← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 211

Sashe 161

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kukan tace" Dana sani nake ji masu yawan gaske Hafsat, dana sanin yadda da auren sa da nayi tun farko, da nasanin rayuwa da shi, haihuwar da nayi da shi da kuma cigaba da barin sa yana kusanatata bayan nasan halin sa.
       Ji nake dama rayuwa ta bata kawo i yanzu ba nasan da duk hakan basu faru ba, 'kila da ko haihuwa da shi ma bazan yi ba, wallahi da nasan hakane da ranar da su Imrana suka zo da da kaina zan ro'ke shi ya barsu su aikata abinda ya kawo su koda kuwa hakan zai yi sanadin raina ne tunda dama burin sa kenan 'kila da yanzu labarin bai iso nan ba da duk hakan bai faru ba.

" Da ya zama 'kaddarar ki kuma fa Noor? Haba dan Allah, kar ki bari tashin hankali ya gusar miki da tunanin ki mana, ina ilimin ki ina ha'kurin ki? Haba Noor ya zaki rin'ka fa'din maganganu tamkar baki san ciwon kanki ba? kar ki manta fa abar halitta ce ke, kinfi 'karfin Allah ya jarabce ki ne ko me? Hala kin manta cewa Allah yana tsarawa bawa rayuwar sa ne tun kafin zuwan sa duniya.."

"Nasa ni Hafsat ban manta ba, amma har abada ni nasan wannan sakayya ce ba 'kaddara ba ce, Allah ne ka'dai yasan yawan rayukan da banzan halin Yah Deen ya cutar ya lalata kuma yayi dumping in su, wanda gashi kina gani 'karshe ya 'kare ne akan Jasmine, kuma wallahi har abada bazan ta6a yafe masa ba, kuma baby ma bazata yafe masa ba koda kuwa abu ka'dai da ya rage masa da zai sa asashi a aljanna kenan baza mu ta6a yafe masa cutar da zuciyoyin mu da yayi ba".

Hafsat goshi ta dafe cike da damuwa da 'kuncin zuciya, sam bata san me zata sake fa'diwa Noor ba da zai kwantar mata da hankali...cikin hakan taji Noor 'din na fa'din" Babu yadda Alhaji Baba bai yi da shi ba, haka ma Ammi hadda Uncle Ja'afar amma duk ya watsar, an nuna masa illolin aikata zina, an gaya masa sakamakon mai yin ta, an kwatanta masa zabar da Allah yake yiwa mai aikata ta amma duk abanza after all ma da kansa yasan komai tunda yayi karatu dai-dai gwargwado amma ya take, ni dai nasan ban ta6a yi masa magana akai ba saboda banga fuskar hakan ba, amma ai nasan Ammi sun yi masa fa'da da kansa kuma shima 'din ya sani, kuma yasan dalilin hakan ne ya hana auren mu 'daukan hanya har yau amma ya share, ko Sani ma na sha nuna masa cewa halin Sani bai min ba amma yayi banza da magana ta ya cigaba da nunanwa Sani 'kauna ya bashi muhimman ci ya 'daukaka darajar sa sama da mai gadin gidan sa da tun zuwan mu Bauchi muke tare da shi...'karshe suka cutar min da yarinya, suka lalata min rayuwar yarinya...insha Allahu duk sai sunga sakayya domin Allah bazai bar su ba, zama da Yah Deen kam daga yanzu ya 'kare, mun bar rayuwar sa kenan har abada..zanje in rayu da yarinya ta in kula da ita da tarbiyar ta, zanyi 'ko'kari wajen ganin na goge duk wasu munanan tabo da yayi mata...ko babu shi tana da Alhaji Baba, tana da Saif ga Zaidu sannan ga ni ga Ummah ta da 'yan uwana mu ka'dai mun ishe ta ba sai da shi ba...daga yau matsayin _babu_ yake a wurin Baby insha Allahu...sai na mantar da ita shi da duk wani abu da ya shafe shi.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *75*

Ha'kika Mu'een ya aikata son ransa a duniya ya manta cewar Allah yana hukunta mutum ne dai-dai da abinda ya aikata a duk lokacin da yaso, ya manta cewar tun a duniya Allah yake sakayya musamman irin wannan zunubin, Mu'een yaci mutuncin 'kauna, ya ci mutuncin yarda da kuma amana, ya zarafin aure 'karshe ya 6ige da yaudarar mahaifan sa ya 6oye musu asalin waye shi.
Allah da kansa ya toni asirin sa wajen mahaifan sa amma duk da haka bai watsar da banzan halin sa ba...'karshe wa gari ya waya?..rayuwa sau'ki ne da ita sosai matu'kar ka tsarkake zuciyar ka ka sanya tsoron Allah a cikin ta, sa6anin hakan kuwa a kullum bazaka ta6a ganin dai-dai ba...Allah ka rufa mana asiri ka yafe mana zunuban mu badan halin mu ba".

Hafsat ce ke wannan tunanin cikin zuciyar ta tana mai jin zafin abin, ga kuma Noor da ke kuka a gefen ta wanda tasan ko ita ce haka ya faru da ita abinda yafi kuka ma zata yishi domin wannan abin kuka ne, abin ba'kin ciki ne sosai, bata da bakin da zata furta wata kalma da take ganin zai taushi zuciyar Noor ko kuma ya hana ta zubda hawaye, to koma ta daina hawayen ai bata isa ta kankare tabon abin cikin zuciyar ta ba, domin kuwa a zahiri an zalunce ta iya zalunci, an ci mata fuska an kuma 'kunsa mata ba'kin cikin da har 'karshen rayuwar ta bazata iya mantawa da shi ba, ina ma laifin ace aure yayi ya cika gidan sa da mataye ta tabbata da sai yafi ma Noor sau'ki fiye da ji da ganin irin wannan lamarin.

Sosai Yah Deen yaci amanar masu son shi, yayi wasa da tunanin su, yayi amfani da 'karfin soyayya duk ya yaudare su da ita ya lalata musu rayuwar su.

Farko rayuwar *Rahma* yaso ya 6atawa tun tana cikin 'kuruciyar ta, sai Allah ya taimake ta ya bata kariya ta hanyar sako yayan ta cikin lamarin 'karshe Allah ya ha'data da miji mai so da 'kaunar ta duk da yasan cewa ga abinda ya so faruwa amma ya kawar da kansa ya aure ta ya zauna da ita da amana...yanzu haka tana nan da yaran ta biyu mace da namiji.

'Kaddara ce ta sake ha'da shi da *Husnah* na biyu wacce ta so shi da dukkan zuciyar ta, ta nuna masa 'kauna, amma shi koda wasa bai ta6a jin soyayyar ta cikin zuciyar sa ba, amfani yayi da hakan yayi rayuwa da ita irin wacce yake so ya maida ita tamkar matar sa batare da yayi tunanin makomar sa ba.
Abu mafi muni da Allah wadai shine zubar da cikin da yayi mata wanda azabar Allah ce ke jiran duk mai aikata irin hakan, ya sani amma ya kawar da kansa.
Mahaifin sa yaso aura masa ita amma Allah bai 'kaddara aure tsakanin su ba sai iyayen ta suka zo da batun aura mata 'dan uwan ta Hisham shi kuma 'kaddara ta ha'da auren sa da Noor batare da neman amincewar ta ba.
Mu'een hakan duk bai ishe shi misali ba sai ma ya 'kara da cin mutuncin auren Husnah bayan iyayen ta sun aurar da ita, duk daraja irin ta aure amma hakan bai hana Mu'een sake shiga rayuwar Husnah ba tana kuka amma sam ya kawar da kai ga hawayen idanun ta, ya kasa fuskantar haukan da yake aikatawa saboda son zuciyar sa ya riga ya rinjaye shi..abin takaici ma cikin gidan da yake zama da matar sa ta sunnah nan ya kawo Husnah da sunan fasi'kanci batare da ko jin tsoron abinda zai biyo baya ba.

Hakan bai ishe shi ba ya sake yin amfani da soyayyar da *Ma'u* take yi masa ya ya yaudare ta da soyayya ya 6oye manufar sa abayan rashin wayewar ta, 'karshe ya barta da guzurin cikin sa batare da ya nuna kulawar sa gareta ba har ta rasa rayuwar ta sanadin cikin da kuma tasku da 'kuncin rayuwa da ya jeta ciki.

Duk yadda iyayen sa suka nuna masa 6acin ransu akan hakan amma ya basar ya rufe kunnuwan sa ya mantar da zuciyar sa nasiha da garga'din da suka 'dauki tsawon lokaci suna yi masa, abin mamaki da zuwan sa Bauchi ma sai da ya nemi *Yusrah* wacce ita ka'dai ce ya nuna ra'ayin sa gareta da karin kansa har suka 'kulla ala'ka irin ta soyayya, 'karshe suka 6ige da aikata zina a hotel a duk lokacin da bu'kaci hakan...itama rabuwa suka yi bisa tursasawar Safwan in badan shi bama 'kila da har yanzu suna tare da ita tunda gata can auren ya kasa yiyuwa har yanzun kuma still tana son shi ta kasa mantawa da shi.

Hankalin Noor har ya kwanta bayan rabuwar sa da Yusrah kwatsam sai kuma ga *Jiddah* ta 6ullo bayan komawar sa Abuja...itama kuma duk abin 'daya ne....abubuwan Allah wadai da Mu'een ya aikata gaskiya suna da yawa sai dai fatan Allah ya yafe mu gaba 'daya...Har ga Allah Noor ba 'karamin ha'kuri tayi ba da cigaba da zama da shi ahakan bayan tasan duk 6oyayyan halin sa, sosai Hafsat ta jinjina mata, ita aganin ta koma me Noor tace zata aikata yanzu bazata hanata ba domin ya cancanci ko wani irin hukunci, Mu'een mutun ne da bai san bambancin hagun sa da daman sa ba, bai san halak da haram nada bambanci ba sam, bata ga alamun ya sawacransa akwai ranqr nadama ba sam baya hangen gaba baya tuna makomar sa wurin mahalicci, rayuwar duniya da jin'da'din ta kawai yasa agaba, in ba haka ba ace kana da mace kamar Noor a gida me zakayi da 'yammatan layi 'kazamai marasa kamun kai in ba son zuciya da neman 6atawa kanka daraja ba.
Chapter 161 · 0% Book details