← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 211

Sashe 171

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin dakatar da shi Safwan yayi ganin cewa da 'kyar yake 'kwa'kulo maganan yana 'kara ran'kwafawa saboda ciwon dake cinsa a zuciyar sa... kafa'dun duk biyun Safwan ya taklafo sannan yace
" Please ka daina irin wannan maganganun  Mu'een, Jasmine ce fa a gaban ka, nd she is just 5yrs yarinya ce 'karama ba fahimtar ka take yi ba sam, baya ga haka ma da wanne kake so taji? Kaima in wahal da kanka kawai kake yi...ka bari aje a duba ka in ka 'dan warware sai kazo kayi mata hiran kaji..".
Safwan yayi maganar ne yana 'ko'karin tada shi amma ya turje ya gyara zaman sa da kyau, da Safwan ya matsa sai Yah Deen yace sai dai azo a duba shi anan amma shi babu inda zai je yana nan tare da 'yar sa, yace"..idan na tafi na bar Baby hankali na bazai kwanta ba Safwan...".

Safwan fita yayi yana jan 'kafafu, duk kansa ya kulle da wannan lamarin, san ya rasa ta ina zai fara ma, da fitar sa sai ya tarar da su tsaye cirko-cirko daga waje, banda Alhaji Baba da har yanzu yake can zaune inda ya bar shi ya zuba uban tagumi shi ka'dai yasan me yake ji.a zuciyar sa game da Yah Deen..lokaci lokaci yakan furta" Ahamdulillah ala kulli halin, ha'ki'ka Allah ya jarabce shi, jarrabawa mafi girma daya bashi 'da irin Mu'een, bai san me zai ce ba face ya godewa Allah kawai.

Ammi ma har yanzu tare take da Noor tana aikin lallashi, ita kam a yanzu Noor ka'dai ke gaban ta, domin ita ka'dai ke bata tausayi sai kuma Jasmine dake can kwance cikin mawuyacin hali...Yah Deen kam koka'dan bata jin sa a zuciyar ta, gaba 'daya taji ya fice cikin ranta, banda tsanar sa babu abinda take ji a yanzu.

Da fitowar sa sai ya sanar da su abinda Mu'een 'din yace, kowa sai ya bu'de baki da alamun mamaki kan fuskokin su, domin sun san idan aka biye a  haka cikin wannan halin.ba zaibkai labari ba.

  Alhaji Baba kam wani wani 'katutun ba'kin ciki yaji ya tokare shi a 'kirji, duk yanda yake jin babu da'di a jikin sa amma hakan bai hana shi mi'kewa ba, cikin 'dakin ya shige direct da ka ga fukar sa kasan yau 'din akwai bambamci da kullum, tsananin 6acin ransa a bayyane yake a fili.

Yana zuwa ya sau'kewa Yah Deen wani mari mai cike da da jin haushin sa atake ya 'kara masa wani bai ko damu da halin da ya gansa ciki ba, ya sake sau'ke mishi wani yana huci..sannan ya nuna.shi da 'dan yatsa.

Shi kam bai ko iya 'daga idanu ya dube shi ba illah Baby da yake kallo, ya riga ya sawa ransa cewar ko wani irin abu iyayen san su masa matu'kar hakan zai sa zuciyar su tayi sanyi shi bazai damu ba...ya san idan a musulunce ne ma hukuncin jefewa ne akansa wanda zai kai shi har mutuwa, so dan sun mareshi hakan ba zai sa yaji haushin su ba..ya cancanci komai daga garesu domin bai yiwa rayuwar su adalci ba.

Tunda yake da mahaifin sa karo na biyu kenan da ya ta6a sau'ke hannun sa saman jikin sa da sunan  mari, kuma duk shine yake jawa kansa.

Alhaji Baba bai bar shi ba sai da ya sau'ke masa maruka har guda biyar a zuciye sannan ya 'kara da finciko hannun sa ya jashi ya tura shi waje yana fa'din" Maza kaje can da banzan halin ka da ba'a maka nasiha kaji,  bazan yi maka baki.ba Mu'een amma kaje indai rayuwar duniya ce gaka ga ita, bacin ka lalata mata rayuwa kuma yanzu me kazo ka zauna kayi mata, ko kake sai kaga bayan ta tukunna hankalin ka zai kwanta? banza wawa marar hankali, wallahi nayi dana sanin baka auren yarinya ta, sam bata dace da mutun irin ka ba,  baka cancanci zama miji agare ta ba balle mahaifi ga Aishatu...har abada bazan daina danasanin haihuwar ka ba domin baka 'kare ni da komai ba sai abin Allah wadai, tun baka kai hakan ba nake fama da kai, tunda da yarintar ka kake dasa min ba'kin ciki a zuciya wanda cikin 'kannan duk babu wanda ya ta6a ko kwatanta yi min irin hakan sai kai ka'dai 'dan iska marar tunani mai halin gwaraye...".

Wannan karon kam numfashin Yah Deen kafewa yayi, daga inda yake dur'kushen ko motsin kirki kasawa yayi...bai masan su wa  da waye bane ke tsaye a wurin har aka 'dauke shi akayi gaba da shi bai san inda kansa yake ba.

Taimakon gaggawa aka fara bashi da 'kyar aka samu numfashin sa ya daidaita amma har a lokacin bai farfa'do ba...numfashin sa yaja sosai.

Baby kam da idanu ta ringa kallon Alhaji Baba ganin dukan da yayiwa mahaifinta a idanun ta, ba ta iya tace da shi komai ba illa idanun ta da ta maida ta ta rufe su a hankali.

Noor kukan ta 'karuwa yayi jin irin mugayen kalaman da Alhaji Baba ya furta akan Yah Deen, sam bata so hakan ya faru ba, sai ma take ganin laifin sa da ya bada labarin rayuwar sa kaf da bakin sa, mai yasa bai bar shi sun cigaba da rufewa tsakanin su ba?
Ita koda zata rabu da shi ne tayiwa kanta al'kawarin bazata fa'diwa kowa abinda ta gani ba, sai gashi da kansa ya bayyana komai ga iayen sa.
Kuka take tana 'karawa, tausayin dukkan su take har zuciyar ta.
Tasan kowa bazai ji da'din wannan abin ba sam.

Da yake Ammi tasan halin 'yar ta jin kukan da take sake yi yasa ta 'dago kanta tace" Karki ce min dan wannan banzan kike kuka..?"
Girgiza kai Noor tayi tace" Ammi baki ji maganganun Alhajin ba? sun yi tsauri da yawa fa".
" Ina ruwan ki to..ni banason shirme, lokacin da yake yin son ransa ya tausayawa kansa ne, sai kece yanzu uwar tsausayi ko, to ba shiryawa zamuyi dake ba matu'kar kika ce kuka zaki dinga yimin saboda shi, ki bar shi can ai shi ya sani ba rayuwar sa bace..."
Mummyn Safwan ce ta sako.bakin ta da fa'din" Hajiya ayi ha'kuri dai, in.kika lura zaki ga tsananin nadama ce tattare da shi yanzu, me yasa bazaku bashi dama ba?"
Murmushin takaici Ammi tayi sannan tace" Ki bar shi ba wani nadama da yayi in dai wannan yaron ne, idan fushin da Alhaji Baba yayi da shi abaya bai sa ya nutsu ba wallahi bana tunanin akwai abinda zai nutsar da shi cikin sau'ki haka..munafurci kawai ke damun sa ba komai ba".

Shiru Mummy tayi kawai tana tunani cikin zuciyar ta, ita kam gaba 'daya tausayin sa take ji, ai kowa da yanda Allah yake tsara masa rayuwa, kuma dan ka tsinci kanka ko wani naka matsayin shiryayye bawai dabarar ka bace tasa hakan kawai Allah ne ya so ganin ka da wannan matsayin, to ko shima Mu'een 'din bawai rashin wayon sa bane ya kai shi ga fara wannan rayuwar face 'kaddarar dake zane cikin rayuwar sa wanda Allah ne ka'dai yasan nufin sa da shi.
Babu wanda ya saje wata magana tsakanin su kawai suka cigaba da zaman alhinin faruwar lamarin.

*****
       'Bangaren Sani kuwa tuni anyi nisa cikin thearter room sai fatan Allah yasa afito lafiya ya kuma sa a dace da aikin da za'a yi masa.

Sun 'dauki kimanin awa guda da rabi a zaune, lokacin har anyi sallar Azahar, bayan sun idar sai mummyn Safwan tace zata tafi gida zuwa yamma zata dawo ko kuma gobe, ro'kon ta Ammi tayi akan dan Allah ta sau'ke mata Noor a gida ta 'dan watsa ruwa ta kintsa in yaso sai ta dawo dan taga alamar tun jiyan bata samu nutsauwa ba.

Noor da farko 'kin amincewa tayi da tafiyar amma Ammi ta matsa dole suka tafi tare da Mummy ta sau'ke ta, ko a motan ma ha'kuri take sake bata saboda yanzu kam da kunnuwan ta taji komai da ya faru, ta kuma fahimci irin ha'kurin da Noor tayi da shi, sai dai duk da hakan tasuayin sa bai gaza zama cikin ranta ba, amma ya zama dole ta.bawa Noor ha'kuri dan ta cancanci yabo, ba kowace mace bace ke da irin zuciyar ta, ko ita nan da take da jikoki ma idan akace ta ga mijin ta da wata macen daban ganin idanun ta tasan Allah ka'dai ne zai gyara lamarin balle Noor da take yarinya mai 'karancin shekaru, ha'ki'ka tayi ha'kuri, ta nuna masa halacci ta kuma rufa masa asiri matu'ka, babban abinda yafi tsaya mata arai ma shine sunan Yusrah da taji cikin labarin, kenan ita aka rufe ba'a gayawa ba tun farko, tunda gashi yace Safwan ne ma ya raba su, kenan shima ya sani amma ya 6oye mata...ta riga ta sa cikin ranta cewar uban Yusrah zataci idan har ta tabbatar da wannan labarin gaskiya ne.

Ai ba yau ta fara yi musu nasiha ita da mahaifiyar ba akan yawacen-yawacen banza  da Yusran ke yi, shine har abin ya zago ya dawo kan abokin Safwan...hmm"

Har suka isa gida tausan Noor take yi kuma ba laifi yanzu kam hankalin ta ya 'dan kwanta tunda da taga Ammin ta sai taji 'kwarin gwiwa ya shige ta sosai, hukuncin da ta riga ta yanke ne dai bata jin zata iya janyewa saboda bata bu'katar sake rayuwar aure da shi, ta 'kwammaci ta mutu ba aure da ta cigaba da rayuwa da mutun maci amana irin Yah
Deen da ba ya ta6a hangen gaba, baya da kyakkyawan zuciyar da zai fahimci kuskuren da yake aikatawa balle yayi tuba na gaskiya.
Watarana idan yayi wani abin sai taga kamar ya daina ne amma da kanta take 'karya ta kanta kuma idan halin san ya sake bayyana mata.
Hakan ne ma yasa ta fahimci cewa daidaiton hankalin sa zaiyi wahala, baza ta ta6a amincewa da nadamar sa ba.
Kullum raba mata hankali yake yi da salon da ke nan iri daban daban, ko kaga alamun nadama tattare da shi kwana kusa kuma zaka sake 'karya ta tunanin ka, domin a fili yake bayyana cewa bazai iya barin harkar neman mata ba.
Chapter 171 · 0% Book details