← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 211

Sashe 70

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita kuwa na bi bayan sa sa'daf-sa'daf ina le'ken sa, sai naga tafiya yayi dagaske amma zuwa bakin hanya ba hanyar gida yayi ba inda yana tafiyar ne ma yana amsa waya hankalin kwance ga dukkan alamu baya tare da damuwar komai.

Da'di naji har cikin raina da ganin ya tafin, gudun kar ya dawo ya tarar da ni da abinda nakeyi ya sanya ni dannawa 'kofar sakata sannan nayi ciki da gudu ina fizge hijab 'din kaina.

Raina fari tas mukayi aikin dan zagewa nayi na tayata amma ina yi ina 'kara jaddada mata cewa kar ma ta yadda tace da ni akayi aikin gudun kar laifi ya shafe ni.

Duk abinda naga be yi ba zan nuna mata a gyara wanda duk ina hakan ne dan kare kaina..." Allah ki tabbatar komai yayi dan in yazo yana masifa cewa zanyi ke ka'dai kika yi abinki dan ban isa da masifa ba ni kam"!
Haka nake ta maimaitawa Nana har muka kammala gyare komai tsaf muka fito bayan mun rufe ko'ina.

A hanyar mu ta komawa gida ne muka ha'du da Ma'u wanda tana ganin mu ta saki fara'a.

Tambaya ta tayi daga ina muke...na gaya mata harda abinda ya kaimu gidan ma duk na sanar da ita.

Bu'dan bakin Ma'u  sai tace " daga yau idan zaku nima zan na raka ku tunda Hudah ma ai tsoro kike ji ko?"
Ta 'karashe maganar tana idanun ta a kaina.

Da kai na bata amsa ina murmushin dan bata san asalin halin sa bane shiyasa take son zuwa inda yake.

Ko da muka 'karasa gida dan gudun magana ma wa Ammi na bawa makullin nasa nace inji shi wai a ajiye zai zo ya ansa.

Anan parlourn Ammi ta ajiye itama bata kai da nisa ba.

Yah Deen kuwa bai zo gidan ba har sai dare shi ko tsoro ma baya ji, arean gidan da yake 'din ba mutane sosai bama shi da makwabci na kusa...amma hakan kullum sai ya ringa yin dare wani lokacin ni har mamakin sa nakeyi ma.

*****
     'Karfe takwas da 'yan mintuna, suna zaune shi da Alhaji Baba da Ammi suna 'dan ta6a hira,
ni da su Saif kam duk muna 'dakunan mu, gara su ma su biyu ne sa6anin ni da nake ni daya sai dai inyi ta buga game ko kuma inta jagwalgwala wayar Ammi dan ba sanin kai nayi ba.

Alhaji Baba ne ya duba agogo sannan ya ce da shi " Tunda ka guje mu sai ka tashi ka wuce ai naga dare ya fara kawo kai".

Kishingi'da ya 'karayi tare da fa'din " Ina waccan yarinyar taki ne Ammi tazo ta bani Key na sai in tafi".

Kan center table Ammi ta nuna masa sannan tace " gasu nan ba ta kai da nisa ba ma".
Bai ce 'kala ba kawai ya tashi ya suri key 'din sa ya nufi hanyar fita". Nayi nan ni kam...Allah ya bamu alkahiri".
" Amin-Amin"
Cewar Alhaji Baba.

Tun daga ranar kuwa Ammi ke turamu ni da 'yar aikin ta Nana duk bayan kwana biyu ko uku da sunan muje muyi masa shara.

    Ma'u da ta gane kwanakin dake tsakanin zuwan namu sai ya kasance bama ko tunanin ina take ko kuma a ina zamu ganta, kawai tarar da ita muke yi tana jiran mu a gefe da gidan, da ta gan mu kuwa sai ta mi'ke mu 'karasa tare.

Ni kam zuwan Ma'u ai rana ya min...gani nake tamkar ceto na tayi, cuz har a lokacin tsoro nakeji dan haka ba kullum ne nake sakin raina in shiga hankali kwance ba, sai dai na kan shigo cikin harabar gidan ne yanzu in jira su har su kammala sannan mu tafi, da yake watarana bai fita har suyi su fito.

Ranar da na samu ya fita ya barmu mu ka'dai ne nakan saki raina in sha shagali na bayan na saka sakata wa mashigar gidan.

A lokacin bansan dalilin da ke sa Ma'u biyo mu ba kuma banta6a tunani akan hakan ba sam, ashe ita burin ta kawai ta ganshi ne...ta kuma kusanci inda yake, masifaffen son shi Allah ya jarabce ta da shi.....

*****
     Satin da hutun Yah Deen zai 'kare a week 'din su Saif suka fara zana JSCE wanda a lokacin Jss 2 ma suke amma da suka ce suna son zanawa sai Alhaji Baba ya shige musu gaba ya tsaya kai da fata har sai sunayen su ya shiga jerin 'yan Jss3 'din masu shirin fita.

        Kwanan su uku da farawa Yah Deen ya tattara ya tafi Jigawa Dutse.

Duk da ba gida 'daya muke da shi ba amma sosai naji da'din tafiyar sa da murnar zan huta ma da zirga zirgan zuwa yi masa shara.

Bayan tafiyar sa ne su Saif suka 'kare jarabawar suka fara hutu kuma.

*****
  Bayan wata uku da tafiyar sannan aka kai su Zaid makarantar boarding, ranar kam nasha kuka da 'kyar Ammi ta lallashe ni nayi shiru...tun daga lokacin gida ya zama shiru daga ni sai Ammi sai kuma Alhaji Baba idan ya dawo daga gidan gona.

Sam banjin da'din zaman gidan kwata-kwata dan ya zama babu da'di...i missed Saif alot dan shi abokina ne sosai ba kamar Zaidu ba.

    Da na kasa gane kan walwala ta sai na dinga tafiya wajen Ummah ta ina wuni acan daga nan mu wuce yawon mu da su Ummie muje gidan Addah da sauran 'yan uwa...inda duk da bana fahimtar hausar ta su sosai amma tun a lokacin na kanji suna cewa wai iyaye na sun bada ni saboda kwa'dayin abin duniya shiyasa suka ringa cusa ni tun ba'a so gashi yanzu har na zama 'yar gida kala ta ta bambanta da sauran 'yan uwa na, wannan maganar sai dai idan bamu je yawo ba sai an fadi min ko kuma idan an ganni ata6e baki sai kiji ance  Lalle fa gaskiya kwalliya ta biya ku'din sabulu". Ko kuma kiji ance " Umm su Hajiya Hudah 'yar gidan masu ku'di gaki nan kin dawo kamar 'kosai" ....Ni sam ba na sa maganganun aka a lokacin nalle in san cewa abin 6acin rai ake gaya min hakan yasa ban ta6a bawa maganar muhimmanci ba.

     Sai ma in an anga yanda na koyi iyayi na canza na dawo fes dani sai kiga ana sakin tsaki da juya kai gefe....ni kam ko ajiki na ban damu da abinda ke faruwa ba...inda har zaki ji wasu na fa'din " Da ayi rawa da bazar uban wani dai gwamma kayi da naka saboda ko babu komai nanne tushen ka kuma nan za'a koma daga karshe musamman idan kasuwa ta watse"..Wannan a gidan da Addah ta Sauda ke aure ne aka fa'di hakan wanda ya fito daga bakib kishiyoyin balbalin ta.

Addah Saudah shiru tayi bata tanka ba balle ni da bama fahimtar manufar su nayi ba sam.

Yawan zuwa gida da nake yi a lokacin ne ya sanya wasu ma'kwabtan mu suka fara gulmace-gulmacen wai ai an fara gajiya dani ne shiyasa aka fara koro ni gidan iyaye na, bansani ba ashe tun zama na agidan mutane da yawa na jin haushi, kuma Ummah ta ta sani amma bata ta6a nunawa ba, haka ma Addah ta ita kuma bata nuna damuwar ta bane saboda tasan abinda suke fa'da 'din ba gaskiya bane shiyasa take juran jin maganganun duk kuwa da cewa suna matu'kar yi mata ciwo har cikin ranta.

A hakan idan maganar tazo kunnan Ummah ta ta kanyi 'ko'karin fahimtar dasu cewa Ammin ke son zama dani ba wai cusa ni akayi ba amma sai aga kamar duk 'karya ne take yi.

Ummah ta shiru take yi musu tunda Allah ya san gaskiya ai shikenan, wannan dalilin ne ya sanya da wuya kaga 'kafar Ummahn mu a gidan Ammi sai indai da 'kwa'k'kwaran dalili kafin nan...sosai take 'ko'karin kare mutuncin ta dana 'ya'yan ta game da hakan.

Akwai ranar da nazo sai na 'ki komawa can wurin Ammi, 'karfe 8 har ta gota na dare na gama shirin bacci na har na kwanta, Ummah ta bata ce da ni komai ba, tun kafin Maghrib da tace min inyi in tafi kar dare ya same ni sai nace mata ai nan zan kwana Ammi ne tace min in kwana.
Na shirga wa Ummah ta 'karya nan kuwa bakomai ne ya sani hakan ba illah sabon 'kaunar ahali na da ya shige ni musamman saboda yawan zuwan da nake yi sai yasa sha'kuwar mu 'kara 'karfi.

Ummah kuwa tun lokacin da na fadi hakan sai ta shiga tunanin kardai dagaske zancen mutanen gaskiya ne cewa an fara turo ni gida da dabara...abin ya kulle mata kai sosai cuz tasan ada matu'kar zanzo gida kwana to da Ammi muke zuwa bata ta6a bari na in taho ni ka'dai...amma ga mamakin ta sai gashi yau 'din ni ka'dai ne na taho.

Ita kanta zata so in dawo gaban ta ta cigaba da ri'kon kayan ta amma tafi so inma hakan ne zai faru to ayi shi cikin mutunci kamar yadda aka 'dauke ni ana ganin darajar juna yafi.
Duk da haka Ummah bata 'kara damuna akan in koma ba kawai tayi shiru.

Har na kwanta ni da Ummie ina bata labari tamkar wata sa'a ta saboda shirme...kamar daga sama kawai sai naji tsayuwar mota wanda ya janyo hankulan mutane da dama harda wasu ma'kwabtan mu.

   Alhaji Baba da kansa ya janyo motar suka zo da Ammi ganin dare har tayi amma ban koma gida ba, shiyasa Ammi ta damu Alhaji Baba sai da suka zo tare dan ya tayata ro'ko a bar mata ni gaba 'daya ta cigaba da ri'ke ni.

Ai kuwa a 'kofar gida wurin Baban mu Alhaji Baba ya bayyana abinda ya kawo su inda ya ha'da da ro'kon kar Baban mu yace a a, dan Ammi ta damu sosai.
Chapter 70 · 0% Book details