← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 211

Sashe 39

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bazan ta6a mantawa ba ranar wata Alhamis da na je gidan da safe, Ummah ce ta aikeni in kaiwa Alhaji Baba sa'kon gidan sa kamar yadda na saba kullum.....

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍
[12/27/2019, 8:16 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

This page is specaially dedicated to👉🏻 *Ummien Diga* naki ne ke ka'dai kiyi yadda kike so da shi...👌🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *20*

Koda naje banji muryar Alhaji Baba ba....haka ma sai naga Ammi duk ta zama wata iri kana ganin ta zaka san tana tare da damuwa, ni kaina sai da naji babu da'di a raina cuz ba haka na saba ganin ahalin gidan ba.

Tun da Ammi ta kar6i abin hannu na ta ajiye akan dinning gami da fa'din " Zaid in kun gama ga breakfast anan".
" toh" yace da ita shikenan ta koma ciki ban 'kara ganin ta ba.

Hatta su Saif ma da kansu suka yi serving breakfast 'din su suka ci...har suka kammala ina gidan kuma Ammi bata fito ba.

Tashi nayi da niyyar tafiya ganin kowa ba kulani yake yi ba yau 'din.

Har zan tafi sai kuma na dawo 6angaren da Zaid yake zaune, nesa ka'dan dashi na tsaya nace masa " wai ina Alhaji Baba yake yau?"

" me ya faru?"
Yace dani cuz dama ba wani shiri sosai mukeyi da shi kamar da Saif ba.

Jin ya sake tambaya ta madadin amsata sai na 'dan ja 'karamin tsaki ciki-ciki, sai na koma gefen Saif a hankali nace " Saif yau me ya samu Ammi?"

Kallona yayi kawai batare da ya bani amsa ba sai kuma ya 'dauke kansa yaci gaba da abinda yake yi.
" Zakiyi late fa better kije kiyi shirin makaranta yafi miki dan bazan hana kowa dukan ki ba yau kam".

Jin hakan ne ya sanya ni ta6e baki gami da mi'kewa na fara tafiya a hankali sai kuma na waigo nace dashi " to ina Alhaji Baba yake ni yau duk ban ganshi ba? Kuma ban gaishe shi ba ma".

Saif ne ya bani amsa da fa'din " sassafe ya wuce Azare Yayan mu bai da lafiya".

" yayan ku?"
Na sake tambayar sa da mamaki dan ni har ga Allah mantawa nake da batun wani wai shi Mu'een a gidan.

Da " erh ai baki san shi ba".
Saif ya sake bani amsa gami da mi'kewa tsaye ya rataya jakar makarantar sa.

Ganin hakan ne ya sanya ni fita nima da 'dan hanzari na na koma gida dan shirin zuwa makaranta ta.

Kwanan Alhaji Baba uku a Azare sannan ya dawo gida bayan ya tabbatar jikin Mu'een 'din da sau'ki.

Wannan karan kam abakin Baban mu mukaji takaitaccen labarin cewa wai ai 'dan Alhaji Baban ciwon zuciya ke damun sa wanda afa'dar likitocin ma wai da abinsa ya girma cuz ciwon ya da'de a jikin sa amma wannan ne karo na farko da ciwon ya ta6a motsa masa dalilin 6ata masa rai da akayi a school abin sai ya bashi haushi sosai, ga kuma club 'din su da sukeyi ma suka sake 'dora wani a madadin sa da yake ya 'danyi zazza6i na kwana kusan tara sanadin targa'de da ya samu a'kafa wajen wasan Ball shine ya ha'da masa harda zazza6i.

Su kuma kamar jira suke dama ya kauce duk sai suka maye gurbin sa da wasu, ya juri wancen bai nuna 6acin ransa ba har suka zana jarabawa.....abinda yafi 'kona ranshi ma shine debate 'din da za'ayi na 'karshen zango wanda duk da yana fama da targa'da'd'den 'kafar amma hakan bai hana shi mai da hankali wajen karancewa da kyau ba tunda jimawa yake bibiyar abin....... abin mamaki ranar ma zazza6i na damunsa amma haka ya matsawa Uncle Ja'afar akan zai zo yaji labarin debate 'din saboda gobene yake saka ran za'a fita na jaha ne kuma, zuwan sa sai ya tarar har an maye gurbin sa da wani tuntuni duk da yake kuwa wancan 'din bawai ya kai sa 'ko'kari bane amma dai mahaifin sa babban mutum ne shiyasa yaron ya maida Mu'een tamkar abokin hamayyar sa a makarantar dan sam baya 'daga masa 'kafa a komai kuma bai isa yace ya kamo 'kafar Mu'een a karatu ba amma haka yake kishi da shi....sai gashi wannan karon yaron na 'daga masa doro dan ya maye gurbin sa wurin debate.....karo na farko kenan da Hayatuddeen yaci nasara a takarar da yake yi da Mu'een.

Koda Mu'een ya nemi ji daga bakin jagoran nasu sai yace dashi ai ya 'dauka ko shi 'din ya fasa ne ganin lokaci na tafiya kuma basu ji daga gareshi ba".
Inda yayi maganar batare da nuna damuwar komai ba.

Mu'een bashi da tsoro shi tun tasowar shi haka Allah yayi sa, dan haka batare da fargabar komai ba yace da malamin " haka mukayi da kai? Ko ni nace maka na fasa?"
Idanun sa har jajaye suka koma lokacin da yake maganar dan tsananin 6acin rai.

Take sai malamin ya juyo gami da dafa gefen kafadar sa yace " kayi ha'kuri zuwa wani lokacin kaji....me kake so kai kam ma yanzu, me kake nema Muhammad?, i thought duk inda ya kamata ace burinka ya cika akan fita debate to ka kai matsayin, in ban manta ba tun kana junior classes ake fita debate da kai toh ina laifi dan ka bawa wani chance wannan karon?
Mahaifin Hayatuddeen da kansa yazo ya ro'ki a sanya Hayat 'din for the first time kaga kuwa da girman sa bazamu bijirewa batun saboda kai ba ko?"

Cikin ido yake kallon malamin tankar wani sa'an sa wanda jin wai Hayat ne ma akasa a madadin sa ya ta6a ransa sosai, yasan kuma ba dan komai hakan ya faru ba sai dan cewa mahaifin Hayat 'din mai yaga Naira ne.....kenan 'karfin ikon Naira aka nuna masa.

Hafsat wannan abin ya 6ata ran Deen sosai fiye da zaton ki....

" Allah sarki"
Hafsat tace cikin sanyin murya yayin da Noor taci gaba da bata labarin da fa' din.....

" Hannun malamin ya sau'ke daga kan kafa'dar sa sannan ya juya batare da ya ce da shi komai ba kawai ya koma gida".

Haushi sosai abin ya bashi fiye da zaton mai karatu sannan bai sanar da kowa halin da yake ciki ba ko Uncle Ja'afar da ya tambaye shi ma cewa yayi dashi kawai wai ai an fasa ne gaba 'daya.

Sai dai ya 'kudura cikin ransa cewa bazai ta6a barin Hayat haka ba sai ya rama, sai ya 'dau fansar abin nan da yayi masa, sai ya 'kuntata masa shima ta yadda zai san cewa bakomai bane Naira ke wakiltan sa, cuz ya san dagangan ne yasa mahaifin sa yazo ya ro'ka masa gurbin sa dan ya kawai ya nuna masa shi ba komai bane, sai dai ta ina....iya tunanin sa bai iya ya tuno abinda zai masa ba sai dai duk da haka bai ta6a cire abin aransa ba........tun faruwar lamarin kuma yake jin 'kirjin sa na yawan mai ciwo lokaci-lokaci...da yake bai san miye bane shiyasa bai damu ba.

Ba'a da'de da yin hakan ba sai ya samu labarin cewa anje anyi debate 'din acan Bauchi kuma makarantar su ce ta kasance ta 'daya wai sanadin Hayatuddeen abin mamaki, wanda har hakan ya sanya suka samu manyan kyaututtuka na ban mamaki daga manya-manyan mutane wanda basu ta6a samu ba, abin sosai zai baka mamaki musamman idan already kasan waye Hayat, mutumin da ko a class kusan kowani semester shike 'daukan second to d last position taya zai iya winning debate din jaha harma kuma ya samu lambar yabo?
amma kuma abin a fili yake domin sai wanda ya sani ne ka'dai zai fahimci cewa mafiya yawan kyaututtukan sun fito ne daga manyan abokan Mahaifin Hayatu.....wanda a fili zaka fahimci manufar hakan ga dukkan alamu yayi ne dan nemawa 'dan sa suna dan kuma ganin ya goge fuskar da'ki'kanci da aka sansa dashi.

Ranar da Mu'een yake da niyyan shigowa makarantar aranar yaci karo da 'kira cikin wayar sa...bai san ko numbern waye ba dan haka koda ya 'dauka shiru yayi........sai ji yayai ance " yane Man har yanzu banga kazo taya ni murna bafa ko ba'kin cikin bai barka ba har yanzu?"

Bai 'kara 6ata lokaci ya saurari komai ba kawai ya yanke 'kiran.

Har ji yayai dama ya fasa shiga makarantar amma kuma idan yayi hakan kamar ya nuna sarewar sa ne dan haka sai ya gama shiri ya ya tafi makarantar.

Amma ko iya zama bai yi ba dan haushi, duk inda ya wulga zancen akeyi, ana yaba 'ko'karin Hayatu bacin shi da suke class 'daya dashi ya san sirrin brain 'din Hayatuddeen tun ba yau ba....amma ya akayi hakan ya faru sam ya rasa.

Babu abinda akeyi cikin makarantar banda hayaniya dan haka sai ya yanke shawarar komawa aji kawai ya 'dan duba takaddun sa cuz gab suke da fara exams.

Dai-dai 'kofar class 'din su yaci karo da Hayat da wasu abokan sa guda uku, bai yi niyyan tanka su ba domin dama can ba magana ce ke hada su ba...take sai suka fara yi masa dariya suna nuna shi " bana an fa'do".
Abinda wani daga cikin su ya fara furtawa kenan yayin da Hayatu yace " an gamu da maza ai...wannan karon ansha kashi.....yaro yaci 'kasa sai ha'kuri".
"....na gaba ma duka za'a sha ai Bahbah".
Cewar wani daga cikin su.

Shiru Mu'een yayi yana kallon bakunan su harma sai ya daina fahimtar abinda suke fa'di...banda 'daci babu abinda yake ji cikin zuciyar sa...
Chapter 39 · 0% Book details