← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 211

Sashe 133

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsarge na mi'ke zaune ina share hawaye na gangara 'daya gefen bed 'din na kwanta can daga nesa sosai da inda yake kwanciya, haka na du'kun'kuna wuri guda kamar marainiya ina share hawayen da bansan dalilin fitar su ba har bacci 6arawo ya sace ni ban kuma kallon inda yake ba balle in san me ke faruwa.

*****
Washegari kuwa da sassafe na fice daga 'dakin tun da asuba da ya tafi Masjid na gudu 'dakin Ammi na 'karasa bacci na acan, ko da ya dawo daga sallah ma da bai ganni ba murmushi kawai yayi ya san ba mamaki guduwa nayi dan naga ya fita masallaci.

Wunin ranar kaf bai ga idanu na ba, ko da wasa banyi gigin fitowa parlour ba dan ko su Saif ma sai bayan da na tabbatar baya gidan kafin na fito muka 'dn yi hira da su.  

Matu'kar na tabbatar yqna gidan to.bana fitowa har dare yayi, lokacin kuma sai naji hankali na ya fara tashi dan nasan dole sai na je inda yake dan Ammi ba bari na zata yi ba.

Sallar Maghrib da isha'i duk cikin rashin kuzari nayi su...ko da na idar kuwa sai na mi'ke nayi kwanciya ta akan daddumar har bacci ya fara 'dauka ta sai naji Ammi na tashi na kamar dai kullum...

Ban san yadda zanyi da Ammi.ba na tabbata da da ne babu abinda zai hana ni sanar da ita damuwa ta amma yanzu ban iyawa, jin Ammin nawa nake yi kamar wata daban.

Raina ba'ki 'kirin na tashi na shiga bayi na barta a wurin, na shafe a 'kalla kusan mintina sha biyar da gangan kafin na fito ai kuwa na sami Ammi zaune tana jira na.

Ban yi mamaki ba dan nasan indai Ammi ce fiye da hakan ma zata jira ni dan kawai taga iya gudun ruwa na, bata ce min 'kala ba ko da na fito in...haka nima ban yi mata magana ba so nake da kanta ta fahimci cewa har yanzu ni fa ba son zuwa can 'din nake ba...amma ga mamaki na Ammi kam ko a jikin ta.

Tsaye naga ta mi'ke sannan tace" Ina zuwa".
Da fitan ta sai na nemi kayan bacci na kamar yanda na saba kullum riga da dogon wando dan ni da irin su nafi sabo sai dai na yau 'din zallar pink ne...turare ka'dan na fesa a jiki na hakan ma ina yi ina tura baki na ina 'ko'karin sanya hijab 'dina sai ga Ammi ta dawo.

Murmushi tayi da gani na cikin nuna yabawar ta tace" Masha Allah yarinta ba dai kyau ba".

Shiru nayi kawai na sunkuyar da kaina 'kasa, nayi tunanin Ammi zata cecinyi zama na ne idan taga ina hakan amma ga ga mamaki.na sai sa6anin hakan na gani domin ko kula ni ta wancan 6angaren Ammi ba ta yi ba.
" My dear dare yayi sai da safe ko".
Ta fa'di tana min murmushi wanda ke fita tun daga zuciyar ta.
Da jin haka sai na kasa ha'kura kawai na shagwa6e fuska ta kamar zanyi kuka nace" Ammi please yau in kwana anan mana wai ni dole sai naje can in ne?"

" Ni ai ban hana ki ba...amma kije ki tambayi mijin ki first in ya yarda sai ki dawo nan da kwana abinki ni ba ruwa na..but for now kama hanya ki wuce sai da safe".

A fusace na 'daga 'kafafu na bar 'dakin.raina duk ba'ki'kirin...ciki-ciki nayi sallama na shiga inada na same shi zaune da system 'din sa agaba kamar dai rannan.

'Dauke kaina nayi daga kallon sa na sunkuyar da kaina 'kasa inda na 'karaso cikin rshin.kuzari.
" Yaya ina yini".
Nace da shi lokacin da na isa gefen bed 'din...ban jira jin amsar shi ba kawai na haye na yi kwanciya ta ina sake share hawaye na.

Ko kula ni kuwa bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi ban san tsawon lokacin da ya 'dauka zaune a wurin ba saboda baccin da ya 'dauke ni.

Cikin baccin naji kamar ana ta6a jiki na, ko da na bu'de idanu na sai na ci karo da shi a kusa dani...a 'dan firgice na yun'kura zan tashi sai naji hannun sa saman jiki na...juyo da fuska ta nayi na kalle shi ina daga kwancen sai ya sakin min murmushi 'kayatacce.

" Matsoraciya.." ya furta 'kasa-'kasa, inda yana maganar ni kuma ina jin yanda hannun sa ke yawo min a jiki.

Kasa jurewa nayi na sake yun'kurawa da niyyar tashi take na ji sau'kan sautin muryar sa cikin kunnuwa na inda ya daka min tsawan" Mai miye hakan wai?"
Luf nayi ban sake motsin kirki ba illa hawaye da ke gangaro min ta gefe da gefen idanu na.

Tsawon mintina uku muka 'dauka a haka sannan ya cire hannun sa daga saman jiki na ya sake rungumo ni cikin jikin sa bai ce da ni uffan ba har bacci yayi gaba da shi...ni kam da na kasance a matau'kar takure sai baccin ya kasa 'dauka ta...shi kuwa baccin sa yayi cikin kwanciyar hankali batare da wata damuwa ba.

Motsin kirki idan nayi sai inji ya sake janyo ni jikin sa sosai...haka dole na ha'kura na zubawa sarautar Allah idanu wanda daga 'karshe hawayen nawa daina fita suka yi ma a hakan nima har baccin ya 'dauke ni rungume a jikin sa.

Tun daga ranar salon kwanciyar mu da shi ya canza zuwa yanda ya ga dama...haka kullum inaji ina gani zai rungumo ni jikin sa har muyi bacci  tun bana sakin jiki na har nazo na saba da hakan na ma daina damuwa.

Alhaji Baba ma ya cika al'kawarin sa kamar yadda ya fa'da ya kawo min wayata sabuwa dal akwalin ta 'yar yayi harda sim 'dina...ranar murna kamar zan tashi sama, Saif yayi ta min dariya yayin da Zaidu ya ta6e baki yayi gaba abin sa.

A wajen Ammi na kar6i numbern Ummah ta na 'kira ta nayi mata albishir 'din an sai min waya nima...daga ita sai Baban mu amma bai 'dauka ba...sai bayan kusan awa guda kafin ya zo ya 'kira ni shima ina murna na sanar da shi bayan mun gaisa..da fara'ar sa ya sanya min albarka tare da min garga'din sai inbi a hankali, in kula da mutuncin aure na.

Ammi ce da kanta ta ta sanar da Yah Deen wayar da Alhaji Baba ya sai min, Yah Deen bai ce komai ba sai" Allah ya sanya Alkhairi" kawai da ya furta ba yabo ba fallasa fuskar sa.

A ranar da dare da naje kwanciya ya tambaye ni wayar wai zai gani sai nace na bari a 'dakin Ammi yace inje in 'dauko.

Zuciya ta fes naje na kawo masa wayar dan duk zato na ganin.kawai zai yi, ko da ya kar6a kuwa sai naga ya ajiye gefen bed yayi shirin bacci abinsa.

Hakan bai bani mamaki ba dan a tunani na ko dan saboda dare ne shiyasa.

Washe gari da na tashi da yake dama hankali na akan wayar ne so sai na duba inda naga ya ajiye jiya sai kuma ban ganta ba, haka na ha'kura na wuce cikin gida batare da ita ba.

Gashi bai dawo daga masallaci ba har a lokacin balle in tambaye sa.

Zuciya ta fal tunanin inda ya kaimin waya ta, tsoro na kar yace bazan kuma bani ita ba.

Ko bayan da gari ya 'karasa wayewa ma ban iya na naje inda yake musamman saboda wayar ba ni dai na zauna inajiran ko zai bani da kansa.
      A duk kuwa lokacin da naji muryar sa ya shigo hankali gaba 'daya nake tattara wurin sa wai ko zanga ya ciro ya bani amma ko alamun hakan ban gani daga gare sa ba.

Kamar wasa kuwa Yah Deen bai bani wayar ba har yamma, sosai na damu da kewan wayata dan kuwa na fara sabawa da ita, ko da na yiwa Ammi maganar ma sai tace min tsakanin mu ai ita babu ruwan ta.

Abinda ta fa'da 'din sosai ya 'kara min haushi dan nasan indai ya Deen ne idan ya ga dama ba zai bani ba in ba Ammin ta sa baki ba, shiru nayi kawai na zuba wa sarautar Allah idanu...ni ka'dai sai ina mita cikin zuciya ta, mutun baka siya min abu ba kuma an siya min kana ba'kin cikin da shi.

Ko da dare kuwa ban samu damar tambayar sa ba dan naga kamar ba'a dai-dai yake ba ransa 6ace yake wanda har kan fuskar sa zaka fahimta halin da zuciyar sa take ciki, tsoron ma yi masa magana naji dan bansan dalilin canzawar tasa ba.

Ranar a 6angaren sa nayi sallar Asubah na jira har ya dawo daga Masjid, shi kansa yayi mamaki da ya dawo ya tarar da ni amma bai ce da ni 'kala ba, sau 'daya kawai ya dube ni ya kau da kansa.

Gai she ni nayi a 'darare da tsoron ko bazai amsa ba, amma daga yanayin da naji muryar sa na fahimci da 'dan sau'ki.
" Yaya ba ka ban wayar tawa ba fa har yanzu".

Na fa'di cikin rawar murya da marairaita kamar mai neman gafaran wani babban laifi.

Shiru yayi ya zuba min idanu...cikin natsuwa yace" Ni me kike yi da wayar ne?"

" Ina 'kiran Ummah ta, kuma zan 'kira Baban mu ne".
Na bashi amsa cikin sauri.

Murmushi naga yayi na gefen baki sannan yace min" Su ka'dai kawai kike 'kira?" Sama na 'dage kain alamar " Erh" da hannun sa ya nuna min drawer inda ya ajiye wayar yace min je ki 'dauka amma ki kula kinji?"
Nace to ina murna har cikin zuciya ta.

Ina 'daukan wayata kuwa na ficewa ta daga 6angaren sa, dama abinda ya zaunar da ni kenan.
Ammi naje na nunawa nace ai ya bani wayar tace" Kin huta ai". A takaice ta fa'di hakan tana 'yar murmushi.

Baban mu shine mutun na farko da na fara 'kira amma still yau ma bai 'daga ba.

Ban damu ba dan nasan yau 'din ma idan yazo yaga missedcall 'dina zai 'kira ni...dan haka sai na 'kira Ummah ta muka gaisa amma muryar ta sanyi 'kalau naji, koda na tambaye ta kuma sai tace da ni bakomai.
Chapter 133 · 0% Book details