← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 211

Sashe 100

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya cigaba da rayuwar sa cikin 'kunci da damuwa kan auren da ake shirin yi masa, ya kan shiga school amma ba kullum ba sai ranar da ya ga daman hakan, su Ishaq ma yanzu na yawan zuwa gidan duba shi musamman idan suka ga shiru bai shiga school 'din ba, cikin hakan har suka samu Mu'een ya bayyana musu damuwar dake damun sa wato auren da mahaifin sa ke shirin yi masa sai dai bai fa'da musu ko wacece ba dan shima bai gama tabbatar wa ba tukunna.

Ishaq sun matu'kar tausaya masa amma hakan bai hana su bashi 'kwarin gwiwa akan kar ya bijirewa mahaifan sa ba ya daure yayi musu biyayya 'kila sai yaga auren yayi albarka ya kuma zame masa abin alfahari.

Yah Deen kam jin su kawai yake yi wani lokacin kuwa sai yayi murumushin takaici da gefen bakin sa..." Wai auren sa da Husnah ne zai zame masa abin alfahari"
In ji shi yace" Banga alama ba".

Duk da ko da ace a giyar wake itace abincin sa a kullum dama bai isa yace zai ja da maganar Alhaji ba, zai nuna baya so cikin harkokin sa, zai iya sanar da Ammi bai so, haka ma Uncle J musamman da ya fahimci cewa har a lokacin bai san labarin asalin abinda ya faru ba...Amma ga Alhaji Baba kam...a a dole ne zai yi masa biyayya ko ma dan kar ya 'kara masa 'kunci kan wanda ya 'kunsa masa abaya.

Wani sa'in ha'kuri kawai yake yi amma baya son zuwan da su Ishaq ke yi gidan sa gani yake suna takura masa ne sosai.

A hakan ma wataran da gangan yake rufe 'kofar ta ciki yana jin su suyi ta bugawa amma motsin kirki bayayi balle asa ran zai tashi yaje ya bu'de musu....ya kai kusan sau biyu hakan na faruwa haka zasu zo su koma batare da sun ha'du dashi ba duk bugun da zasu yi wa 'kofar gidan kamar babu wani abin halitta mai rai dake rayuwa cikin gidan baza'a bu'de musu ba, haka zasu ha'kura su tafi suna masu trying layin sa amma har lokacin bata shiga bai ko tattare wayar a inda ta fa'di ba balle aje ga batun kunna ta..Ishaq kuwa har ransa dan su ringa rage mai yawan tunani ne yake sanyawa gayyato su Imran su taho.

Mu'een kam bai ko damu da yawan mutanen da ke neman layin sa basa samu ba, duk da yasan dole dama za'a neme shi, musamman Ammin sa da Uncle J, amma ya zam masa dole ya nuna musu 'karara shi ba ya son auren nan, wanda ganin sa hakan ma ka'dai ya isa ya bayyana meke cikin ransa.

To Husnah fa da sauran mutanen da zasu neme shi? Wa'dannan duk basu dame shi ba kwata-kwata, bai ma sasu cikin tunanin sa ba, in sun gaji da neman layin nasa kowa ya ha'kura kawai..acewar sa.

*****
   Kamar yadda aka tsara... sati na cika su Alhaji suka koma shi da Uncle J da yake har ranar bai koma ba inda suka tafi da duk wani da duk wani da suka san za'a bu'kata ranar...bayan ganawar su da Alhaji Mamman sai aka sanya lokacin biki sati uku masu zuwa kacal...Uncle Ja'afar ne ya biya sadaki dubu 'dari cif   sannan suka koma gida.

Uncle Ja'afar kam washe garin da aka basu auren yayi shirin sa tsaf domin ya tattara ya koma Jalingo a fa'dar sa wai sai lokacin biki ya 'karato sannan zasu dawo da iyalin sa cuz shi zai kar6i auren matsayin waliyin Mu'een.

Shi kansa ya damu da rashin samun Mu'een a waya duk da ma ya san iskanci ne ya sashi rufe wayar tasa amma duk da haka ya kasa daurewa da da hakan.

Da farko ya so ya share shi amma zuciyar sa ta kasa aminta hakan tausayin Mu'een ya fara kama shi, dan zuwa yanzun ya fara yadda cewa ba da yardar sa Alhaji Baba ya shirya wannan auren ba.

Wannan tunanin ne ya sa shi yanke shawarar sake komawa Jigawa ya ganshi kafin ya wuce amma Alhaji Baba bai bashi damar hakan ba yayi masa katsalandan da cewa zasu je Jos tare da shi su duba Gidan gonar Alhajin dake can in yaso daga Jos 'din sai ya wuce abinsa Taraba.

Hakan kuwa akayi dan tare suka yi tafiyar suka dira Jos wurin Baban mu, inda suka tarar abubuwa na tafiya normal babu matsalar komai, sosai Baban mu ke 'ko'kari wajen kulawa da amanar da aka dan'ka masa.

Da yaji labarin batun auren Yah Deen kuwa cikin farin ciki ya ringa sanya albarka yana fatan Allah ya nuna musu lokacin suna cikin rayayyu.

A ranar Uncle J ya wuce Taraba yana mai sake dialling number Mu'een amma baya samu zuwa lokacin kuwa abin nasa sosai ya fara bashi haushi,  dan haka sai ya yayi fushi ya share sa bai ko sake gwada 'kira ba har ya isa gida.

Alhaji Baba kam kwanan sa 'daya ya dawo gida cikin farin cikin yanda yaga dukiyar sa na 'kara habbaka wurin Baban mu...wanda kafin rabuwar su Baban mu sai da yayi alkawarin insha Allahu kafin ranar auren zai zo ayi komai da shi Alhaji Baba sosai yaji da'din jin hakan kuwa duk da cewa shima auren ba wai ya kwanta masa bane amma gani yake yiwa Yah Deen auren shine babbar mafita saboda gudun fitinar shai'dan da kuma abinda zai biyo baya.

Lamarin da ya matu'kar 'daga hankalin Husnah shine jin wai ansa ranar bikin ta kuma kwanaki 'kalilan, ba 'karamin tada hankalin ta hakan yayi ba gashi har a lokacin ta kasa samun sa a waya balle taji ta tabbatar da cewa shi 'din ne ko kuwa wani daban ba.

Abin ya dame ta sosai, gashi Abbah ya hana ta komawa Jigawa wai har sai bayan bikin, badan haka ba ai da taje sun magantu da shi, fitan kirki ma yanzu bata yi Alhaji Mamman ya hana ta zuwa ko'ina. 

Da farko kamar abin bazai dame ta ba amma daga baya har kuka take 6uya tayi cikin 'dakin ta bayan ta kulle gudun kar mahaifiyar ta ta ganta tana kuka damuwar ta ta ninku.

Wasa-wasa sai da aka share kwanaki goma da dawowar ta amma har ranar bata samun layin sa.

*****
       Yanda yaga Ammin sa cikin mafarkin sa na jiya da dare tana kuka da hawaye tana bin sa da idanu ne ya sanya duk jikin sa yayi sanyi 'kalau, har bayan ya idar da sallar asubah ma ya kasa warwarewa, photon scene 'din ya kasa barin kwanyar sa.

Yanzu ne ma yaga rashin kyautawar sa da yayi watsi da tunanin halin da mahaifan sa zasu shiga na rashin jin sa da basu yi ba...musamman Ammin sa da Anty Zainab ga kuma Uncle Ja'afar da yasan cewa sun fi kowa damuwa da shi, Alhaji Baba ne ka'dai bai sa ran zai neme shi ba saboda abinda ya faru kwanaki.

Jikin sa sanyi 'kalau ya isa ga wayar tasa inda ya watsar duk tayi 'kura kasancewar tun bayan tafiyar Husnah gidan bai sake samun gatan shara ba ko'ina in ka duba zaka gansa futu-futu illah bedroom 'din sa ne yake iya kintsawa shima 'din dan acan ya fiye zama ne shiyasa, ranaku 'da'dai ku ne zaka gansa kwance a palourn sa.

Ko da ya rufe wayar ya kunna ta sai yaga babu caji sannan fuskar wayar ya tsatstsage, mi'kewa yayi ya isa ya saka wayar a caji tare da zama gefen ta ya rafka uban tagumi yana bin wayar tasa da kallo zuciyar sa fal da tunanin Ammin sa.

Tsawon mintina 30 yana a haka sannan ya cire wayar yana 'ko'karin shiga dan 'kiran Ammin yaga duk bata 'daukan hannun sa saboda fashewar da tayi, da 'kyar ya samu da dabara ya yi dialling numbern nata tare da 'kara wayar akunnan sa yayi shiru yana jiran ta 'daga.

Ringing biyu ana uku sai aka 'daga tamkar dama zaman jiran shigowar 'kiran nasa akeyi...dan Ammi yanzu bata ta6a yin nisa ta bar wayar ta.

Shiru Ammi tayi duk da irin jin dadin da ya shige ta da ganin kiran sa yau a wayar ta, sai da yayi sallama sannan Ammi ta amsa masa ciki-ciki kamar dole aka sanya ta amsawa.

Gaida ta ya fara cikin kwantar da murya da tunanin 'karyar da zai shirga mata akan rashin samun sa da ba'a yi ba tsawon kwanaki...sai dai kafin ma ya 'karasa furta gaisuwar Ammi sai tayi saurin dakatar da shi da harshen su na Igbo tace" Sai yau ka ga daman tunawa da ni kenan ko Muhammad?"
Da sauri ya girgiza kansa tamkar a gaban ta yake tare da fa'din" Ba haka bane Allah Ammi...am sorry..wayar tawa ce ta lalace amma Ammi believe me kullum kuna cikin raina".
Inda ya bada amsa cikin harshen Hausa kamar yadda ya saba a duk lokacin da tayi masa yaren Igbo baya ta6a mayar mata amsa da yaren sai dai ya canza harshe zuwa wani yaren daban turanci ko kuma Hausa.

Tun lokacin da naji 'karar ring 'din wayar Ammi na farka daga baccin da nake yi har tazo gefen bakin gado ta zauna tana amsa wayar da hannun ta 'daya a 'kirji..ido kawai na tsura mata da son jin da wa take wayar domin babu mamaki 'daya daga cikin yaranta ne da yake duk basa gida a lokacin.

Sai dai jin da nayi ta ambaci suna Muhammad yasa na gane da wanda take wayar kasancewar mutun 'daya tak nasan take 'kira da wannan sunan baya ga shi kuwa sai dai wani daban can da ba 'dan gidan ba.
Chapter 100 · 0% Book details