← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 203 OF 211

Sashe 203

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ko wani da'ki'ka rashin natsuwa ke sake ziyartar ta haka take yini ba ko walwala domin kuwa sosai Hakeem ya matsa mata a hakan ma bata fasa Addu'ahn da take yi kullum ba, wani sa'in yini take yi da wayar ta akashe saboda Hakeem ka'dai, gefe guda kuma maganganun Saif da Anty ke mata yawo aka, banda wanda Ummah ke shigar mata cikin brain 'din ta kusan kowace rana tana sake nuna mata ribar da mai ha'kuri ke da shi, ta kan ce ita kanta lokacin da labarin ainahin waye Muhammad ya iso gareta ba 'karamin ba'kin ciki taji da auren da ke tsakanin su ba dan a ganin ta bai cancanci a ha'da jini da shi ba, amma tunda taji cewa ya bada sakin Noor shikenan kuma sai jikin ta yayi sanyi, bata tsinke da lamarin ba sai da taga ya kasa samun cikakken lafiya tun rabuwar sa da matar sa tace da 'kafafun ta ma ta sha zuwa duba shi idan an dawo da shi gida da yake zuciyar tausayi ne da ita tuni ta zubar da makaman ta ta fara tausaya masa..." Bani da tabbacin ga dalilin ciwon sa amma ina ji ajikina kina da ala'ka da ita, kuma naji wasu ma na fa'de cikin gari...bazan yi son kai ba domin bamu san inda rana zata fa'di ba...haka nasan idan har ya kasance kece matar sa na san mu bamu isa mu hana ku rayuwa tare ba..kinga anan dole ne ke ki danne naki burin kibi za6in da Allah yayi miki..idan kika cigaba da ha'kuri sai kiga Allah ya dubi zuciyar ki sanadin biyayyar auren ki sai ya saki a aljannar sa ma'daukakiya kinga idan hakan ya faru ai bakiyi hasarar rayuwar duniyar ki ba ko?"
" Hakane Ummah".
" Toh ki yi ha'kuri ni dai a kullum shawarar da zan baki kenan shine ki sawa ranki ha'kuri ki rungumi 'kaddarar ki kinji?".
" Insha Allah Ummah..nagode sosai..".
" Yauwa Uwa ta..idan kin kunna wayar ki ma ki 'kira Addar ki, 'dazun take gaya min wai a kwanakin nan bata samun ki sai ki neme ta kinji..".
" Uhum" Tace gami da tashi ta bar inda Ummahn ke zaune.

Cikin 'daki ta koma ta rizgi kukan ta son ranta kafin daga bisani ta nemi layin Addar tata.

Ko Addah maryam ma shawarar da ta bata kenan duk kalan na Ummah ne wanda zuwa wannan lokacin ita kanta ta fara jin wani 6angare na zuciyar ta na yin na'am da batun amma mafi rinjaye na zuciyar tan yana garga'din ta ne yana kuma tuno mata da can abinda ya wuce abaya..ji take kamar ace an canza ta ba ita bace yafi mata, wani sa'in har ji take dama Allah ya 'dauke ranta 'kila hakan zai fi mata sau'ki..har ga Allah ita bata son komawa auren sa amma ya zatayi? abu ne mai mai matu'kara wahala agare ta ta iya duban idanun su Ammi tace da su wani daban zata aura ba 'dan su ba, aganin ta sam Ammi bata cancanci hakan daga gareta ba bayan duk 'kaunar da ta nuna mata arayuwa.

Tun ba yau ba ta za6i ta farantawa Ammi fiye da kanta wanda hakan ke nuni da cewa ta amince da sake zaman aure da Mu'een ne, amma inda matsalar take yanzu shine ita sam bata san ta ina zata fara furtawa ba, a zuciyar ta take jin ta amince saboda Allah da kuma Ammin ta amma bakin ta yayi mata nawi da furtawa.

Addar ta Saudah ka'dai ce bata yi na'am da batun ba cuz ita cikin gari take tana kuma yawan jin maganganu akansa musamman da yake rayuwar babban gidan take yi shiyasa a kullum aibun Mu'een baya ta6a barin kunnuwan ta.

Hatta Yah Usman ma bai nuna rashin amincewar sa ba lokacin da Ummah ke bashi labari sai yace Allah dai ya shige mana gaba.
Abinda kawai ya iya fa'di kenan da yake shi ba gwanin jan magana bane hakan yasa bai sake sanya bakin sa ba..dama ace Saudah ce ko Maryam da a matsayin sa na babban wan su dole ne zai yi wani yun'kuri amma Noor kam yasan ko ya fa'di wani abin ma aikin banza zai yi domin ita tun mahaifin su na raye aka bawa Alhaji Baba ri'kon ta so yanzu su ke da iko da ita ba shi ba...gashi sanadin su har waje ta samu daman fita dan yin karatu wanda ko cikin 'ya'yan Alhajin ma ya tabbata babu wanda ya fita karatu a waje ita ka'dai suka bawa wannan gatan...da ace kuwa suna da son kansu da nasu 'ya'yan ka'dai da ya tabbata Noor ko kusa da jikin 'dan su ma bata isa taje ba balle har batun aure ya ha'da su...talk more of fita malesia karatu.

Wannan tunanin yayi shi ne cikin zuciyar sa kawai amma a fili bai wani yi dogon magana ba.

*****
Cikin satin kuma jikin Yah Deen ya matsa sosai hatta Uncle Ja'afar sai da yazo Bauchi, idan yana tari har ta hancin sa jini ke fita duk ya galabaita baya iya ko yin numfashi mai kyau dole aka tafi da shi asbitin koyarwa dake garin Zaria.

Tuni Uncle Ja'afar ya fara shawarar fitar da shi waje ma amma sai likitocin suka nemi abar shi tukunna akwai possibilitin sabon dashe da zuciyar sa ke so ayi dan gab zuciyar tasa take da daina yi masa amfani kuma koda anje can 'din ma duk zancen 'daya ne..so idan ance za'a ja lokaci kuma yana iya rasa ransa ma gaba 'daya duk da ba lallai ne sai anyi dashen ba amma dai hakan na da matu'kar muhimman ci..sai dai kuma hakan zai iya zama tarihi idan zasu iya wani abu..likita yace su tanadi abinda suka tabbatar zai sanya shi farin ciki da farkawar sa idan anyi sa'a ma yin hakan zai iya sau'kar da kaso mafi girma daga cikin ciwon nasa.

Dole ba dan suna so ba suka ha'kura suka zubawa sarautar Allah idanu sai dai zu'katan su cike da yake tunanin abinda ya kamata su tanada kowa ya rasa mafita yayin da dukkan su suka zurfafa tunani wajen gano abinda ya dace suyi, kowa tunanin sa kan Noor ya fa'da dan sun san itace ka'dai matsalar sa a yanzu sai dai ta ya zasu iya sanya shi farin ciki da batun ta wannan me har yanzun sun kasa ganowa..Duk 'ko'karin da ya kamata ace likitocin sunyi sun yi shi akan sa kafin su samo kan matsalar tasa.

Kwanaki na sake 'karatowa lokacin tafiyar Noor na sake matsowa domin kwanaki hu'du ya rage mata ta tafi..sam bata san cewa ankai Mu'een Zaria ba saboda babu wanda ya sanar da ita, Saif kuwa da shi aka tafi balkanatan taji labarin daga wajen sa, Zaidu kuwa dama tuni ya tattara ya koma Taraba wurin Uncle Ja'afar so baya gida yanzu.

Kan batun tafiyar tata taje gidan Alhajin domin su tattauna da Anty hadda Ammi ma, nan ta tarar da su kowa jigum-jigum gashi dama tun ranar da suka yi magana da Antyn basu 'kara ha'duwa ba ko awaya basu gaisa ba yau kusan kwana shida kenan rabon su da juna shiyasa ma ta raso ta zo.

Hankalin ta tashi yayi da ganin yanayin su Ammin gashi da alamu hankalin su duk ba wuri guda yake ba.

A bakin Anty Zainab take jin labarin abinda ke faruwa..wanda nan take taji gaba 'daya tsigar jikin ta ya tashi.
Bata kai ga dai-dai ta natsuwar ta ba taji wayar Ammi na ringing nan duk suka maida hankalin su kai..Saif ne ke yiwa Ammi bayanin duk abinda likitocin suka ce..harda lokacin da suka nemi abasu dan shawo kan abin suga ko dashen ne ya dace ko kuma zasu dace su shawo kan matsalar tunda da saura zuciyar tasa bata daina amfani ba har yanzu.

Ammi kawai hawaye ne ya fara gangaro mata wayar ma sulalewa tayi ta fa'di kan cinyar ta batare da ta kula ba..." Allah ka jarabce ni, Yah Allah ka bani ikon cinye wannan jarrabawar..".
Haka ta fa'di cikin kuka wanda da sauri ni da Anty Zainab muka zo kusa da ita ni kam ban iya magana ba illah kukan da yaci 'karfi na ganin halin da Ammi ta shiga.

Anty Zainab ma hawaye take yi tana kuma bawa Ammi baki..Ammi sai girgiza kanta take yi tana jin zuciyar ta babu da'di...idanun ta lumshe tace" Zainab Mu'een na shan wahala sosai, ban san inda ya samo ciwon zuciyar nan ba gashi tana neman halaka min shi, wallahi ji nake da ina da damar da zan bashi farin cikin da yake so da na bashi Zainab bana so in rasa shi...'kalubale da yawa ya fuskan ta a rayuwar sa kuma ya jura wannan kam ina jin ba zai iya jurewa ba...".
Ban da shashshe'ka babu abinda ke tashi cikin parloun idan ka gammu sai kayi zaton ko labarin mutuwa ce ta riske mu a lokacin.

Ni da Anty Zainab ko magana ma bama iyawa Ammi ce ka'dai ta cigaba da fa'din"...yaro ne shi mai matu'kar 'kauna da tausayin iyayen sa, 6angare 'daya kawai ya samu mummunar shaida..."
Bu'de idanun tayi tace" Zo Noor zo kusa da ni..." Da sauri na matso jikin ta na kwantar da kaina a jikin ta na cigaba da kuka na..tana shafa kaina tace" Zainab ku yafe masa dan Allah duk abinda yayi muku ku yafe masa...Noor please ki yafewa yayan ki kinji..kar ki ri'ke shi a zuciyar ki kinga ma rayuwar sa gaba 'daya tana neman 'karewa...kar ya mutu da fushin ku akan sa..."
'Dago kai Noor tayi tana toshe bakin ta da hannun ta 'daya take duban Ammi, idanun ta cike taf da hawaye wasu na gangarowa yayin da idanun ke sake cikowa.

Girgiza kanta kanta take yi a hankali tace" Ni bana jin haushin sa Ammi...tuntuni na yafe masa..ban rayu da haushin sa cikin zuciya ta ba..kuma na riga na yanke shawaran sake auren sa kice masa kar ya tafi ya barni Ammi dan Allah kice masa ya yafe min...".
Chapter 203 · 0% Book details