← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 211

Sashe 103

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta 'dauki tsawon lokaci tana a haka kafin ta samu ta bawa kanta ha'kuri ta tashi ta je ta watsa ruwa, ko cikin bathroom 'din ma ta da'de kafin ta fito tunanin ta yadda zata tunkari mahaifiyar ta da wannan maganar take yi, me zata ce da ita da bazai tashi hankalin ta ba, tana son mahaifiyar tana kuma son farin cikin ta ta yadda take jin koda zata 'kuntatawa zuciyar ta ne tana son ganin mummyn ta na walwala, domin ita ka'daice ta fi kowa damuwa da damuwar ta in akwai na biyun ta to Yayan ta Hisham ne.

Haka ta fito ta sake shiri jikin ta sanyi 'kalau, kallo 'daya zaka yi mata ka tabbatar ba dai-dai take ba, gaban mirror taje ta tsaya tana 'karewa fuskar ta kallo sam bata so mahaifiyar ta ta fahimci halin da take ciki, dole zata 6oye mata komai dan kar ta shiga damuwa tunda tasan yadda Alhaji Mamman ke treating Mummyn ta ba lallai ne ya saurare ta kan batun ba, ta kuma san da mahaifiyar ta taji asalin meke tafiya dole ne tace zata same shi tayi mai bayani, ko da kuwa cewa akayi bata son auren sa6anin yanda ya yadda akan cewa sun daidata kansu tun farko 'din ma idan yayi niyya sai anyi to ina amfanin ta bar mahaifiyar ta da tunanin an aura mata wanda zai muzguna mata ya kusantata da lahirar ta.

Abin ma zai fi cimata rai a duk lokacin da ta tuna cewa Mu'een na azabtar da ita ne saboda already ya san ta matsayin 'ya mace shiyasa ya tsane ta yake azabtar da ita tasan ba komai bane ya kawo hakan face sakamakon yaudarar mahaifiyar ta da tayi take mata fuska biyu bacin a gefe tana holewar ta agaban ta kuma ta zama saliha, shiyasa ma tayi na'am ta kar6i hukuncin ita ka'dai bazata yadda zuciyar mahaifiyar ta ya 6aci sanadin hakan ba tunda babu s
hannun ta aciki...( _Mata fa naku...karfa kiyi zaton ko kinje kin yi kalar rayuwar da kika ga dama Allah ba zai kamaki ba...ba wai maza ne ka'dai Allah ke hukuntawa bisa aikata Zina ba a a harma da matan wallahi...gara ma mu nutsu dan babu yadda za'a yi iyayen ki su baki tarbiya su 6ata lokacin su wurin jan ki ajiki su saki farin ciki su wadata ki da komai na rayuwa 'karshe suje suna alfahari dake cewa sun haifi natsatstsa, amma 'karshe ki watsa musu 'kasa a idanu sanadin soyayyar wani banzan mayaudari sai ki zama mai fuska biyu bayan kin biyewa saurayin kun gama aikata son ranku... gaban iyayen ki kuma kina acting as babu yake fannin hankali da natsuwa dan munfurci, kuma a hakan sai kiyi zaton Allah ba zai kamaki ba? wallahi matu'kar baki tuba ba dole ne Allah ya hukunta ki....kar kiji ance in kayi da 'yar wani za'ayi da taka, haka in kayi da matar wani ma za'a yi da taka ki zaci hukuncin kan maza kawai ya sau'ka...to ki sani kema da kika biye masa akwai naki hukuncin gagarumi kuwa yana jiran ki, wasu mazan ma zasu yi ta aikata Zinan son ran su, su kuma yi dacen samun nitsatstsiyar mace su aura, 'karshe ma kika ga 'ya'yan su sun rayu cikin kariyar ubangiji...sai kiga sun yi tunanin ai sunci bulus....duk babu yadda Allah baiyi da bayin sa, kuma yana 'kaddara abu ne a duk kan wanda ya ga dama, yana jarbtar bayin sa ne da kala-kalar 'kaddara, idan ya so ka da Rahama nema zai hukunta ka tun anan duniya ba sai anje can ba....Sannan akwai Zina ta tilastawa misali kamar rape da sauransu, shine wanda hukuncin sa ke sau'ka kan namiji ma'ana shi wanda yayi niyyar yi 'din har ya tilastaki, amma in kin san ke da kanki kam kika je da niyyar ki da kuma yardar ki to fa ke ma kinsan naki hukuncin na jiran ki wurin mahalicci...'YAN UWA NA MU DAURE MU TUBA MU DAINA, ZINA FA DATTIN ZUCIYA TAKE SAWA ZATA NESANTAKA DA RAHAMAR ALLAH TA KUMA KUSANTA KA DA SHAI'DAN DA AIYUKAN SA 'KARSHE YA BARKA DA AZABAR WUTAR ALLAH MAJI RO'KO .... Yah Allah ubangiji muna ro'kon ka kayi mana tsari da kusantar Zina_ ).

Ba'kin kwalli ta nema ta ranba'da a idanun ta take ta 'dan sauya kamanni,  harda powder ta shafa ta saka lipstick a bakin ta sannan ta kama hanyar fita tana addu'ar Allah ya rufa mata asiri, fita tayi taje gefen mummyn ta dake zaune a palour tana kan lissafe-lissafe ta isa ta zauna daga gefen ta cikin sanyin murya tace " Mummy barka da hutawa".

" Yauwa Husnah...an fito ne?"

" Erh mummy...".

Kafin Mummyn ta sake magana sai ta riga ta da fa'din " 'Dazun nan munyi magana da shi ina zaune kawai naga ya 'kira ni".
Tayi maganar bayan ta 'ka'kalo murmushin 'karya.

Ba bu'katar sake tambaya cuz already abin ke ran kowannane daga cikin su, tsawon kusan sati biyu suka 'dauka suna jiran ji daga gare shi, hakan yasa mummyn Husnah cikin farin ciki ta furta " Alhamdulillah...ya kuma kuka yi da shi?"
Tayi maganar tana yi mata duba irin na jin da'di.
Husnah sai ta sunkuyar da kanta sannab tace
" Mummyn ce min yayj wai iyayen sa ne suka zo, kwana kin nan 'din ma an sace wayar sa ne shiyasa ya 'dauki lokaci bai 'kira ni ba...amma yanzun ya sai wata".
Cikin sanyi da dukkan dauriyar ta take magana, sosai tayi 'ko'kari wajen 6oye dukkan damuwar ta saboda son ganin farin cikin masoyiyar mahaifiyar ta.

Mummyn Husnah kam banda _Alhamdulillah_ babu abinda take ta nanatawa, dama damuwar ta shine kar a aura wa Husnah wanda bata san shi ba ko kuma ace bata son shi..yanzu kuwa da taji cewa wanda ta sanin ne ya sata 'dan ji sanyi cikin ranta.

Cikin kwantar da hankali ta yi mata nasiha akan kar ta 'daga hankalin ta dan ta ganta ta koma wata iri komai zai dai-dai ta da iznin Allah..ina ta 'karashe da fa'din" Ko akwai wara matsalar ne daban?"

Husnah na jin haka rayh saurjn girgiza kanta tare da fa'din" Babu komai Mummy kawai dai naga kamar lokacin yayi kusa ne sosai".

Murmushi Mummyn tare sannan tace" Shiyasa ai nace ki kwantar da hankalin ki, shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya riga ya rubuta mutun bai isa ya canza shi ba, da shiri ko babu shiri idan lokaci ya tsaya to fa sai anyi, misalin sa tamkar mutuwa ne...karma wannan batun ya dame ki...ki saki ranki ki runguni 'kaddarar ki kinji Uwata".

Kai ta jinjina cike da gamsuwa still idanun ta na kan hannun ta bata iya ta ha'da idanu da Mummyn nata ba.

Kawar da wancen maganar Mummyn Husnah tayi inda tana gyara zamanta zuwa kishingi'da tace
"..Tambayar da nake so in miki tuntuni da nace sai kun yi waya da shi 'dinnan kin tuna ko?"

Husnah cewa tayi
" Erh mummy ban manta ba".

" Dama ina so idan ya kasance shi 'din ne in tamabaye ki shin Husnah daman can kuna soyayya da shine ne, ma'ana kina son shi yana son ki?"

Fuskar ta tayi saurin rufewa da hannuwan ta biyu kamar gaske sai kuma ta ta shi da hanzari ta bar wurin tama fice daga palourn gaba 'daya, ga duk wanda tayi hakan agaban sa zai yi zaton ko kunya ce ta sata tashi, sai dai sam ba haka bane kuka ne yaso 'kwace Husnah gudun kar tayi gaban mahaifiyar ta yasa tayi saurin ta shi ta bar wurin, dan tasan dole in Mummyn ta taga tana kuka sai ta tambayi dalili ita kuwa bata san amsar me ya kamata ta bata.

Yayin da Mummyn Husnah tayi tunanin ko tsabar kunyar ne ya sanya ta yin hakan, dan haka da murmushi kawai ta bi bayan ta tana jin farin ciki na ratsa ta ta ko'ina, yanzu kam tasan ba auren dole ake son yiwa Husnah ba dan haka bata da sauran damuwa.

Tun daga ranar ta fara sanar da 'yan uwa da abokan arziki tana fa'din date 'din bikin cikin farin ciki marar misaltuwa.

Haka ta fara shiri gadan-gadan wanda ya dace tayi ta 6angren ta na uwa, tayi 'ko'kari waje. gyare Husnah tsab cikin 'yan kwanakin duk kuwa da bata san ma cewa ita 'din already ta biyewa son zuciya ta lalata rayuwar ta ba, hatta da kayan fitan biki duk ta bada sa'kon su za'a kawo mata daga lagos bayan an 'din ke su.

Ko ha'duwa da Husnah ba sa yi sosai saboda yanda ta saka hidima agaban ta, bata san cewa Husnah na kashe kanta da damuwa akowace rana ba, kallo 'daya zakayi mata kasan cewa ta rame sosai.

Tsimin da Mummyn ta ke bata kuwa bata wasa da shan su, cuz tayi tunanin cewa babu mamaki idan yaji ta canza zai iya sakkowa su raya auren su kamar kowa cikin farin ciki, hakan yasa bata yi wasa da gyaran jikin ta ba...wani abin ma ta hannun friends 'din ta ake sayo mata su a 6oye batare da sanin Mummyn ba.

*****
    'Bangaren Ammi ma shirye-shirye ya kankama sosai...Anty Zainab tuni tazo suka wuce Kano da wata 'kawar Ammi suka yi siyayyar kayan lefe wanda Alhaji Baba da kansa ya bada ku'din masu nawin gaske, Anty Zainab kam sakin ranta tayi tayi siyayya tsakanin ta da Allah na ganj a yaba, duk kuwa da cewa bason auren take yi ba amma ance abinda ka sowa kanka ka sowa 'dan uwanka daga cikin ingantattun hadisan manzo, hakan yasa ta zage ta za6i latest kaya na gani a bada labari masu kyau da tsarin gani ga kuma daraja a jikin wanda ya sanya su.

Tun tana can ma ta 'kira Mu'een tana dariya tayi masa albishir 'din yawan ku'din da Alhaji ya bayar na siyan lefen auren sa, Yah Deen kam sai cewa yayi  " Ni ina ruwa na kuma Anty?".

Dariya tayi masa sosai  sannan tace" To kai me zan siya maka..?"

Tun ma kan ta rufe baki tace" Babu komai ". Inda ya bata amsa a takaice yana kashe wayar sa.
Chapter 103 · 0% Book details