← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 211

Sashe 199

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kam fatan sa Allah yasa idan Anty tazo in ta taho masa da Noor 'din sa cuz tunda yaji muryar ta awayar Anty yasan tare suke da ita, sai ma yanzu yake jin haushin kansa da tuntuni bai yi tunanin hakan ba bayan dukkan alamu sun bayyana a fili, bai ta6a zaton Noor na wurin Anty Zainab ba da tuni ya tafi Taraban yama rasa dalilin da ke hana shi zuwan kwata-kwata.

Komawar Uncle Ja'afar da kwana uku sai ga Ishaq ma yazo duba shi wanda washegari aka disacharging 'din su ya koma gida dan ciwon da 'dan sau'ki ba laifi kuma likitan nasa yayi al'kawarin bashi kulawar da ta dace koma a ina yake.
Tare duk suka koma gida da Ishaq wanda har a lokacin maganar bakin sa take 'yar 'kalilan, baya ta6a yin maganar da tafi uku zuwa hu'du a kowace rana.

Shuwarin suka koma gaba 'dayan su sai washe gari kafin Ishaq yayi musu sallama ya koma Maiduguri.

Ammi ce ta cigaba da kulawa da 'danta tana nan-nan da shi, gaba 'daya ta sau'ko tayi sanyi, banda tausayin sa babu abinda take ji yanzu.

Ji take da tana da dama da babu abinda zai hana ta dawo masa da matar sa amma taga alamun Alhaji ba niyyar sa kenan ba, da kansa ya sanar da ita shirin sa akan Noor in 'din wanda hakan sai yasa wani sa'in take ganin kamar shi 'din bai damu da rayuwar Mu'een 'din bane bai damu da farin cikin sa ko ba'kin cikin sa ba.

Ranar da su Zainab suka sau'ka aranar ma zazza6i ne sosai ya rufe shi..ko sanin wanda ke kansa baya yi, dayake ma likita dake kula da shi yana nan kusa kuma yana zuwa duba shi akai-akai shine ke yi masa duk abinda ya dace kafin ya tafi...jikin sa kam Alhamdulillah yanzu dan illah zazza6in da ke yawan kama shi kuma sosai yake galabaitar da shi.

Shima likitan yayi wa su Alhaji bayani cewa abinda ya sa cikin ransa da be samu ba shike hana shi warwarewa kuma a kullum tunanin sa a kai ne shine kuma ke haddasa masa yawan zazza6in...

Saif kam kallon su kawai yake yi dan haushi ma ko batun Noor da yaji Uncle yayi be iya zancen da kowa ba cuz yasan duk suna da masaniya kuma suka bar shi yake shan wahala suna ta 'karar da ku'daden su abanza, to tunda kam sun sani shime ze sake cewa da su.

Ko ranar da za'a sallamo su ma batun da likitan yayi musu shine dai guda 'daya na cewa a rin'ka 'ko'karin kwantar masa da hankali ta hanyar sada shi da duk abinda yake so...tunda basu da niyyan ganin kwanciyar hankalin sa ai shikenan shikam ido zai zuba musu duk ranar da 'dan uwan sa ya rasa ransa kuwa a lokacin zai karantar da su babban kuskuren da suka aikata, a lokacin zai bayyana musu babbar illan da suka yiwa rayuwar 'dan uwan sa sanadin sakacin su da son zuciya.

Duk wani kulawa da Ammi ke bashi a yanzun Saif duk ba yabawa yake yi ba, gani yake duk na banza ne tunda ga can inda matsalar take kuma sun sani suke basarwa.

Anty Zainab da sau'kan ta ko ruwa bata sha ba ta ce ita kam yaron ta take son gani...
Ammi ce ta sanar da ita cewa yana 'dakin sa.

Noor kam shiru tayi tana danna wayar ta hankalin ta kwance.
Ta yi kyau shar abinta tamkar wacce bata ta6a zaman aure ba.

Ammi kan ta tayi mamakin canzawar Noor ga wani salo da wula'kanci da ta koyo.

Noor 'din ta duk ta canza ba kamar Hudahn ta me tsananin kunyan tan nan abaya ba.

Ammi bata yi mata batun zuwa duba Mu'een 'din ba ganin kamar bata da niyya sai kawai itama ta mi'ke tabi sahun Anty.

Noor tashi tayi ta koma 'dakin Ammi ta kwanta dan ba 'karamar gajiya tayi ba, ga tafiyar jirgi ga ta mota duk ga6o6in ta sun gaji sosai, hakan ma sai da suka kwana a Azare gidan su Anty Zainab suka 'dan huta kafin suka 'karaso.

Vibration wayar ta ta fara..ni kaina nayi mamaki da ganin sunan dake kai ha'di da jan symbol na heart na yawo akan fuskar wayar...'dauka tayi tana murmushi murya can 'kasa take magana ni kaina banji komai da tace ba.
Sai dai mamaki ya kasa bari na na ganin wannan lamari.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *90*

Basu samu daman gaisawa da Saif ba har kusan la'asar gwamma Zaidu ma shi kam sun ha'du sun gaisa da shi sama-sama.

Shi kansa Saif da ya ganta sosai mamakin ta ya kama shi ta zama wata 'yar gayu sosai ta murmure da alamu bata da damuwar komai..." Hudahn Ammi wai kece haka?"
Tambayar da yayi mata kenan da alamun mamaki 'karara kan fuskar sa.
Murmushi tayi masa sannan ta bashi amsa da fa'din" Ni ce mana Saif hala har ka manta da ni ne?"
" Ko nayi hakan ma aganin ki inada laifi ne? how many months ban gan ki ba, baki neman mutum kuma ko a waya ne.."
Murmushi kawai kawai tayi masa.
Sai yace " Allah fushi ma nake da ke.."
Ido ta 'dan zaro tana murmushi sai yace" Erh mana sam baki kyauta mana ba, ban ta6a zaton zakiyi irin hakan ba wallahi".
Tana duban sa still tana murmushin tace da shi" Hala wani laifin nayi mai girma..."
" Sosai kuwa, haushi ma naji shiyasa ban ta6a tambayar ki wajen Ammi ba, amma Noor ace ki tafi tsawon watanni ko irin ki neme mu awayar nan, ba sa'ko ba gaisuwa ba komai...ai ke kanki kinsan baki kyauta ba..kin bar mu kawai da kewar ki gida ya kasa samun natsuwa".

Murmushi kawai tayi tana maida idanun ta kan wayar hannun ta tace" Saif kenan...ya karatu kuma?"
" Karatu ya 'kare sauran wata kuma Insha Allah".
"To Allah ya taimaka..har kun 'kare service kenan?"
" Soon zamu fara.."
" Owk Allah ya bada sa'a"

" Ameen" Ya amsa yana mai gyara zaman sa.
Shiru ya 'dan biyo baya can.sai Saif ya mi'ke yana fa'din" Bari in duba Yaya anjima mu ha'du pls kinji".
" OK bakomai"
Haka kawai tace masa ta maida idanun ta kan chat da take yi.

Saif kam girgiza kansa yayi sannan yayi gaba abin sa.
Ya fa'di duba Yaya ne da tunanin ko itama zata ji kunya tace suje tare amma ga mamakin sa sai tayi kamar ma bata ji abinda ya fa'di ba.

Ita kam ji take kamar zaman gidan zai takura ta, cuz Yah Deen na gidan kuma bazata iya denying zuwa duba shi ba a koda yaushe ba ko dan saboda Ammi ma and bata son ganin sa balle ta tuna wani abu da yata6a ha'da ala'kar ta da shi...cikin zuciyar ta take yi masa fatan samun lafiya amma duk da hakan tasan idan har bata je ta duba shi ba Ammi cikin ranta bazata ji da'di ba sam dan hakan gwamma ta 'dan yi nesa ka'dan da su...zai fi mata.
Cikin ranta ta yanke shawaran komawa gidan Ummahn ta ayau in amma bayan sallar maghrib.

Hakan kuwa akayi sai dai kafin tafiyar tata ta samu ta bi Ammi 6angaren nasa badan ranta na so ba ma, haka dai kawai dan kar ammi taga kamar ko bata damu da lafiyar sa bane.

Allah ya taimake ta kuma lokacin ma bacci yake yi, har cikin zuciyar ta taji sanyi...hakan yasa tayi masa fatan samun lafiya sannan ta fito tana karanto yanayin sa da ta gani cikin zuciyar ta.

Sosai ta fahimci ramar da yayi duk kuwa da cewa ba wani sosai ta kalle shi ba, tasan babu mamaki ba 'karamar jinya yake yi ba dan tasan kalar ciwon sa..amma wata zuciyar ta sai ta kwa6e ta akan zurfafa tunani akan sa bata son ta fame tsohon ciwon da ta jima da binne shi hakan yasa ta tsagaita tunanin da cusawa zuciyar ta tsanar sa kamar yadda ta saba kullum.

Bata tafi ba sai da ta jira Alhaji Baba ya dawo gida suka gaisa kafin ta sanar da su cewa tana so zata gidan Ummah ne.
Babu wanda ya hana ta sai ma Saif Alhaji ya sa ya sau'ke ta dayake yasan tasu tafi zuwa 'daya.

Haka suka tafi suna 'yar hira ka'dan-ka'dan nan yake tambayar ta makaranta tace ai 3months kacal ya rage mata ta kammala gaba 'daya.

Murna sosai yayi mata da fatan Alkhairi sannan suka rabu.

Su Ummah kam ba 'karamin da'di suka ji ba da ganin ta bayan tsawon wani lokaci, sun jima suna hira ranar dan Ummah har mamaki ta bawa Noor, cikin hirar Ummah ke bata labarin duk wahalhalun da Mu'een ke sha da bata nan, tace tausayin yaron take ji sosai dama so take tayi mata maganar amma tabari akan sai sun ha'du saboda ta fahimce ta da kyau.

Jin Ummah ta fara maganar Yah Deen ne ya sata yin shiru kamar tana bacci...Jin shirun yasa Ummah ta 'kyale ta da tunanin ko baccin tayi da gaske.

Nan kuwa itama duniyar tunani ta fa'da...sam bata so ta sake komawa rayuwar Mu'een shiyasa ma ta yadda da soyayyar Abdulhakeem da ya nace mata, ba wai dan tana son shi ba sai dai dan kawai ya 'dauki hankalin ta, kuma ko batun aure ne ya tashi a shirye take ta aure sa tunda ta yadda da soyayyar da yake yi mata tsawon lokaci.

Ko ja masa rai da ta tayi ma tasan da ba dagaske yake son ta ba da tuni ya janye amma haka ya jajirce akanta ya nuna tsantsar juriya da ha'kuri duk kuwa da cewa yasan labarin komai akan ta amma bai janye ba.
Chapter 199 · 0% Book details