← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 211

Sashe 145

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ba yau ba Addah ta ta gaya min cewa duk wacce Allah ya jarabce ta da miji irin nawa mai kula wasu matan a waje,  wallahi zama bai ganta ba sam, dole ne matu'kar tana son dai-daita al'amuran gidan ta sai ta tashi tsaye ta hana idanun ta bacci, ta ro'ki ubangijin ta ta kuma dagewa wajen kula da dukkan al'amuran sa, kula da hakko'kin sa da sauran su, a wancen lokacin ganin abin nake tamkar wasa, gani nake tamkar ni ban kai matsayin ba tukunna, da yake kallon wasa nakewa auren namu, sai gashi yanzu na fara sanin muhimmancin aure na, ina jin zafi cikin raina idan na tuna halayyar miji na.

Addu'ah kam ba laifi ina 'ko'karin yinta amma sauran abubuwa kam har yanzu ban ga ranar yin su ba...(agani na kenan).

Haka na cigaba da zuwa makaranta ta hankali na rabe bibbiyu, sai dai ban bari 'dayan 6angaren ya rinjaye ni ba kawai nafi bada hankali ga karatu na.

Shima Yah Deen duk wasu abubuwa da ya kamata yayi su bayan gama makarantar sa anan garin Bauchi yayi su, a asbitin ya ha'du da sabon abokin sa mai suna Safwan wanda ko makarantar da nake yi ma tare da shi suka yi min komai.

*****
        Watanni biyu da sati uku kenan da zuwan mu garin Bauchi wanda yake dai-dai da cikar shekara guda yanzu da auren mu.

Bazan ce ga abinda Yah Deen yayi min na rashin jin da'di ba tun zuwan mu Bauchi haka kuma bazan iya furta shin tsakani na da shi wake son wani cikin zuciyar sa ba, har yau na kasa fahimtar hakan.

Ni dai ta 6angare na nasan bana jin soyayyar sa cikin raina, amma na kanji kewar sa a duk lokacin da baya tare dani, na kanji tsananin son ganin sa matu'kar na yini  ban gansa ba, sannan na kan yawaita tsintan kaina da son faranta masa duk dama ba yaba min yake yi a zahiri ba amma bana damuwa, uwa uba kuma kishin sa da na fahimci yake damu na, da kaina na fahimci kishin sa ne ke sani yawaita tuna wancan al'amarin da har ya kasance wani lokacin idan na kasa controlling zuciya ta har kuka inayi da hawaye na saboda ciwon sanin halayyar sa da nayi tun abaya, da kansa kuma zaki ga ya rarrashe ni idan yana gida dan ya rsani ganin hawaye a idanu na, in kuwa baya nan sai inci kuka na in 'koshi har inyi shiru, ko da ya dawo kuwa tambaya 'daya yake min akan me ya same ni har nayi kuka?"
Idan yaji ban bashi wata gamsashshiyar amsa ba sai ya 'kyale ni baya sake kula ni akan hakan.

Sau da dama irin hakan na faruwa tsakanin mu amma ban ta6a sanar dashi ainahin abinda ke damina ba sai dai ince masa ni kawai Ammi na nake missing.

Wani sa'in zaunar da ni zama yake yi atake ya 'kira Ammi sai kiji ya 'kira Ammi ya gaya mata, idan ya ha'da mu awayar tayi ta bani ha'kuri tana lalla6a ta.

Duk hakan kuwa ni a gani na basu isa hujjar da zan ri'ke su matsayin so ba, kawai na bar shine akan matsayin da yake da shi na miji agare ni shike sa ni jin wa'dannan abubuwan.

Ko daga 6angaren sa kuwa haka na fahimta, Yah Deen baya sona a gani na dan bai ta6a furta min kalmar so ba ko da wasa, duk yadda yake shiga shau'ki idan munatare da shi amma hakan bai ta6a sawa yayi ko kuskuren ambata min kalmar so ba.

Abinda nasan yake bayyane daga 6angaren sa shine yana matu'kar kula da duk al'amura na, baya son ganin kuka na a yanda na fahimce dan ko kusantata yaso yi idan na yaga ina kuka bari na yake yi, ni kuwa tsananin takaicin halin sa idan na tuna shike sani wannan kukan ba komai ba, amma zaki ga ya 'kyale ni ya koma lallashi na har muyi bacci, na kuma fahimci yana matu'kar jin da'din ganin walwata, domin a duk sanda na yi dariya har ha'kora na suka bayyana ko da bada shi nake ba zaki ga  shima yayi murmushi mai sanyi kuma ta'kaitacce.

Tsananin kishin da yake da shi akaina ma ban kasa fahimta daga gare shi ba, shiyasa duk abinda zan yi na kan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ban aikata abinda zai motsa kishin sa ba.

Sosai ya garga'de ni lokacin da zan fara fita makaranta, a lokacin bai 6oye min ba yace min" matu'kar ina son Ammi da farin ciki to in kiyaye maganganun sa, yace min in kula da darajar aure na a ko'ina, rantsuwa yayi min akan cewar matu'kar na kuskura ya kamani da laifi ko kuma yaji ko yaga ina mu'amala da wasu mazan to in sani daga ranar batun makaranta ya 'kare kenan a rayuwa ta, idan kuma ina son farin cikin Ammi to dole ne in bi maganar sa dan baya tunanin zai iya sake rayuwa idan har wani labari daban ya riski dangin biyewa wasu mazan dan yana da tsananin kishi wanda yake tunanin har lahira zai iya kaishi idan har akan iyalin sa ne, kuma mutuwar sa dai-dai yake da tashin hankalin Ammi da Alhaji harda Anty Zainab..ya 'karashe da fa'din..." Ko kina so kiga hankalin su Ammin ki a tashe?"
Da sauri nace da shi  a a gami da girgiza kaina.
Sai yace" to dan Allah ki kiyaye kinji?"
Ya hane ni da shiga motar haya, hawa lift ko wani abu yace sam bai amince min ba, yace matu'kar inada bu'katan zuwa gida lokacin tashi ne a school ko wani abu daban idan bangan sa ba to in 'kira shi a waya kawai zai zo ya same ni.

'Banagaren abokan sa ma duk yana taka tsantsan da duk wata ala'kar da zata ha'da mu, bama ya kawo kowa gidan sa, Safwan ka'dai ne Yah Deen ya sakewa fuskan zuwa gidan sa,  shima 'din kamilalliyar sutura ya hore ni da sawa ko da yazo.

Duk wannan kuwa agani na ba so bane tunda bai furta da bakin sa ba, kishi ne da kuma son kula da maratabar auren sa ya ke sa shi yin hakan, balle ma da nasan lamarin da ya faru tsakanin sa da su Imrana shikenan na bar dalilin  akan hakan, dan tun lokacin ya ke gudun abota da kowa, Ishaq ka'dai ya yarda da nagartar sa sai kuma Safwan mutun na biyu.

A yanda tunani na ya bani a hakan na 'dauka kuma naji araina gaskiyar kenan, wato babu wata soyayya tsakani na da shi, haian yasa ban ta6a bawa kaina 'kwarin gwiwar gyara mu'amalar mu saboda a gani na tunda baya sona ai babu amfani yin hakan, dalilin kenan da yasa muka cigaba da zama cikin gidan auren mu amma babu wata sha'kuwa tsawon lokaci.

*****
    Shirye- shiryen bikin Safwan aka fara gadan- gadan (bikin ku kenan) ta 'dago ta kalli Hafsat, sannan ta cigaba da fa'din sai kuma ya kasance Yah Deen sune a gaba da komai har aka 'kare bikin wanda nima sai lokacin ne ya kaini gidan su Safwan wajen mahaifiyar sa, ko ranar bikin ma can na yini da su, 'kannen sa kyawawa da su fulanin Bauchi, sosai Allah ya ha'da jinina da su, dan ma biyu daga cikin su daga wasu garuruwa suka zo ba anan suke aure ba, 'daya ce ka'dai ke aure a Bauchin amma duk da haka sosai sha'kuwar mu tayi 'karfi.
Duk matsayin 'kanwa suka 'dauke ni da yake duk sun girme min.

Ba 'karamin da'din zama da su nayi ba dan kuwa basu da mugun hali, kafin 'karewar bikin kuwa har ji nake dama Yah Deen ya barni in zauna agidan tare da su in huta abina, ni da kaina ma nasan hakan ba mai yiyuwa bane, domin kusan 3days muna zirga-zirga zai kaini zai kuma koma ya 'dakkoni da kansa baya gajiya amma ba zai ta6a bari na in kwana ba.

Su kuma 'kannan Safwan ganin hakan da suka yi sai suke tsammanin sosai wai miji na yake ji da ni shiyasa ma ba ya bari na kwana a waje.

'Daya daga cikin su ce tana dariya tace" ai kuwa ba laifi Noor akwai kyua ga tsafta 'kila sune suka sa tayi nasaran siye zuciyar shi".

Dariya suka sanya harda nima ina sunkuyar da kaina dayake nasan ba hakan bane, tana cikin dariyar ta 'kara da fa'din amma fa kin birge ni wallahi, gaki 'karamar yarinya amma Allah ya baki baiwa, mutum kamar Dr. samun kansu abu ne mai wahalar gaske, na jinjina miki 'kanwata".

Murmushi na ne ya 'karu still ina 'kara sunkuyar da kaina cuz sosai kunyar su ta kamani.

Wannan shine _kallon kitse ake yiwa rogo_ dan duk yanda suka 'dau ki abin ba haka yake ba.

Ban 'kara tsinkewa da al'amarin su ba ma sai lokacin da 'daya daga cikin su ta bani wani turare akwalba 'dan 'karami mai shegen 'kamshi tace wai sai zan kwanta zan yi amfani da shi, inshafe a jiki na har zuwa wuya na..tana murmushi tace wannan kam da kanki zaki zo ki bani labari 'kanwa ta".

Murmushin nima nayi cikin raina nake jinjinawa karkataccen tunanin su, nan wai su a dole sun ga masoya...hmm

Wani sa'in idan na tuna maganganun su har dariya kamani take yi ni ka'dai, sam koka'dan banji haushi ba, ji ma nake da ace yanda suke tunani 'din zai faru ai da sai nafi kowa farin ciki da samun natsuwa, nima da kaina yanzu ina so inji kalmar so daga bakin miji na sai dai ga dukkan alamu bani da wannan matsayin agare shi...hakan yasa na bar abin a zuciya ta.

Lokacin da na koma gida kamar yadda Anty Fiddausi 'kanwar Safwan ta gaya min haka nayi da turaren da yake bata fito fili ta bayyana min ainahin amfanin sa ba hakan yasa nima ban yi wani dogon tunani akai ba.

Zato na ko kawai turare ne na bacci shiyasa nayi amfani da shi, ai kuwa ranar na gane kure na wajen Yah Deen, dan ko kukan da na keyi ma ranar bai bi ta kai ba sam...anjima ka'dan ya kuma dawowa kamar zan mutu haka naji.
Chapter 145 · 0% Book details