Sashe 106
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka kawai Alhaji Baba ya fa'di sai ya yanke wayar batare da wani dogon 'karin bayani ba , take kuwa Uncle J ya 'kira shi inda yace" Wai Mu'een me ke damun ka ne? Wallahi idan baka daina yiwa Alhaji irin halin kan nan ba Ubanka zaka ci awaje na, ko an gaya ma shi 'din abokin wasan ka ne?"
" Yi ha'kuri Uncle..."
A tsawace ya dakatar da shi da fa'din" Shut up da Allah ban san wannan ha'kurin ni...kuma maza ka 'kirashi ka bashi ha'kuri sannan ka aikata abinda ya saka ka banson iskanci".
" Uncle wai fa in tafi Shuwarin yace kuma naga ai bikin da saura sannan ina so ne mu tafi tare da friends 'dina shine fa ban tafin ba har yanzu".
Ya fa'di hakan ne da tabbacin laifin da yayi wa Alhaji Baba kenan dan yasan abinda ka'dai ya aikata kenan shine rashin tafiyar sa a dai-dai lokacin da Alhajin ya bu'kata.
Uncle Ja'afar kam cewa yayi" Koma dai menene bansan wani excuse 'din ka, maza kayi abinda ya saka, in banda ma rashin wayon ka hakan da kake yi shi zai sa ya fasa 'daura maka auren ne, kai kanka kasan da kai ko babu kai auren nan kamar anyi shi an gama ne...so kama nutsu kasan me kake yi...wallahi kar ka yadda 'kafata ta riga 'kafar ka taka Shuwarin...in ba ka yadda ba kuma try me an see d real me".
Ji yayi tamkar ya fasa ihu saboda takaici, haushin sa 'karuwa yayi akan nada ma, to shi me ze je yayi musu tun yau da bikin ya rage saura har kwanaki biyar? Shi ba mace ba balle ace zai fara shiri...yana cikin tunanin nan yayi dialling number Alhaji Baba...amma bai 'daga ba, har sai da ya jera masa 3missedcall sannan ya tsaya da wayar a hannun sa yana kallo, shi da kansa ya san ya 6atawa mahaifin sa rai matu'ka amma ya zai yi.
Text ya rubuta ya tura masa da fargaban mai ze biyo baya kuma...'kila yace na raina shi ne shiyasa nayi hakan...ya fa'di yana dafe goshin sa.
Alhaji Baba na kallon wayar sa na ta rurin neman agaji amma bai 'dauka ba saboda yanda yake jin haushi har cikin ransa, baya son ya zama mai zafin rai amma Mu'een na tunzira shi cikin kwanakin nan, text 'din da ya shigo masa ne ya sashi 'daga wayar ya duba nan yaga Yah Deen ne ya turo" _Alhaji dan girman Allah ka gafarce ni...abokai na nake jira mu taho tare shiyasa banzo akan lokaci ba, amma da iznin Allah gobe ina hanya_ ".
Idanu ya lumshe bayan ya gama karantawa sai ya 'dora wayar saman 'kirjin sa, cikin zuciyar sa yake addu'ar" _Allah ubangiji kar ka jarrabe mu da fitinannun 'ya'ya wa'danda zasu datse farin cikin mu a lokacin da bama zato...Yah Allah ka shirya min Muhammad ka daidaita min hankalin sa wuri guda ya Allah_ ".
Bai bu'de idanun ba ya cigaba da tunanin sa, shi ada ya san Mu'een ba haka yake ba, sam baya mishi taurin kai akan abu, mutun ne shi mai matu'kar biyayya da sanin ya kamata, ga shi da girmama iyayen sa, amma sam yanzu halayyar sa ta bambanta da na baya bai kuma san me yasa abubwan sa ke 'kara rikicewa haka ba.
( Ni kuwa nace sharrin Alafasha ce tsantsa Alhaji, ta kan canza mutun daga nagari ya koma gur6atacce in ba'ayi sa'a bama har ta kan 6ata wa mutun 6angaren ibadun sa..ALLAH YAYI MANA TSARI DA AIKATA ALFASHA).
*****
Ran sa be so ba amma haka washe gari ya shirya ya tafi bayan sun yi sallama da su Ishaq akan cewa ranar thursday zasu taho suma.
Ko da yake cikin mota ma tunanin auren sa da Husnah yake yi, ta yadda abin ya fara, ya tsinewa randa ya fara sanin Husnah fin sau 'dari a rayuwar sa, gashi duk da irin kashedin da ya mata hakan bai sa yaga 'kiran ta da albishir 'din an fasa auren ba, yasan dama da wahala ta iya sa afasa auren...sai dai in hakane kuwa shima ba zai ta6a janye 'kudurin sa ba.
Cikin sa'a sai suka dira rana 'daya da abokin sa Imrana, sai dai basu ha'du ba dan Mu'een can gidan Alhaji ya sau'ka yayi wani kalar tausayi a wurin Ammi, ita kam Nasiha kurum ta ringa yi masa tana sake bashi 'kwarin gwiwa akan lamarin, haka ma Anty Zainab dan zuwa lokacin ta gama fahimtar cewa auren daga Alhaji Baba ne ba za6in Mu'een ba, itama jan hankalin sa tayi sosai akan ya daina damun kansa, ai shi namiji ne kuma shine da ragamar auren da gidan ma complete, tace kana da damar 'kara wata matar a duk lokacin da kayi niyyah babu mai hanaka, 'kaddara kuwa babu yanda zaka yi da ita, idan tazo dole ne ka kar6e ta tunda ba'a guje mata ko a ina dan haka ka 'dauki wannan auren matsayin 'kaddarar rayuwar ka".
Jin su kawai yake yi bawai dan ya 'karyata abinda suke fa'di ba a a, kawai dai shi baya jin zai iya ha'kurin ganin Husnah matsayin mata agare shi ne.
Yayin da Alhaji Baba daga gaisuwa babu abinda ya 'kara ce masa sunyi zaman a 'kalla mintina kusan goma a haka sannan Yah Deen ya yun'kura, har ya tashi zai tafi ma sannan yaji Alhajin na fa'din" Hope kasan meke faruwa ko Muhammad?"
Komawa yayi ya zauna yana mai jinjina masa kai alamar " Erh ya sani"
Ya na ji cikin ransa cewa da wani daban ne yayi tambayar da ko kallan shi ma ba zai yi ba balle har ya bashi amsa.
Alhaji cewa ya sake yi" Masha Allah...to sai kaje ka cigaba da shiri..ranar friday insha Allahu za'a 'daura auran ka da Asma'u..sai dai bansan ina zaka fi son matar ka ta zauna ba...kaga wancen gidan ba'a kammala gyaran shi ba za'a ha'da da filin bayan duk agina shi aikin da saura sosai, sai dai in ko can makarantar zata tare idan hakan yayi maka".
Kansa 'kasa ya amsa da fa'din" Ba damuwa Alhaji duk yadda kace haka za'a yi insha Allahu". Inda ya bashi amsa da sanyin murya kamar gaske.
Alhaji Baba kam kai ya jinjina masa tare da komawa baya ya kishingi'da abinsa harda lumshe idanu, wanda hakan da yayin shine ya alamtawa Yah Deen cewa ya sallame sa.
Fita yayi yana tunanin a can Jigawan ma sai yafi masa cuz zai fi samun isashshen daman da zai hukunta ta son ransa dan babu su Alhaji, Ishaq kuwa a ganin sa 'karamin alhaki ne bai damu da shi ba...musamman ma da ya san ba wuri 'daya suke rayuwa da shi ba.
Duk nasihar da akayi ta masan abanza ta tashi, duk ya watsar babu wanda ya zauna kansa, shiyasa yake jin 'kudurin sa na nan cikin ransa babu abinda ya ta6a shi, kaf laifin akan Husnah ta 'daura sam bai ganin nasa, hala ya manta cewa tun ranar farko shine ya fara tattaki zuwa 'dakin baccin ta, ya manta a
Shi ya fara kawo mata batun cikin rayuwar ta shiyasa yake so ya hukunta ta ta yadda zata san babban kuskuren da ta tafka na yadda da tayi ta aure shi despite warning 'din da ya mata amma tayi kunnen uwar shegu da shi tace taji ta gani a hakan zata aure shi.
Bai san cewa itama ta daure zuciyar ta bane kawai saboda kar aci mutuncin mahaifiyar ta a banza da wofi shiyasa ta yadda zata aure shi ko da bayan auren kasheta zai yi akawo gawar ta ga mahaifiyar ta hakan yafi mata fiye da ace ganin idanun ta mahaifiyar ta ta shiga 'kunci ta dalilin ta.
*****
Da yamma lis ya koma gidan sa, nan ya tarar da canjin da aka yiwa gidan, an fa'da'da shi sannan aka tada wani tsari mai kyau ginin zamani sai dai ba ai komai a ginin ba tukunna, haka ya shiga asalin side 'din da yake anmfani da shi dan aikin bai iso kansa ba tujunna, iya abinda zai iya ya kimtsa kafin zuwa safiya kuma yasan yadda zai yi da sauran aikin.
Tun daren ranar suka yi waya da Imrana nan suka sanar da juna cewa suna Shuwarin...washegari kuwa sassafe Imrana ya iso gidan zuciyar sa fal farin ciki har fuskar sa na nunawa...Yah Deen na ciki jin sallamar sa ne ya sashi fitowa ya bu'de masa 'kofar palourn sannan ya bashi hanya domin ya shigo inda ya koma saman kujera ya zauna yana sakin ajiyar zuciya.
Nan take Imrana ya fara zuba masa uban kirari yana daga tsaye yana zuba smilling ya wani 'daga hannu gaban sa tamkar yana gaban wani basarake yake cewa" Woo sai kayi nawa, kamili uban 'yan iska, na Alhaji baka yaudara sai dai horo, sai kai bindiga mai kauda abokin gaba, ka zarce Ak47 sai dai 48, gaye uban mazajen duk duniya, sai kai nuclear tarwatsa dukkan taro...kyautar ka ta musamnan ce ta zarce ta kowa...mai kyau mai hali kyakkyawa....".
Murmushi Yah Deen yayi masa batare da ya furta komai ba.
Yayin da Imrana ya buga tsalle ya yiwa kansa masau'ki kan kujerar dake facing da inda Mu'een ke zaune sannan ya sake fa'din" Kafa ha'du gayen nan gaskiya ka iya shirya mugunta, yanzu dai kace ka bamu dama mu fara shirin ra'kashewa kenan ko?"
Yana murmushi yace" Sosai ma, ai ku kwantar da hankali kawai nake gatama kowa zai shana, zaka iya gayyato abokan ka ma in sun shirya".
Dariya Imrana yayi wannan karon tare da bashi hannu suka tafa cike da jin da'di.
Sai da suka gama shan hirar su kafin suka yi aikin gidan tare...Inda Yab Deeb ke yj yana sakin tsaki...a fili ya furta" Ammi na ta hana 'yar ra zuwa min aiki ai da yanzu ina hutawa ta".
Da jin haka Imran sai yace" Ai da kayi auren shikenan ka huta da irin wa'dannan aiyukan matar ka duk zatai maka..."
Wani harara da Yah Deen ya jefa masa ne ya sashi saurin canza magana inda yana 'yar dariya yace" Aww na manta ma ashe ramu ce matar".