Sashe 130
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka take amsa masa gaisauwa faram-faram su kuma sha hirar su amma ko da wasa bata ta6a sako sunana a cikin zancen su.
Zancen waya ma nake so in tunawa Ammi zancen da tace zata sa a siya min amma ina tsoron kar tace ai ban kwantar da hanakalin nawa ba tunda nace ni gida zan dawo, ita kuwa ina ganin kamar ta manta ma da batun, hakan yasa nima 'din dole nayi shiru na barwa lokaci kawai inda rabo na nasan wataran da kanta ma zata sai min in dai Ammi ce ba ma sai na tambaya ba.
*****
Bayan tafiyar Yah Deen da Sati uku wani tashin hankalin ya sake faruwa, domin kawai wayan gari akayi Ma'u bata raye Allah ubangij ya amshi abin sa bayan tasha uwar rashin lafiya, tunda ta samu cikin nan bata samu nutsuwar kanta ba...ranar nasha da naji labarin mutuwar nasha kuka sosai, kuka kamar raina zai fita, bazan manta ba yanda nayi ta damuwa da son zuwa dubata amma aka hana ni, bacin ina jin labarin wahalar jinyar da take sha a bakin mutane 'yan makarantar mu.
A kullum tausayin ta 'kara kamani yake yi, bayan uban gorin da ake binta da shi agida cewa ta bi ku'di ta lalata rayuwar ta, haka ma duk ranar da Alhaji Baba ya aika mata da kayan marmari da kaji ko 'yan ku'di ta kan yini cikin bakin ciki na gori akan ta, gashi ko iya cin abincin ma bata yi bata iya cin komai da ta ci zata harar...maltina ka'dai ne ke iya zama acikin ta shima 'din babu wanda yake siya mata cuz ko Alhaji ya aiko ku'di bata ganin idanun su, babu wanda ya damu da lafiyar ta balle yunwar cikin ta, ga tsananin wahalar laulayi ga zazza6in typhoid da ya sako ta a gaba...a kullum kuka ne aikin ta, yau gashi ta bar mana duniyar ta koma ga mahallicin ta.
Alhaji Baba yayi namijin 'ko'kari wajen ganin ya kula da lafiyar Ma'u, saboda yasan koma menene ya same ta 'dan sa ne sanadi.
Akwai ranar da ya kawo mota ma da kansa yace akai ta asbiti dan lokacin bata da lafiya amma daga ranar ba'a 'kara sanar da shi rashin lafiyar ta ba.
Shi 'din kuma yanzu baya zuwa gidan nasu sai dai kawai yayi aike koda, ya Deen yazo ma bai damu ya sashi zuwa wajen ta ba dan ya bari ne akan idan ta haihu dole maganar auren su ta taso.
Allah cikin ikon sa sai
lokaci 'daya kawai ya amshi ran baiwar sa.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_🎑🎆🌙Barka da sallah to d all Ummah...Taqaballahu minna min kum...ubangiji Allah ya maimaita mana shi da Alkhairi_ 🙏
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *63*
Tsanar da naji ta Yah Deen cikin zuciya ta a lokacin ni kaina ban san iya adadin ta ba...ban ta6a jin na tsani mutun sama da yanda nake jin haushin sa a lokacin ba.
Ji nake tamkar duk duniya baza'a ta6a samun mai mugun hali irin nasa ba, saboda duk lokacin da tunanin sa zaizo raina baya ta6a zuwa min da Alkhairi, shiyasa nake gani kamar nasa halin na musamman ne.
Yau gashi sanadin sa Ma'u ta ta rasa ranta, ta tafi tafiya irin ta har abada, ta tafi ta bar duniyar cikin 'kuncin zuciya..ni da kaina a lokacin na yi fatan Allah ya saka mata zaluncin da aka yi mata sau babu adadi...ban sani ba ashe sakayyar har da ni ma da nake tare da shi zata shafa...Hafsat dubi abinda aka yiwa yarinya ta dalilin mugun halin sa, Jasmine 'di na....bata iya ta 'karasa maganar ba kawai ta sunkuyar da kanta ta sanya kuka mai matu'kar tsuma zuciya.
Hafsat kanta sai da ta share hawaye amma gudun kar a rasa mai lallashin wani a cikin su ya sanya itan ta daure ta shanye nata kukan ta bawa Noor ha'kuri cikin nuna mata ai komai dake faruwa da bawa 'kaddara ne, duk abinda ya samu bawa to rubutacce ne tun kafin ya zo duniya 'kaddarar sa ta zanu..shiyasa ake so bawa yai imani da ko wace irin 'kaddara idan ta same shi mai kyau ce ko kuma akasin haka, wannan shine cikar imani da Allah da kuma Manzo.
" Hakane...".
Noor tace tana me share hawayen ta da suka kasa tsaya mata, tana goge wa amma wani na sake gangarowa...amma a hakan ta daure ta furta..." Allah ubangiji ya ji'kan Ma'u, Allah yasa ta ta huta, Allah ya ji'kan duk wa'danda suka mutu ya kyautata makwancin su, muma da muke raye Ubangiji Allah ya sa namu 'karshn yayi kyau, Allah yasa mu mutu muna masu aikata Alkhairi ba sharri ba.."
" Ameen Thumma Ameen" Hafsat tace cikin sanyin murya, yayin da Noor ta cigaba da labarin ta kamar haka" Babban abin tausayi ma shine Malam Barau, dattijon kuka ya ringa yi da hawaye yana sharewa, Alhaji Baba kam komai tsaya masa yayi cak, musamman da yake yana ganin cewa 'dan sa ne sanadin komai, abin ya tsaya masa arai sosai har ya hana shi sukuni.
Da shi akayi komai har aka sada Ma'u da makwancin ta na gaskiya, hatta abincin da za'a bu'kata gidan rasuwar Alhaji Baba duk shi ya 'dauki nawin komai har aka 'kare kar6an gaisuwa, bayan bakwai jama'ah kowa ya koma harkokin gaban sa amma banda Alhaji Baba.
A kullum zaka same shi ne cikin tunani, yana so ya sanar da Yah Deen batun rasuwar amma idan ya tuno shi sai yaji takaici ya kama shi haka ya sa ya kasa sanar da shi da kuma nuna masa muhimmancin sa a wurin.
Alhaji baya ta6a yin kwanaki biyu batare da ya ziyarci mahaifin Ma'un ba saboda zuciyar sa ta kasa nutsuwa wuri guda.
Ko gidan gonar sa badan mutane masu amana ne akai ba da komai lalace masa zaiyi dan baya tuna zuwa can kwata-kwata illah waya da suke yi, hakan ma sai dai yace da su suyi duk abinda ya dace kawai kar su damu.
Ammi ce ta sanar da Yah Deen batun rasuwar inda yaji abin har zuciyar sa saboda mutuwar ta masa bazata, sosai jikin sa yayi sanyi...amma ko da Ammi ta nuna masa dacewar zuwan sa dan gaida mahaifin ta take ya kawo wani excuse cuz baya son zuwa cikin irin wannan taron musamman ma da yasan cewa sai an ta nuna shi idan yazo wurin, shi kuwa ba ha'kuri ne da shi rayuka sai su 6aci a banza.
Da gama wayar su da Ammi take sai ya 'kira Imrana da tun baya zuwan su gidan sa basu sake wata gaisuwar kirki ba, ko rasuwar Ma'u Imran bai 'kira shi akai ba, nan suka nunawa juna alhini cuz shi Imrana bai ma san da batun ba ashe tuni yana Kano sai da Yah Deen 'din ya sanar da shi kafin nan daga nan kuwa suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.
Cikin sati na biyu da rasuwar Ma'u sannan Yah Deen yazo gida bisa umarnin Alhaji Baba da yake ma a lokacin duk an watse babu kowa sai mutanen gari.
Lokacin da Alhaji ya umarce shi da zuwan ma sosai hankalin sa ya tashi, zaton sa ko magana ce akaina ko kuma abinda ya faru abaya kafin tafiyar sa, hakan ya sa natsuwar sa tayi masa 'kaura dan Alhaji bai kawo batun Ma'u cikin maganar tasa ba.
Da niyyar sa yace su taho da Ishaq amma sai yayi tunanin kar Ishaq yaji wannan uban abin kunyar da ya tafka wanda basu da masaniya sam akanta, hakan yasa ya shirya kawai ya taho dan ba zai iya yiwa Alhaji musu bane ma baya ga haka da babu abinda zai sashi tahowa.
Sai da ya iso ne ma kafin ya 'dan ji natsuwa da yaji dalilin zuwan nasa ashe ba abinda yake zato bane gaisuwar gidan Malam Barau ne kawai.
Bai wani damu ba cuz can cikin zuciyar sa ma wani kwantaccen farin ciki yake ji wanda daga baya bayan jin labarin rasuwar Ma'un yayi tunani, a ganin sa Allah ya so shine ma shiyasa ya kar6i ranta bayaga haka da ina zaije da ita da abinda zata haifa a duniyan nan...ba'a farin ciki da mutuwa saboda kowa mutuwar zaiyi amma shi kam sai dai yace Alhamdulillah...duk da haka zuciyar sa na 'dan jin abin a sirrance saboda shi kansa yasan ya zalunce ta ya ci mutuncin 'kuruciyar ta da wayo.
A fili kuwa sosai yake nuna alhinin sa ga Alhaji Baba da duk wanda zancen ya ha'da su.
Washegari da sassafe Alhaji Baba ya sa shi gaba suka wuce gidan Malam Barau ya gaida shi ya kuma nemi gafarar sa bisa abubuwan da suka faru, inda Malam Barau ya nuna masa ba komai ai 'kaddara rubutacciya ce sai dai fatan a kiyaye gaba, Allah kuma ya shirya, yace karamcin da mahaifin sa yayi masa ma ka'dai ya ishe sa..Ma'u kuwa addu'ah ce kawai tsakanin su a yanzu, Ubangiji Allah yajiqan ta da Rahama ya kyuatata makwancin ta.
Nasiha ya yiwa Yah Deen sosai game da rayuwa sannan suka taho gida bayan sun yi masa goma ta arzi'ki.
Kwanan sa biyu ya sake komawa Jigawa wanda a kwanaki biyun nima sau uku ka'dai na ga fuskar sa, tsanar sa ce ta ke sake girma a zuciya ta yanzu, musamman da na san cewa shine sanadin mutuwar Ma'u...haka abin yake kuwa ko a bakin mutane 'yan kaiwa da kawowa ma abinda suke yawo da shi kenan...hatta Ammi a lokacin na lura abin ya dame ta sosai sai dai ban san takamamman dalilin damuwar tata ba dan bamu tattauna batun da ita ba.
Ina dai da tabbacin itama 'kilan taji ra'de-ra'den da jama'ah ke yi ne game da rasuwar, kawai sai naga ta 'kara jana a jiki ta jan yawaita bani ha'kuri da nasiha mai kwantar da hankali wanda a hankali na fahimci duk ta nayin hakan ne saboda ta rage min damuwa, cuz tasan dole yanda taji nima zanji koma fiye da hakan.