Sashe 165
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun sa 'dayan Safwan ya kamo cikin nasa da alamun rarrashi yace da shi" Ka kwantar da hankalin ka please, kai fa namiji ne, 'karfafa musu gwiwa zakayi Mu'een ba wai kaima ka tashi hankalin ka ba".
" Dole hankali na ya tashi Safwan, da kanka kasan ni ne silar komai, ni na jawa Baby wannan abin, 'kila da ban kasance mahaifinta ba da hakan ba zai faru da ita ba.. gaskiyan Noor ne, gaskiyan ta ne da take neman cire ni daga rayuwar su, ha'ki'ka ban kasance abin alfahari a gare su ba...i wish mutuwa nayi Safwan da ace Baby ta taso da wannan tabon agaba na ina ganin ta da shi zuciya ta bazata iya 'dauka ba Safwan..."
Ya 'karashe da sakin kuka mai tsuma rai irin wanda bai ta6a yin irin sa ba..kansa ya kwantar bisa hannun Safwan ya cigaba da kukan sa.
Safwan kam shiru yayi shi kansa idan ka ganshi duba na farko zaka fahimci a matu'kar tashe hankalin sa yake.
Hannun sa 'daya ya 'daga ya 'dora a kan Yah Deen tamkar wani yaro 'karami da ake shirin lallashi, a hankali yace da shi" Kayi ha'kuri, abin ba da'di kam amma babu yanda zamu yi, u have to bear that pain Mu'een, ko ba komai yanzu nasan zaka fahimci abinda na da'de ina nuna maka a baya game da rayuwa, nd ka kwantar da hankalin ka Baby na nan lafiya haka Noor ma..yanzu haka ma na baro su ne zaune Baby zata ci abinci".
Murmushi yayi mai ciwo yana jin zafi cikin ransa, ko shi da kansa ya tsani kansa tunda ya kasance silar rugujewar farin cikin gidan sa..kuma ko Safwan bai fa'da ba yanzu kam ya san irin ciwon da ake ji idan aka lalata rayuwar wani naka, Hayat ya tuno, yanda hankalin sa ya kasa kwanciya bayan ganin da ya yi masa da Rahma 'kanwar sa, hankalin Hayatu bai kwanta ba sai da ya tabbatar da ya aurar da Rahma tukunna.
Ma'u Malam Barau kam da kansa ya san ba 'karamin 'kunci iyayen ta suka shiga ba musamman mahaifin ta, dan sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya kula da tarbiyar ta amma duk ya 6ata masa shirin sa, abu mafi muni da mahaifinta ya fara cin karo da shi shine cikin da take 'dauke da shi, yasan wannan ba 'karamin tada hankalin sa yayi ba.
While a lokacin shi bai wani damu ba, da yake bai san yanda ake cin abin ba haka yayi watsi da Ma'u Alhaji Baba ka'dai ne ke kulawa da rayuwar ta har ta rasa rayuwar ta sanadin cikin.
Sai gashi Allah cikin ikon sa shima ya bashi haihuwa, haihuwa kuma ta 'ya mace wacce ta kasance mafi soyuwa cikin zuciyar sa fiye da komai, daga 'karshe ya jarrabe shi da abu makamancin wanda ya jima yana aikatawa akan 'yar sa, yasan Allah yayi hakan ne badan komai ba sai dan kawai ya nuna masa nasa ikon ya kuma sawa shima ya 'dan'dani 'dacin da ake ji akan duk yarinyar da aka 6atawa Rayuwa, Yah Allah ka yafe min....
'Dago kansa yayi a hankali da jajayen idanun sa yace
" ...Ina so inga iyali na Safwan, inaso inga Baby, ina so in ro'ke ta ta yafe min alhakin ta da ke kaina, amma tsoron Nuree nake yi tace ta tsane ni bata son gani na, tace in fita daga rayuwar su, please Safwan help me..."
" Is okay...ya isa haka nan Mu'een be a man mana, ka daina yin abu tamkar mace please, Baby ma ta yafe maka ka daina damun kanka dan Allah".
" Ni dai ina so in gansu, inaso in rungumi Baby a jiki na.."
" To shikenan ka kwantar da hankalin ka zaka gansu amma ka bari sai zuwa anjima ka'dan idan ka samu 'karfi sai in kaika wurin su kaji, Nuree ma ta sakko yanzu kuma inada ya'kinin zata yafe maka itama insha Allahu ".
Kallon Safwan yake yi har ya dasa aya a maganar sa, sai da ya lumshe idanu ya bu'de kafin ya tambaye shi
" Sau nawa Nuree tazo ta dubani anan Safwan?"
Shiru yayi bai kamar mai tunani cuz rasa amsan da zai bashi yayi, bai san zai tambaye sa hakan ba kwata-kwata, dole dan ya sake kwantar masa da hankali ya 'kirk'iro 'karya yace masa tazo sau 'daya amma a lokacin bai farka ba".
Komawa yayi da bayan sa ya kishingi'da yana murmushin takaici a hankali yace..." Nasan halin Nuree sosai Safwan, Nuree na da taurin kai da kafiya, nasan ko mutuwa nayi da 'kyar ne ta min.duban Rahama bazata ko kula gawa ta ba tunda ta tsane ni sosai yanzu..."
Idanun sa ya mayar ya rufe su tare da cije la66an sa daga gefe" 'Kirji na zafi yake min Safwan ina jin tamkar rayuwa ta 'kare ne, farin ciki na yazo 'karshe, 'kilan ma bazan sake kallon Baby ba, bazan sake kallon Nuree na ba har abada..."
Safwan hannun sa ya sanya cikin nashi zai yi magana sai Yah Deen ya riga shi da cigaba da fa'din" Alhaji Baba, Ammi na dan Allah Safwan kace su yafe min nasan suma idan suka ji labarin abinda ya samu Baby tsanata zasuyi hadda Uncle Ja'afar, Safwan dan Allah ka kula min da iyalina ka basu farin ciki...ka...".
Kasa 'karasawa yayi saboda wani suka da yaji a 'kirjin sa, hannun sa dake cikin na Safwan ya dam'ke da 'karfi while 'dayan hannun san still na nan saman 'kirjin.sa saitin zuciyar sa.
Numfashi mai 'dumi ya furzar yayin da Safwan ke faman jera masa sannu cuz ya fahimci sosai yake jin jiki.." bari in 'kira Dr."
Safwan ya fa'di cike da kulawa.
Dauriya yayi ya 'dan bu'de idanun sa tare da cire hannun sa daga cikin na Safwan a hankali ya yun'kura ya kwantar da kansa da kyau...Da kansa ya tsani rayuwar sa yanzu, shi kansa baya so ace ya cigaba da rayuwa saboda bai san da wani idanu zai sake kallon Baby ba matsayin sa na mahaifin ta da ya kasa bata kulawar da ta dace ya kasa tanadar mata kyakkyawan 'kaddara yayi silan rushewar farin cikin ta dana mahaifiyar ta mafi tsananin takaici cikin zuciya.
Fita Safwan yayi ya 'kira likitan dake kulawa da shi, ko da suka dawo kuma sai suka tarar baya 'dakin kansu duk ya kulle yayin da hankalin Safwan yayi mummunan tashi, kafin ya dai-daita tunanin sa suka gansa ya fito daga bayi, wani ajiyen zuciya Safwan ya sau'ke, bai tanka su ba ya wuce ya zauna bakin gadon sannan ya kalli Safwan yace masa" Zanyi Sallah".
" Ok"
Safwan yace tare da fita ya tafi sauri-sauri gudu-gudu ya 'dakko masa dadduma daga office 'din sa.
Suna nan zaune har ya idar da dukkan sallolin dake kansa tun na jiya har na yau, ya jima yana addu'ah sannan ya shafa.
Duk yadda likitan yaso sake duba shi Yah Deen 'kin amincewa yayi yace shi kam ya bar shi ya riga ya warke...key 'din sa da wayar sa yace su bashi Safwan ya 'dakko ya mi'ka masa ya kar6a amma bai kunna wayar ba saboda baya son a dame shi a halin yanzun.
Dole haka suka ba dan sun so ba suka barshi ya nufi hanyar fita bako takardar sallama.😀
Safwan ne ya bishi abaya yana ro'kon sa akan kar yayi driving, yace ko yasa a sau'ke shi a gida ya girgiza masa kai, da 'kyar yake tafiya daka gansa zaka fahimci yana jin jiki amma a hakan ya cigaba da tafiya, 'dakin da su Noor suke ya nufa ga mamakin Safwan sai yaga bai yi gigin shiga ciki ba ta window ya tsaya yana 'kare musu kallo yana murmushi ganin kamar bakin baby na motsi tana yiwa Noor magana, yayin da ta kwantar da kanta gefen na Babyn tana shafa kanta.
Sanyi yaji har cikin zuciyar sa, tare da godewa Ubangiji...haka kawai ya tsinci kansa da son ganin su, yaso wannan hirar ta kasance da shi amma ba dama ya riga ya yiwa kansa babban katanga tsakanin su, sam bai ga laifin Noor bisa hukuncin da ta yanke masa ba, fiye da hakan ma yasan ya cancanci ayi masa.
Yana daga wurin ko jin abinda suke fa'di baya yi amma sai sakin murmushi yake yi lokaci zuwa lokaci kuma yana share hawayen tausayin su.
Cikin ransa ya ayyana indai hakan shine farin cikin ku Nuree har abada bazan 'kara takura muku ba, ni kece farin cikina haske na da walwala ta amma tunda kin za6i rayuwa ba ni, kin za6i in barki in fita daga rayuwar ku, nayi al'kawarin bazan sake takura muku ba bazan sake shiga rayuwar ki ba Nuree...".
Girgiza kai Safwan yayi ganin yanda Mu'een ke uban zubda hawaye, sosai yake jinjinawa wannan lamarin da har ya isa sa mutun irin Mu'eenuddeen zubda hawaye, abu mai girma ne zai iya sa hawayen sa sau'ka... dai-dai lokacin da wayar sa ta 'dauki ringing yana dubawa sai yaga mahaifiyar sa ce, 'dauka yayi yace" Kar dai har kin iso Mummy?".
Deen baiji mai aka fa'da daga 'daya 6angagaren ba sai gani yayi Safwan ya fara faciya yana fa'din" Gani nan nan zuwa yanzu".
Saurin barin window in Yah Deen yayi ya ha'da bayan sa da jikin bango yana sakin numfashi, sosai ya gaji da tsayuwan numfashin sa har sama-sama yake yi amma saboda jin da'din ganin su da yake yi a hakan.ya daure ya cigaba da tsayuwa.
Ahankali ya bar wurin ya fara tafiya hanyar da yasan bazata ha'da shi da Safwan ba yabi ya koma parking space na asbitin ya bu'de motar sa da tun jiya take a wurin ya shiga ya 'dage duk gilasan motar ya kwantar da kansa idanun sa a lumshe.
Idan baka sani ba bazaka ta6a tunanin da mutun acikin motar ba, duk yayi hakan ne kuma dan kawai ya kaucewa ha'duwa da Mummy, sosai yake jin kunyar ta, nawin ha'da idanu yake yi da ita..zaton sa ko itama tasan abinda ya faru ne shiyasa yayi hakan, dan yasan babu wanda zai goya masa baya, shi da kansa ma yasan shi mai laifi ne, bai ta6a sanin akwai ranar da zaiji da kansa ya tsani kansa kamar yau 'din nan ba.