Sashe 168
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yasan cewa ba komai ne yasa Jiddah 'kiran Noor a waya ba face rashin amincewa da batun auren ta da yayi, amma ko anan ma ya matu'kar jinjinawa Nuree, jinjina mai girman gaske, domin ko alama bata nuna masa ba na cewar wata ta 'kira ta saboda shi ba, balle akai ga ta furta masa da bakin ta, shiyasa a kullum yake 'kara bata wani babban matsayi na da muhimmanci na daban cikin zuciyar sa, soyayyar ta a kullum sake ratsa shi yake yi, ba zai ta6a iya ha'da soyayyan Nuree da kowa ba a fa'din duniyan nan, shi dai barshi ya hole yaji da'din rayuwa in a waje ne amma babu batun aure kam ya gama sawa cikin ransa cewar Nuree ta ishe sa rayuwa, ko shayin fa'dar hakan ba ya yi ga kowa wanda yake kyautata zaton dan hakane Jiddah ta tanadi wannan Videon dan kawai ta tunzura zuciyar Nuree akan sa, ta muzanta soyayyar dake tsakanin su, ta wargaza tubalin ginin 'kaunar sa dake cikin.zuciyar Noor.
Zaton Jiddah ko Noor bata san asalin halin sa ba, ta 'dauka duk a munafurce yake komai...bata san Noor mace ce da ko wani namiji yake burin samun irin ta ba, da kansa yasan ba wayon sa bane ya bashi Noor matsayin mata face ya bashi ita ne kawai saboda yaji 'kansa, Noor mata ce ta rufin asiri abin so ga kowa.
Shi kansa ma bai san mai yasa ya nemi Jiddah ba tun farko, yasan lokacin da ya nemi Yusrah laifin Nuree ne bayan ya yiwa kansa al'kawarin zama da ita ita ka'dai cikin ko wani irin hali amma daga baya Nuree sai ta fara gudun sa tana gudun bu'katun sa, shikuwa mutun ne da baya da juriya ta wannan fannin hakan yasa ya karyawa kansa al'kawari, amma Jiddah kam yasan son zuciyar sa ne kawai ya kaisa gare ta ba komai ba, sharrin shai'dan ya ja shi ga kusantar ta, gashi ta kai shi ta baro shi, ta kunna masa wutan da yasan kashe shi zai matu'kar wahal da rayuwar sa, tunda har yau Nuee ta iya duban tsaban idanun sa ta gaya masa magana son ranta yasan cewa ha'kurin ta ya 'kare ne, sosai ya kaita bango ta yadda shawo kanta zai yi masa wahalar gaske...sosai yake jin haushin Jiddah da ma shi kansa gaba 'daya.
A ganin sa Jiddah hauka tayi ba komai ba, dan shi ko ma mai zai faru bai ga abinda zai sa ya aure ta ba, abu mafi muni da ta aikata masa shine ba'kanta zuciyar Noor da tayi, hakan matu'kar ta6a shi, bata san cewa Nuree itace mutun na farko da zata iya bada shaida akan 6oyayyan halin sa da ba kowa ne ya san shi da shi ba amma ta ruaf masa asiri, itace mutun na farko da ta ganshi da mace ra'ayil ain kuma ta rufe maganar duk da hakan ma kuma ta 'kara ha'kurin zama da shi har ta haifa masa Baby sanyin ransa.
Wa'dannan dalilan ka'dai aganin sa sun isa susa ya ji tafi kowacce muhimmanci agare sa, bazai ita6a iya ha'da ta da kowa ba dan ta cancan fiye da hakan ma...matar sa mai ha'kuri ce, kawaici da sanin.ya kamata, baya tunanin har abada zai sake yin sa'an samun irin ta cikin mata...'kaunar da yake mata shi da kansa bazai iya misalta shi ba, a yanzu bashi da burin da ya wuce ya faranta mata koda kuwa hakan na nufin 'karshen rayuwar sa ne.
Cikin ramsa yake jin cewa matu'kar ta za6i rayuwa babu shi a yanzu yayi al'kwarin barin ta, ba zai matsa mata ba, ba zai sake tilastata zama da shi ba koda kuwa shi 'din hakan na nufin cutar wa agare shi..koda zai rasa rayuwar sa yayi wannan al'kawarin for the first time zai sata farin ciki madadin farin cikin da ta sashi abaya, zai barta da Baby kamar yanda ta bu'kata amma kafin hakan yana so ya sake ganin Babyn sa, yana so ya sake neman yafiyar Nuree ko zai yi sa'a ta yafe masa.
Yana so ya gaya mata cewar ba da yaddan shi Jiddah ta tura mata wancan Videon ba, sam bai isa ya 'karya ta batun kusantar Jiddah da yayi ba dan yasan Nuree tasan halin sa zai aikata fiye da hakan ma dan haka ba zai sake yi mata 'karya ba...amma ta sani cewa ba da sanin sa Jiddah ta tura mata ba.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *78*
Zaune ya tashi yana kallon 'dai'daikun mutane da ke wucewa lokaci zuwa lokaci wasu na shiga yayin da wasu ke fita, kowa fuskokin shi na tafiya ne da yanayin sa, idan yaga mutun na farin ciki sai yaga kamar shi bashi da damuwar komai ne, ji yake dama ace shine yake wannan farin cikin, yayi Allah wadai da rayuwar sa yafi a 'kirga, idan ya tuno Baby kawai sai ya rintse idanu, tausayin yarinyar yake ji sosai.
Yasan da ace tasan halin sa zai iya ja mata wannan abin da ko abaya ma bazai samu ko quartern 'kauna daga gare ta ba, amma yarinyar sosai take ji da shi matsayin sa na mahaifi agare ta amma bai yi wa rayuwar ta adalici ba sam...Allah sarki Mama na, ki yi ha'kuri, ki yafewa Daddyn ki ba dan ya na da wanna matsayin sa ba.
Dishi-dishi yake gani idanun nasa zogi sosai suke yi masa, kansa ciwo ga kuma 'kirjin sa dake barazanar tarwatsewa...shi ka'dai yasan me yake ji a jikin sa...banda yafiyar Ubangiji babu abinda yake iya furtawa.
A duk lokacin da ya tuno ta'asar da ya tafka a fili zakiji ya furta _Astaghfirullah_ ...lokaci- lokaci yake furta hakan tamkar zautacce.
Ya 'dauki tsawon lokaci a ahakan kafin ya koma da kansa ya kwantar...ya cigaba da danasanin rayuwar sa kaf.
*****
Misalin 'karfe sha 'daya da rabi su Alhaji Baba suka iso, duk neman da Safwan yayi wa Mu'een cikin asbitin amma bai gansa ba, yayin da hankalin mahaifan sa ya 'kara tashi sosai fiye da ganin Jasmine da suka yi da halin da take ciki.
Tsoron su kar wani abin ya same shi a inda babu wanda ya sani dan tun jiyan Safwan ya sanar da su halin da shima yake ciki..shiyasa hankalin su ya kasa kwanciya.
Yayin da Safwan kuma ke fargabar kar mahaifan nasa suga kamar bai ri'ke musu amana bane cuz Jiyan a hannun sa Alhaji Baba ya mi'ka ragamar komai a fa'dan sa wai kafin su iso.
Sai gashi sunzo in kuma babu Mu'een babu alamar sa.
Ammi kam kuka sosai take yi dan harga Allah hankalin ta bai kwanta ba, gashi sunzo kuma suna tarar da jikin Baby yayi tsanani, ko ganin ta da kyau ma basu samu daman yi ba aka fito da su waje likitoci biyu Safwan da wata Nurse suka tsaya akanta...shikansa hankalin rabe yake gida biyu ciz yasan duk inda Mu'een yake to cikin wani matsanancin hali yake.
Jikin Baby sai rawa yake yi ga wani zazzafan zazza6i da ya taso mata lokaci guda, takan 'dan fizgi jikin ta lokaci zuwa lokaci kamar mai razana da wani abu.
Noor ma kuka kamar ranta zai fita, haka ma Ammi da abin ya zame mata biyu ga rashin ganin Mu'een ga kuma jikin Baby da yayi tsanani, tasan jinyan Baby ne ya tashi hankalin Mu'een shiyasa yayi nesa da inda suke, dayake tasan irin 'kaunar da yake mata, duk wanda yasan Mu'een to yasan irin soyyayar dake tsakanin sa da Jasmine ba na wasa bane, wanda ko wani irin hali ya shiga saboda ita ba abin ayi mamaki bane, gashi tasan yanda yake fama da ciwon sa idan ya motsa masa sosai hankalin ta ya tashi ta kasa natsuwa, Alhaji Baba ka'dai da Mummyn Safwan sune masu 'dan natsuwa har ma suke iya basu ha'kuri...Noor ma ba'a cewa komai.
Safwan na gamawa da Baby ya fito ya 'kara kwantar musu da hankali da tabbacin komai zai daidaita da iznin Allah sannan yayi gaba dan shima zuwa lokacin hankalin sa ya tashi sosai, har gida yaje ya duba amma bai tarar da Yah Deen ba, sam ya rasa ina ya tafi a ina zai same shi, gashi kuma motar na nacan a Parking space cikin asbitin inda ya ajiye tun jiya anan take bata motsa ba.
Hanyar office 'din sa ya nufa yana tunanin a ina ya kamata ya neme shi, da shigan sa sai ya 'dago wayar sa ya gwada 'kiran layin Yah Deen Amma shiru bata shiga.
Tunowa yayi da lokacin da Yah Deen ya kar6i wayar sa da key 'din motar da safe a wurin sa.
Fita ya sake yi cikin sauri da wani tunani a ransa...Addu'ar sa Allah yasa hasashen sa ya kasance gaskiya.
Yana zuwa jikin motar Yah Deen 'din sai ya tsaya yana duban motar ko.zai ga alamun mutun a ciki amma baiga wani alama ba saboda tinyed glass in dake lullu6e da motar.
Motar da ya siyawa Baby na zuwa makaranta ce dan tashi na Abuja yayin da ta Noor kuma na can ta zama wani abu sanadiyyan accident 'din da akayi da ita jiya.
Gwada bu'dewa yayi amma yaji a kulle, dum.zuciyar sa ta tsinke tsoro y kama shi, in dai akace Mu'een ba yanan to ina ya shiga?
Ya tambayi kansa.
Bashi da tabbacin yana ciki amma sai ya 'kwan'kwasa da fatan Allah yasa yaga an bu'de masa.
Yah Deen tsayawa yayi yana 'kare masa kallo daga cikin da yake, bai so zuwan sa a wannan lokacin ba sam.
Safwan cigaba yayi da 'kwan'kwasaw yayin da Yah Deen yayi luf ko motsin kirki bai yi ba balle asaka ran zai tashi ya bu'fe masa.