fara alamun juyawa sai nayi saurin fa'din " Yayah fa na ciki Zaidu...bazaka gaida shi bane.."
Na fa'di hakan ne kawai dan bani son ya tafi tun yanzu.
Waigo yayi ya 'dan ha'de goshi sannan naga ya dawo da baya ya nufi hanyar parlourn, abaya na bishi hannu na duka biyu ri'ke da basket 'din saboda akwai 'dan nawi..kallo 'daya zaka min ka fahimci fara'ar da nake 'kunshe da shi.
Sallama yayi bakin parlourn yayin da Yah Deen ya amsa masa 'kasa-'kasa kamar yadda ya saba.
'Karasawa yayi ya zauna saman kujera sannan ya gaida shi tare da yi masa bayanin abinda ya kawo shi.
Yah Deen jinjina kai yayi kawai...mintina biyu masu kyau Zaidu bai 'kara ba ya mi'ke da niyar komawa.
Yah Deen na daga inda yake yace da shi" Zaid da mota ka zo ne?"
" Erh" Zaidu ya bashi amsa yana kallon fuskar sa...Yah Deen sai yace da shi" idan kaje ka tambayi Ammi key 'din 'daki na akwai kayana aciki ka kawo min su gaba 'daya..."
" To" Zaidu yace sannan ya juya har ya kusa barin 'dakin sannan Yah Deen ya sake fa'din" Zaid kar ka da'de fa ina jiran ka yanzu please".
Jin cewa zai je ya dawo ne ya sani saurin dakatar da shi da fa'din" Zaid in zo in raka ka?"
Bai tanka ni ba sai ya waigo ya dube ni sannan ya dubi Yah Deen yayin da shi kuma yayi kamar bai san me muke tattaunawa ba.
Fita Zaidu yayi daga 'dakin yana 'ko'karin saka takalman sa nima na bishi abaya kaina har yanzu da Hijabi na...tsakani na da Allah nake so in bishi ni kam...so nake na koma gida...inga Ammi na da Ummah ta.
Ina gab da barin 'dakin najiyo muryar sa yana fa'din" Bani san rawar kai da hauka fa".
Cak na tsaya amma ban waigo ba...sarai nasan da ni yake yi wanda hakan ya sa na fara jin hawaye na taruwa cikin idanu na.
Daga hakan kuma bai sake furta komai ba ina ji ina gani daga inda nake ina hango Zaidu ta cikin labile har ya fice a gidan batare da na bishi ba, abu na 'karshe da naji shine dirin motar sa daga haka na lumshe idanu na take sai hawaye na ya gangaro a hankali..." _Kar ki yadda magana ta iso kunnena cewa kina fita ba da izinin mijin ki ba...koma ni ban ji ba kar ki manta Allah yana kallon ki..kuma baya son mace ballagaza marar kamun kai...duk macen da bata yin abu bisa tsari da koyarwar Annabin mu to azahiri za'a iya 'kiranta da suna ballagaza...kuma banda girman kai Hudah ki riga gaida shi kina yi masa biyayya kar ki yadda ki tsiri mugun hali da rashin kunya cikin zamantakewar ku, idan ma kika yi kece da asara domin darajar martabar ki kike ragewa_ ....."
Kalaman Ummah ta na tuna da tayi min irin su kusan sau uku a 'dan sati biyu da na zauna dasu kafin akawo ni gidan Yah Deen.